✍🏻✍🏻✍🏻 *SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)* ✍🏻✍🏻
Na
Hauwa'u Salisu (Haupha)
🌟6Stars Indeed
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 14
Turus Lantai tayi ganin Malam Muntasir zaune yayi kicin-kicin da fuska, babu alamar fara'a ko kaɗan akan fuskarshi.
Ayarin Barbushe kuwa suka dinga ihu suna karta wuƙaƙe tartsatsin wuta na tashi, yadda hankalin mutanen wajen zai tashi sosai.
Mai gari ya rarrafa ya kamo hannun Lantai cike da karayar zuciya yace, "Don darajar Allah Lantai ki mana haƙuri ni Wallahi ban san Uban da ya kwashe maganarki ya gayama Lado ba."
"La"ila ! Mai gari daga maida magana sai ka zageni ?Ba mai gari ba hatta mutanen gun cikinsu sai da ya juya, idan ka cire Malam Muntasir dake ta kallonsu, musamman Barbushe.
Barbushe ya daka uwar tsawa cike da muryar ƙauraye yace, "Ina Lado mai ƙarar kwana daya taɓa min ƙanwa Nuratu ? Su waye iyayensa a ƙauyen nan ? Su waye maƙwabtansa a ƙauyen nan?
To baki ɗaya yau ƙanwata Nuratu ta ce duk ku ji bala'i da masifa tare da ƙuncin da taji a ranta akan abin da Lado yayi mata.Kun san da a taɓa min Nuratu gyara an mareni, da kuwa a mareni gwara an kashe ni .
Duk wanda ke da jarumtar kashe Barbushe kuwa har zuwa yanzu Kakan Ubansa bai zo duniyar ba."Waje yayi tsit, kowa na karanto duk addu'ar da ta samu a ranshi.
"Nuratu Kabir zo nan." Cewar Malam Muntasir.
Sai kallo ya koma kansa baki ɗaya.
Lantai kuwa sadda kanta ƙasa tayi tana jin bata ji daɗin zuwansa ba, so tai yau a saka mutanen ƙauyen sharar garin da wanke bishiyoyin ƙauyen yadda sai sun gaji don kansu suna bata haƙuri suna kuka, to amma zuwan Malam Muntasir ya wargaza komi, domin dai duk yadda take son Barbushe bai kai yadda take son Malam Muntasir ba.
Shi kuma Barbushe sai ya ɗauka Yayanta ne na birni Hafiz da take yawan magana don haka sai ya share bai tanka ba, saboda yana son duk abin da Nuratu ke so.
"Nuratu Kabir yaushe kika zama ƴar daba mai kashe mutane ?
Nuratu a she rashin jin naki har yayi yawa haka ?
Nuratu me yasa kika haka ne ?
Kina so mu ɓata da ke ne ?Da sauri ta kalleshi, ("taya zan bari mu ɓata bayan gunka nake samun littafan Jarumi Nasimat? Ai kai duk inda kake dole na zama inuwa a gun na rantse da Allah ƙafarka-ƙafata Malam.")Tunanin da take a zuciyarta kenan wanda ko shakka babu da gaske take.
Zumɓura baki tayi, "Yo ni Malam ramanin za ai dukan da yayi min ai.
Kuma ai daman nace ka daina dukansa nayi Allah ya isa ne daman saboda nasan ta nan zan farke ai, domin ba a Allah Ya isa sai ga wanda kake jin tsoro ni kam ai ba tsoronsa nake ba kasan.
Malam Muntasir sai abin ya ba shi dariya ma.
"Kenan duk wanda kaima Allah Ya isa tsoronsa kake ji ko Nuratu ?"
"Tabbas Malam shi ya sa kaga ban yin Allah Ya isa ni duk gumu sai na fitar da haƙƙina.""To yanzu abin da nake so ki tarkata ƙaurayenki su koma inda suka fito ko ranki ya ɓaci yanzu Nuratu."
Marairaicewa tayi tana son yin kuka.
"Shike nan yanzu Lado ya daki banza ya yaga min littafi a wofi ?"
YOU ARE READING
SAI NAGA MARUBUCI (NASIMAT)
Fantasylabarin wata yarinya ce wadda babu abin da take so a rayuwarta irin taga marubuci Nasimat, ansha bata kyautuka tana maidawa akan marubucin tasha kwana da yunwa akan tunanin hanyar da zata gano marubucin ƙarshe wani malaminta ya cika mata burinta ind...