50-55

1.6K 92 0
                                    

(AUREN HADI)
:

Matsowa Khamis yayi kamar zai dauki Ummi, saiko Salman ya hankad'eshi yana fad'in" dallah malam gafara daga nan" bushewa sukayi da dariya, shi kuma sunkuyawa yayi ya zura hannunshi ta bayanta ya tallafota, daya hannun kuma ta kasanta nan fa ya ciccibota gaba d'aya.

Kamar zuciyarta zata fasa k'irjinta ta fito haka yake jiyo bugun zuciyarta, yana sama da ita Ummi ta rufe ido ta kau da kanta gefe, Salman kam wucewa yayi su Hajia na gaba suna baya, tafiya kawai yake fuskarnan a had'e kamar hadarin gabas gashi babu wani alamu daya nuna yana jin nauyin abinda ya dauka.

Dan kuwa a tsaye yake kyam, dan shi anashi bangaren kawai bai d'auketa mai nauyi ba duk da kibarta, dan karafan da yake dauka ma sunfita nauyi, suna haka ne wayarshi ta fara ruri, ba tare daya kalleta ba yace,

"Malama fito damin wayata".        

Sai lokacin ta juyo da kanta, a hankali tasa hannu a cikin aljihun rigarshi na gaba ta ciro wayar kamar ta dauko maciji, tana ganin sunan daya fito a screen din take taji hankalinta ya tashi xuciyarta ta cigaba sa bugawa da karfi, domin kuwa gani tayi an saka (SARAUNIYATA)

Hawaye taji  sun zubo mata,  kawai sai  ta jefar da wayar k'asa, Salman na ganin haka ya tsaya cak tare da kallonta yace "meye haka Ummi kina lafiya kuwa, kodai hadarin harda kanki ya taba?"

Kawai saita k'ara fashewa da kuka tana fad'in "azzalumi kawai dama kasan wacce zata kiraka wato sarauniyarka shiy asa kace na dauka dan dai naji haushi ko, to wallahi sai Allah ya sakamin mugu kawai."

Sai lokaci yasan ko wacece ta kirashi, tabbas Nusaiba ce dan ita ya sama sunan sarauniya, (kenan abinda Jawahir ta fada gaskiya ne, Ummi tana kishin shi, to amma miyasa?),.

Kara matseta yayi a jikinshi ya sunkuya ya dauki wayar, tuni har ta fashe, a  aljihu kawai ya saka sannan suka wuce.

Jiniyar kukan da take ne yasa yace "kenan wannan kukan na kishi ne ?"

Share hawayenta tayi tana kallonshi tace "Allah ya sawake nayi kishinka"

Ba tare daya kalleta ba yace "kenan najin dadi ne saboda na daukeki?"

Mutsu-mutsu ta fara tana cewa "kaga ni saukeni dan Allah zanje da kafata, abinda hannun ma sai tauri kamar katako"

Tana fadin haka hannunshi dake kusa da kirjinta ya ida zurawa ya matse mata mama, yar karamar kara ta saki saboda yanda taji zafi, kallonta yayi ya daga mata gira yace "me kika ji 'yan mata?"

Cike da shagwaba tace "Allah saiya sakamin kuma ban yafe ba mugu"

Rufe idonshi yayi lokaci daya kuma ya bude, harga Allah baya so yaji tana fada mashi irin haka, amma ya zaiyi bakinta ya riga ya saba ba zata iya dainawa ba.

Suna kaiwa Jawahir ta bude masu kofa ya ajeta sannan kowa ya shiga suka wuce, gaba d'aya gidansu suka wuce, Hajia saida ta dora ruwan zafi ta barma Salman sallahun ya gasa mata kafa ya kuma tabbatar tasha magani sannan ta kwanta, haka ma mahaifiyarshi saida ta sake jaddada masa kula da ita sannan suka bar gidan, Khamis ne ya mayar dasu gida,

Ruwan nayin zafi ya dauko tare da dan karamin towel, kusa da ita ya zauna inda ta mike kafafunta, towel din ya tsoma cikin ruwa ya fiddo ya matse sannan ya aza mata a kafar, kara ta saki tare da janye kafar da sauri, saidai ina ta manta ciwon da take mata, runtse ido tayi saboda azaba ta fara matso kwalla.

Salman kam in banda dsci babu abinda zuciyar shi keyi masa, ji yake kamar ciwon ya dawo jikinshi zaifi mishi sauki, rike kafar yayi yace "sannu koh, bari nayi maki a hankali"

Mamaki ne ya lullube Ummi dan haka ta saki baki tana kallonshi, a hankali ya dinga gasa mata kafar Ummi kam tun tana jin zafi harta fara jin dadi kallonshi kawai take zuciyar ta na kara narkewa akan son wani abu da bata so taji tana jinshi akan Salman din,

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now