56-60

1.3K 92 0
                                    

(AUREN HADI)
:
:
Sai Da safe ummi ta tashi, wanka tayi cikin dabara saboda kar ciwonta ya jike sosai,  bayan ta kammala ta fito ta shirya, powder kawai ta shafa a fuskarta sai turarenta data shafa a jiki, gajeran siket ta saka ko gwiwa bai kai mata ba, saboda ciwonta gaba dayanshi a baje yake sai bakar riga data dace da zanen siket d'in mai siraran hannaye.

A hankali ta fito falo harta zauna a saman kujera ta mike kafafunta amma bata lura da Salman ba dake zaune akan daya daga cikin kujerun dinning dim, da kayan sport a jikinshi yana shan ruwa tare da sauke gajiya.

Saidai tun fitowar Ummi ya saki baki yana kare mata kallo, in har yace bata birgeshi ba to tabbas k'arya ya fad'a, dan haka ya ci gaba da kallonta har saida takai kallonta in da yake, cikin sauri tace,

"Ina kwana"

Bude baki yayi amma kuma sai ya nemi kowace kalma ya rasa, in'ina ya fara da k'yar ya samu yace mata  lafia

Ita kam ko kallonshi bata sake ba, tashi yayi ya shiga d'akinshi dan yayi wanka, Ummi kam sunna tv ta kama tana kallon d'aya daga cikin malaman dake birgeta wato (malam Lawan Shu'aib Abubakar).

Salman na fitowa kuwa d'akin Ummi ya shiga ya dauko magungunanta, ya juyo zai fito amma kuma sai  ya koma kan madubi yana duba turarukanta, duk wanda ya shinshina baya jin mai wannan k'amshin, gashi kuma ya manta sunan data fad'a masa saboda lokacin baya cikin hankalinshi, harya juya zai fita sai  kuma ya kara dawowa wata 'yar k'aramar kwalbar ya gani ya d'auka tare da karanta sunan dake jiki, cike da farin ciki yace,

"Yes shine arebian oud,

Yana fitowa ya bata maganin yace ta ajiye kafin ya dawo, fita yayi  daga gidan yana shiga mota ya ciro turaren ya bud'e tare da dan shinshinar shi, lumshe ido yayi, a hankali ya bude idon  sannnan yasake maida shi cikin aljihu sannan yaja mota.

Ummi kam tana ganin ya fita tace "to meye ya kaishi daki na?  kodai ajiya yayi bansani ba?"

Yana zuwa gida yaga canji daga wajen Mama, dan kuwa ko gaisuwarshi bata amsa ba, fada kawai ta balbaleshi dashi, wai jiya yasa an yiwa Ummi fada harda mari, bayan kuma laifinshi ne tunda baya sakar mata jikin da zata Saba dashi,

Yayi mamakin jin abinda ya faru a bakin Mama saboda shi bai fada Mata bah, tashin hankalin kuma shine tunda Mama ta sani, to La Mama ta sani kenan kuma abinda ita za tayi tofa ko kad'an bazai masa dad'i ba, saboda baya san abinda zai tab'a lafiyar Ummi yanzu.

Cikin ladabi ya kalli Mama yace "Mama wai dan Allah waya fad'a maku wannan maganar?"

Cikin b'acin rai Mama tace "dama ai kai ba fad'a za kayi ba, to Islam ce ta fad'a min tunda a gabanta a kayi."

Cike da mamaki ya sake maimaita sunan "Islam" gira ya hade kafin ya mik'e tsaye zai fita, cikin fad'a Mama tace "ni tsaya na d'auko maka abincinta ka kai mata"

Cak ya tsaya ba tare daya juyo ba, Mama kuma wucewa tayi tana fad'in "aikin banza kawai, kai d'in wani k'aramin yaro ne da za ace saita baka abinci, idan kana jin yunwa aika sani ka kuma san inda zaka je ka nemi abinci, amma haka kawai a dinga takura yarinya harda bata da lafiyar ma."

Bin Mama yayi da kallo, ganin ta dage tana ta fad'a akan abinda ba laifinshi bane, ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin abinda zai yiwa Islam d'in, saidai kuma ba zaya iya yi mata komai ba saboda mutuniyarshi ce sosai, wata dabara ce ta fado masa in har baya so La Mama ta b'ata ma Ummi rai, to dole ya nemi alfarma wajen Maman.

Mama na zuwa ta mik'a mashi kwanan harda dangwara masa, karb'a yayi yace "Mama dan Allah wata alfarma nake so kimin , in ba damuwa?"

Jin tayi shiru ya bashi damar cewa "dan Allah Mama kuje kuba La Mama hakuri, kunsan halinta wallahi zata iya zuwa har gida kawai dan taci mutuncinta, dan Allah kuce tayi hak'uri, sannan ku nuna mata nine mai laifi kamar yanda kuke ganin nine da laifin abinda ya faru."

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now