60-65

1.4K 156 0
                                    

(AUREN HADI)
:
:
Ummi tana ganin ya shiga toilet ta bishi da harara tana fadin "kaji min mutum dan Allah kawai sai na kwana a dakinka, ae na san meka shirya min."

Fita tayi daga dakin ko rufe kofar ba tayi ba dan kar yaji fitarta ma, kai tsaye fridge ta nufa ta bude ta dauki madara tasha ta mayar ta dauki ruwa ta kora dasu, zata rufe robar ruwan sai ta fadi ruwan ya zube, ajewa tayi ta nufi cuisine dan dauko abinda zata goge a rashin tsammani ta taka ruwan da ya fallatsa in da ba tayi zato ba, sai ko santshi ya kwasheta tsaf ya ajeta kasa ji kake timm.

Kara tayi lokaci daya kuma ta kama bakinta tayi shiru,  dafa fridge d'in tayi ta tashi tana kallon ruwan, Salman ne ya fito daure da towel a kugunshi gabanta ya fadi saboda ganin ai niyin surarshi duk a mummurde fizgota yayi da karfi bai tsaya da ita ko ina ba sai dakinshi, wurgata yayi akan gado ya koma ya rufe dakin da key ya kashe wutar dakin.

Ummi na ganin haka ta tashi da gudu ta makale a jikin bango gaba daya ta manta da raunin dake jikinta, Salman kam kallonta yayi yace "nace karki fita daga dakin nan amma sai gashi kin fita, bayan kuma kince zaki dinga jin magana ta"

"Ni na rasa me Alhaji ya gani a jikinki da har yayi tunanin kin isa aure, bayan ke kuma har yanzu ba ki da hankali."

Jin bata amsa masa ba yasa ya dauko kayan baccin shi daga toilet, ganin yana  shirin zare towel din daga jikinshi yasa Ummi juyawa tana kallon bango ta daga masa hannu ta baya tana fadin,

"Meye haka malam? dan Allah ka rufa min asiri kar kasa naga ciji ina zaman lafiya na."

Kallonta Salman yayi cikin takun izza ya karaso wajenta tare da juyota da k'arfi ya hadata da bango yana kallon fuskarta yace "meye kuma ciji?"

Sai lokacin ta daga idonta ta kalleshi sai dai yayi kusa da ita sosai, dan haka ta fara in ina " a...amm....amm...e...bbb ba komai"

Gaf da ita ya matso ya hada hancinta da nashi numfashin su na gauraya dana juna tare sarka hannunshi ta bayanta ya rike kunkuminta ya hada kugunsu waje daya, hannayenshi yasa a jikin bango ya dafe gaba d'aya ya rufeta ko ganinta ba ayi.

Cikin wani irin yanayi yayi mata magana "zaki fada min meye ciji, ko sai na nuna maki cijin kin gani da idonki?"

Tana daga idonta kwallan da suka taru suka zubo, gaba daya ta rasa iskan shaka  ga takura da matsatsi ga bakon abinda taji kusa da kugunta yana taba ta, ga kuma  tambayar daya mata tare da cewa zai nuna mata ciji,  da kyar ta fara fadin,

"A..ddd....dan" kawai sai Ummi tayi luuu tana shirin zubewa k'asa, cikin sauri Salman ya tallafe ta yana kallon fuskarta cike da mamaki, kallona yayi yace "yarinyar nan fa suma tayi."

Daukarta yayi ya shinfid'e akan gado sannan ya fara saka kayanshi yana ci gaba da kallon fuskarta yana matukar mamakin suman da tayi, tabe baki yayi yace "matsalar hada hanya da kananin yara kenan, wacce ta suma saboda kusancin da muka samu ni da ita, to ina GA in na kusanceta kenan sai mutuwa kamar yanda ya fada."

Gefenta ya zauna tare da shafa mata ruwan daya dauko a falo,  a hankali Ummi ta bud'a idonta kamar mai jin bacci, tana hada idonta da Salman ta zabura ta mike zaune tana fadin"wayyo Allah dan Allah ka rabu dani wallahi ni ba haka nake bah,

Rumgumeta yayi a jikinshi sosai tare da dora bakinshi a kunnenta ya fara fadib "ya isa haka Ummi ki nutsu babu abinda zan miki, na kawo ki  nan ne saboda Islam bana so taje ta fada cewa ni da ke kowa a d'akin shi yake kwana,  kin santa da surutu shiyasa na kawo ki nan."

Gaskiya kam ta gamsu da abinda ya fada dan haka tayi shiru tana shakar kamshin jikinshi tana sauke numfashi a hankali, bata sake motsawa ba har bacci ya dauketa a kirjinshi.

Gyara mata kwanciya yayi ya mata addu'a yana kallonta na dan wani lokaci, kafin ya mik'e dan ya gabatar da nafilfili dan kusancin da suka samu da ita yanzu yasa service din sa ya fara sauka,  kuma idan ya ci gaba da zama haka to wani abu zai iya faruwa amma duk da haka saida naga ya balli maganin nan yasha kafin ya fara sallah.
:
Har asuba Salman bai idar da sallah ba, saida yayi sallah asuba sannan ya kwanta akan dardumar bacci ya dauke shi.

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now