(AUREN HADI)
:
Ummi tayi nisa sosai a cikin baccin taji ana tsawa, zunbur ta tashi zaune tare da rike robar madarar da takea bacci ya dauketa, ganin babu wuta a d'akin sai duhu yasa ta fara kara tana fad'in" yaya Salman, dan Allah ka zo, wallahi tsoro nake ji, dan Allah kayi hak'uri ka zo, Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un shikenan mutuwa zanyi" shiru tayi dan tasan ba zai zo taimaka mata ba zanin rufa taja ta k'ank'ame a ciki tana rawar jiki.Cike da k'asaita ya shigo d'akin da wayar shi a hannunshi, gefen gado ya ajeta ya zauna ya mik'e k'afafunshi saman gadon ya jingina bayanshi tare da rumgume hannayenshi a k'irjinshi sannan ya kalleta yace" haka ya maki?nasan za kice tsoro kike ji ba zaki iya bacci ke kad'ai bah ana ruwa, to gani sai ki kwanta yanzu." ya k'arashe maganar da hararenta turo baki tayi a hankali ta sulale ta kwanta tare da gyara rufarta nan-danan bacci ya sake gaba da ita.
:
Makara yayi wajen tashi ko da Salman ya farka gari har yayi haske sai lokacin yaga yanda ya kwana daga zaune, juyawa yayi ya kalli Ummi sai yaga ba tanan mamaki yayi ta tashi amma ni ta k'yaleni, tashi yayi ya nufi d'akinshi ya na ta matsar wuya saboda ciwon da yaji yana yi masa, sallah yayi ya sako kayan sport ya fito dan ya yaje bayan gidan a wani hankad'ed'en d'aki in da yasa aka gyara shi ya zuba kayan motsa jiki, Ummi ya gani tana Aje kwanuka a dinning ba tare da ya tsaya ba yace" ki biyo ni da jus mai sanyi" jiki na rawa Ummi ta bud'a fridge ta d'auko dan yanzu kam harga Allah tsoron Salman ya kamata, saida ta kai farfajiyar gidan saboda sanyin da taji na ruwan da aka sha jiya ta tuna doguwar riga ce a jikinta wacce ta d'ora a kayan da ta kwana da su, juyawa tayi da nufi ta d'auko hijab Salman ya juyo yace" zaki wuce ko sai rai ya b'ace" wucewa tayi da saurinta harya bud'a d'akin suka shiga, kallo Ummi take sosai yanda aka k'awata wajen mik'a mashi jus d'in tayi dan ta koma in da ta fito, hararan daya mata yasa ta sunkuya ta aje ta tashi zata fita yace" zo nan, kinga waccen k'arfen shi nake so ki d'auko min" kallan k'arfen tayi taga ko zai kasheta ba zata iya d'aukarshi ba,dan haka ta juya ta kalleshi tace" yaya Salman ba zan iya d'aukar shi ba wallahi" wata kyakyawar waya ya d'auka yana shirin zuk'a mata ta nufi wajen k'arfen a guje ta fara 'ko'karin d'aga shi, ganin ta kasa yace ta d'auko na kusa da shi shima bata d'auko ba saida kanshi yazo ya d'auka ya fara d'agawa k'wanji na fitowa da jijiyoyi haka ta saki baki tana kallonshi, yana gamawa ya d'auki ball ya fito tsakar gidan ya fara bugawa, haka kawai Ummi taji tana san ta yi ta kallonshi yanda yake ball d'in da kuzari da salo, Salman na ganin ta saki baki ya jefo mata ball d'in da nufin koda xata sameta ta sameta a in da ba za taji ciwo ba, sai ko a fuskar Ummi ji kake Timm ball ta mare ta, dukewa tayi tare da rufe fuskarta, jin ba tayi kara ba yasa Salman tunanin ba taji zafi ba, d'aukar ball d'in yayi ya ci gaba da bugawa saida yaga Ummi ta jima bata d'ago ba ya zo kusa da ita, sunkuyawa yayi ya d'ago da kanta take gabanshi yayi wata mummunar fad'uwa saboda ganin idonta na dama ya kumbura ga jini ya kwanta abin tausayi" oh mon Dieu, pardon Ummi kinji bansan haka zata faru ba dan Allah kiyi ha'kuri" hawayenta ta goge ta mike tsaye tace" ba komai akwai Allah" wucewa tayi d'akinta nan ta fara sabon kuka kamar da bakin kwarya.Jikinshi ne duk yayi sanyi da yaji tace akwai Allah, Allah kuma ba azzalumin bayinsa ba ne dole zai mata sakayya, aje ball d'in yayi ya koma ciki saida yayi wanka ya shirya cikin k'ananan kaya wanda suka karb'e shi matuk'a sun masa kyau ga k'amshin turarenshi mai sanyaya zuciya, haka ya shigo d'akin Ummi ya sameta tana ta kuka a tsakiyar gado, sai ya ji baiji dad'in hakan ba tausayi ta bashi sosai ( k'aro na farko kenan a rayuwar Salman da ya ji tausayin Ummi har cikin zuciyar shi) zaune yayi cikin muryar rarrashi yace" Ummi dan Allah kiyi ha'kuri ki yafemin, wallahi banyi nufin ta sameki ba" d'ago da fuskar tayi yanzu kam gaba d'aya fuskar ta d'an kumbura ido sun ida yin ja saboda kuka, kau da kanshi yayi kai lokaci d'aya kuma ya kalleta yace" kin yafemin Ummi?" bata tanka saba haka yaci gaba da rarrashinta har saida yace" dan Allah Ummi ki yafemin, wallahi ba zan iya kwana dà alhakinki a kaina ba Ummi kin had'ani da Allah kinsan kuma dole zai maki sakayya, kiwa Allah ki yafemin kinji, in kuma ba zaki iya ba to ki fad'i abinda kike so nayi sannan ki yafemin?" sai lokacin kad'ai tayi magana tace
YOU ARE READING
Auren Haďi (COMPLETE)
RomanceTayaya ummi da salman zasuyi rayuwar aure wanda da abaya basu son junan su an hada su AUREN HAĎI ku biyoni muji yadda zata kaya