✍🏻✍🏻✍🏻 *SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)* ✍🏻✍🏻
Na
Hauwa'u Salisu (Haupha)
🌟6Stars Indeed
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*Wannan page kyauta ne sukutum ga ƙawata wato A'isha Muhammad Sani (Xayyeesherthul-humaerath) Cele 2 kiyi komi ba komi mabiya ko da yaushe bayyana suke gareki 🥰 Allah ya barmu tare ki ta sambaɗo mana labarin SAI NA AURI MARUBUCI JAMEEL NAFSEEN muna kwashewa🥰*
Page 6
Inna Kande dai na waje batasan wainar da Lantai ke toyawa ba.
Lantai ta sake dubawa ko ina ba littafi ba hankalinta ya tashi haiƙan, ta rasa abin da ke mata daɗi ta fice daga gidan batare data ko kalli inda Inna Kande take zaune ba.
Inna Kande ta bi bayanta da kallo ta ce, "Umma ta gaida ashsha yarinya sai neman maganar tsiya."
Lantai na fita ta sake bin hanyar data biyo lokacin data dawo daga makarantar, sai dai bata ga ko mai irin littafin ba, har ta isa makarantar ta iske ba kowa an jima da tashi.
Ta zauna ƙofar office ɗin su Malam Muntasir ta dinga kuka tana cewa "Wayyo abuna, ni sai naga abina wallahi bazan yadda ba."
Taci kukanta mai yawa har fuskarta ta fara kumbura ta miƙe ta sake bin hanyar ta koma gida, har idan taga tarin ƙasa sai ta yamutsa wai ko littafinta na ciki.Tana isa gidan ta sake wucewa banɗakin ta duba bata dai ganshi ba ,sai ranta ya fara bata cikin biyu za a samu ɗaya inda yake ko dai cikin shaddar gidan ko cikin rijiyar gidan dole a sameshi waje guda.
Ita kuwa Inna Kande ta lura yau Lantai ba zata tsinana mata komi ba a gidan sai ta miƙe ta kama aikinta na girkin abinci tana cikin aikinne ta ci karo da fanken nan guda da Lantai ta ɗauko gun Musa sai tayi tunanin ko shi Lantai ke nema duk ta ruɗe haka? Tasan Lantai da son fanke don haka ta ɗauki fanken ta kira Lantai ɗin "Lantai zo ga abin da kike ta nema."
Lantai ta kwaso da gudu ta shigo ɗakin fuska ɗauke da murmushi.
Inna Kande ta miƙa mata fanken itama da fara'a kwance a fuskarta.
Lantai tai sototo tana kallon fanken ta amsa ta zauna ta miƙe ƙafafuwanta ta gutsira ta fashe da kuka sosai har waje ana jinta."Wayyo ni Lantai na mutu na mutu ni Lantai ."
Inna Kande ta fara gajiya da koke-koken Lantai ta zaro zaborinta (Tsintsiyar kwakwa) ta rufe Lantai da duka taita tsula mata ita.
Da gudu Lantai tabar gidan tana kuka.
"Yarinya kin isheni da kuka don sakarci to yanzu ai sai kiyi na gaske ko ? Nasha gaya maki kukan banza kashe mutane yake na kusa da mutum kin ƙi bari."
Lantai ta koma ƙofar gidansu ta kwanta ƙasa taita kuka tana Inna Kande ta kasheta ga abinta ya ɓace ita ba zata yadda ba.
Mutanen layin tun basu damu da ita ba har suka fara mata magana tai haƙuri ta bar kukan ta koma gida amma kamar ƙara tunzura ta suke .
Tai buɗu-buɗu da ita amma ko a jikinta kukanta take kawai tana abinta ya ɓace ba zata yadda ba.
Sauri yake kada ya rasa motar da zata kai shi garinsu don haka ko tsayawa gaisawa da iyayen yara bai yi sai dai ya ɗaga masu hannu ya wuce.
YOU ARE READING
SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)
Fantasylabarin wata yarinya ce wadda babu abin da take so a rayuwarta irin taga marubuci Nasimat, ansha bata kyautuka tana maidawa akan marubucin tasha kwana da yunwa akan tunanin hanyar da zata gano marubucin ƙarshe wani malaminta ya cika mata burinta ind...