91-95

1K 70 0
                                    

(AUREN HADI)
:

:

Haka rayuwa ta dinga tafiya tsakanin Salman da Ummi cikin farin ciki da kaunar juna, sun dunkule sun zama d'aya yayin da suka zama abokan juna suna hira da kuma shawartar junansu akan duk wani abinda ya shafesu.

Lokaci gudu yake yayin da kowace awa ke wucewa cikin gaggawa, kwana kuma tamkar kyabta idone a lokacin kuma kwanaki ke taruwa suna zama shakara, a haka kuma har aka fara kidaya shekaru.

*BAYAN SHEKARA HUDU*

Abubuwa sun faru da dama na ciki a wannan shekarun, Ummi ta kammala karatunta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali tare da taimakon mijinta d'aya tilo kuma gwarzonta, wato Salman.

Tun kafin Ummi ta kammala karatunta Salman ya mayar da ita 'yar kasuwa ta hanyar siyo mata takalma da jakunkunan mata tana siyarwa, duk abinda Allah yasa ma albarka to tabbas akwai nasara da ci gaba a ciki, tun ana kawo mata guda hamsin har aka fara kawo mata guda dari har dari da hamsin daga nan kuma sai ya fara kawo mata less, atamfofi, material, da boyel, da mayafai, hade da takalma da jakunkuna.

Kasuwanci na tafiya yanda ya kamata saboda jajircewar Ummi akan harkarta, ko kadan babu wanda ya isa yayi wa Ummi wasa da al'amarin kudinta, tofa za kaga tijara tana da saukin kai wajen mu'amula amma idan ka fara mata wasa da hankali wajen biyan kudi to ba zaka ji da dadi ba, lokuta da dama Salman yakan sha dariya idan yaji tana waya tana fada akan kin biyan kudi, wani lokaci kuma yakan sa ta daga wa wata kafa musamman idan yaga mai shirin biya ce, duk lokacin da zata tafi karbar kudi da kanta to Salman ne ke kaita in dai har yana gari, in kuma basuyi tafiya tare ba saboda karatu to dama ya bata izinin zuwa ko ina in dai akan maganar data shafi kasuwancinta ne akan babur d'inta daya siya mata.

Yanzu dai haka Ummi ta zama gwaska a kasuwancinta, tana yinshi yana kuma tafiyar mata yanda take so, yanzu haka burinta d'aya take so ta cimma wanda ta shawarci Salman ya kuma girmama tunaninta.

Salman kanshi yanzu duk wani abu da zaiyi mai mahimmanci to saiya shawarci Ummi akai, akwai lokacin da wani mutum ya bashi fili a maimakon kud'in da yake biyarsa, suna zaune da Ummi ya kira Khamis yana fad'a mashi cewa bai san yanda zaiyi da filin ba, dan haka kawai ya samo masa mai siya ya sayar dashi, Ummi na jin haka tayi shiru saida suka kammala hira ya kashe waya sannan ta gyara zama tana kallonshi cikin nutsuwa tace,

"Mon sweet, saina ji kamar kuna magana akan zaku siyar da filin ko?"

"Eh, ina so in siyar dashi, dama na karb'a ne saboda in ban karb'a ba to bai zama lallai kud'in su fito ba."

"Amma da ba zaku damu ba da nace wani abu?"

Murmushi yayi yace "damuwa kuma, tame kenan? fad'i kawai ina jinki."

"Sai nake ganin fili kadarace bai kamata ku siyar ba, wanda ya baku shi ya baku ne saboda rashin sanin mahimmancinshi da kuma rasa yanda zaiyi, shi yasa nake ganin me zai hana ku tayar da gini a wajen tunda kunce filin yana cikin mutane ne akan titi, kunga kenan zai iya yin amfani."

"To ke yanzu me kike ganin ya kamata ayi a wajen idan an gineshi?"

"Zaku iya tayar da shago a wajen, ko dai ku dinga zuba kayan da kuke kawowa, ko kuma ku mayar dashi wata babbar super market in har kuna ganin aljihunku yana da nauyi zaku iya yi, amma fa wannan tunanina ne."

Wani kallo ya bita dashi ya jima yana kallonta, hakan yasa ta tsargu dan bata san me kallon yake nufi ba, fad'awa tayi jikinshi tana fadin "kuyi hakuri dan Allah idan na fad'i wani abu ba daidai ba, shawara ce kawai."

Rumgumeta yayi sosai a jikinshi yace "Ummi na kin had'u sosai gashi kin bani shawara akan abinda banyi tunaninshi ba, nagode sosai kuma insha Allah zanyi yanda kika ce."

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now