(AUREN HADI)
::
Tunda khamis ya dawo ya tambayi jawahir ina ummi? sai tace masa tana daki, sai ya ciro wayarsa ya turawa Salman number dinta sannan ya shiga harkokin gabansaUmmi hira kawai take da k'awayenta a group dinsu musamman (RAYUWAR MU A YAU) tana jin dad'in hirar sosai saboda Ana karuwa sosai, 11:30 ta wuce sai taga bakuwar number ta shigo wayarta, dubawa tayi dan taga ko waye sako ne a rubuce kamar haka,
#waya baki izinin buda WhatsApp, sannan me kike har yanzu? take Ummi ta fahimci ko waye, amma tayi niyyar raina masa hankali dan haka ta maida masa, ita ma tace" wanda ya baka izinin bude wa a lokacin da ka bude, sannan abinda kake yi nima shi na keyi" bada jimawa ba ya maido mata yace" karki raina min wayo, ina hira ne da budurwata mai debe min kewa" cikin dakewa tare da karfin xuciya ta mayar masa da martani kamar haka" kenan jirgi daya ya dauko mu ni da kai, dan nima nayi kewar samari na ne shiyasa nake rage dare da su" wani irin takaici ne ya kama Salman dan yasan zata iya aikatawa, mai da mata yayi da cewa" ke bana san iskanci wallahi ki sauka ko kuma ranki ya baci, dariya Ummi tayi ta mai da masa da alamar (murguda baki) take ya maido mata yana fadin wa kike juyama bakin? wallahi ki kiyaye ni" dariya tayi ta koshi sannan ta maida masa" kaga malam dan Allah nifa matar aure ce kake min made idan mijina ya sanka to zai kashe ka, dan haka sai anjima" harta koma cikin group ya aiko da wani sakon dubawa tayi taga yace" har haka mijin naki ke sonki dama?" maida mashi tayi da" sosai kam, yana sona fiye da ransa, nice mahadin rayuwarshi" dariya yayi yace" to ko zan iya ganin photonki da na mijin naki?"cewa tayi" me zai hana, amma karka ce mijin yafi matar kyau idan ka gani" kafin ya aiko ta dunkule photo kusan talatin ta aika masa wanda Jawahir ta tura mata dazu, buda photunan yayi ya fara kallo, sakonta ne ya sake shigowa tace" idan ka gane ni a ciki zan maka kyauta" sai lokacin ya sake duba photunan da kyau, babu inda take ita kadai duk ita da su Jawahir ne sai kuma k'annanta su Islam da Mubbashir, inda ya ganta tare da su Jawahir da Khairat Kwance akan gado tana tsakiyar su, tayi dariya sosai hakoranta sun bayyana ga kumatunta sun lotsa kamar ka saka kwandala kuma ta zauna daram, babu ko digon Kwalli a fuskarta amma tayi kyau, sai ya aika mata yace" wacce tafi zama baka a ciki to ke ce ita, kuma banga mijin naki ba?" dariya ta aika masa tace" ka canka dai-dai, dan haka ka zo da kumatunka ka karbi cadeaux dinka, bani da photon mijina" _tambayarta yayi" ban gane kumatuna ba? me yasa baki da photon mijinki?" mai da mashi tayi" kaga nifa ina da abinyi , dole ne saina samu photonshi? nida nake ganinshi kullum a cikin zuciyata, dan haka sai anjima_ " _tana aika masa ta sauka ta kwanta sai bacci_ .
:Tunda Ummi tayi sallah ta koma ta kwanta sabon bacci, dan rabon da tayi baccin safe harta manta, lokacin da Khamis zai fita yana break ya tambayi Jawahir Ummi, sai tace masa tana bacci dariya yayi yace" to wannan baccin haka take yin shi ko gidan malam manu? inko hakane akwai dangwarma dan shi nasan bashi da da'bi'ar siyan abincin waje, kuma yana fita da wuri to kenan ya yake oho"Jawahir ce tace" ai in fada maka yaya Salman yanzu ya fara gyara mata zama, dan jiya zuwanta nasha labari , nidai har cikina ma ya fara ciwo tsabar dariya" da gaske kike?" ya tambayeta, " eh mana, amma gaskiya yaya Salman baya kyautawa dan inda kaga jikinta duk duka ne,wallahi sai taban tausayi kuma da naga jikinta a farfashe" wani irin iska ya hurar yace" ni nasan dama sai haka ta faru, dan Ummi ba taji, Salman kuma ba yashi da hakuri ga zuciya" to mijina me zai hana kai masa magana akan dukanta, kaga fa hakan babu kyau tunda yanzu tana yin abinda ya sata" ajiyar zuciya ya sauke yace" zan masa, amma sai ya dawo daga tafiya, dan kinsan halin shi murdaddan mutum ne" haka su kaci gaba da tattaunawa harya gama break ya fita.
:
Jawahir ce zaune a falo tana charting, Salman ta gani online dan haka ta gaishe shi ya amsa, tambayar ta yayi ina Ummi tace tana bacci, cewa yayi taje ta tasheta, haka taje tasa Ummi gaba tana magana amma sam taki tashi, dole ta fada masa cewa taki tashi, kiranta yayi ta vedio call yace ta bata wayar, da kyar Ummi ta buda idonta ta kalli wayar sai magagin bacci take da hamma,
YOU ARE READING
Auren Haďi (COMPLETE)
RomanceTayaya ummi da salman zasuyi rayuwar aure wanda da abaya basu son junan su an hada su AUREN HAĎI ku biyoni muji yadda zata kaya