Part 11-15

1.4K 92 0
                                    

An nufi da amare gidan mazajensu inda kuma ummi suka tafi gida tare da Mahaifiyarta, dama gidajen su suna kusa ne, suna shiga ďakin ta ta shiga ta soma sabon kuka har saida bacci ya dauke ta duk da la mamma najinta amma ta kyaleta dan yanda ta ďauki salma ba ta ďauki ummi haka ba shiyasa bata ga abin ďaga hankali aciki ba.

Ckin dare ummi ta farka ta fito ta buďa fridge da ďauki madarar shanunta wanda mahaifin ta ya sabar mata shanta tun tana k'arama yanzu haka in bata sha ba kanta ke ciwo tana sha ta koma ďaki tayo alwala tayi sallah isha'i da batayi ba ta ďauki Al'Qur'ani tayi karatu tayi karatu sannan ta kwanta.
Tana tashi da safe la mamma tasa aka fara mata gyaran jiki mai zafi dan basuda lokaci wanda aka basu kaďan ne.

Kwana ukku aka kwashe har yanzu basu haďu da salman ba, Abba ne kadai ke rarrashinta dasu hajiya idan suka zo gidan sai kuma mamar salman in wato HAJIYA HALIMA, yau kam mahaifiyar salman ta tiso shi gaba akan yazo yaga matar shi ba karamin ďaci yakeji ba idan yaji sun kira ummi da matar shi haka ya daure yazo gidan, tinda tayi sallah magriba bata sake fitowa ba sabida kiran da jamaal yayi mata, buďe kofar da taji ne yasata saurin aje wayar tana muzurai duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, kallan tuhuma salman yake mata har ya k'araso inda take cikin rashin yarda yace,

"Mi kike yi dawa kike waya"?" Wata harara ta dalla mashi tace" to ina ruwanka dani miye matsalarka? " hannunta ya fizgo da k'arfi ya karbi wayar ya duba number ce babu suna dan haka yace " dawa kike waya?" Cikin bacin rai tace"a'ah malam wai miye haka ina ruwanka dani toh?" Cikin hasala ya matse mata kumatu yana faďin" bana ciki da iskanci kar ki dauke ni sakarai ni yanzu mijinki ne dole nasan mi kike aikatawa" duk da tayi kokarin fizge hannun ta amma ta kasa dole tace "aww kenan kai ka dauka da gaske ni matar kace, to wannan kishi ne ko mi"? Sakinta yayi yace "Allah ya tsareni nayi kishi akan ki, wallahi ke kinsani in banda darajar aure ke baki isa in kiraki da matar aure na ba" nunata yayi da wayar yace "daga yau babu ke babu waya har lokacin dana gadama ki rike" wucewa yayi zai fita da sauri ta sauko daga gadon ta tare shi tace " kaga malam dan Allah bani wayata sai kace wani kai ka siya min ita " nuna mata wayar yayi yace "ki kwata mana idan kina da karfi" shiru tayi tana kare mishi kallon tasan bazai bata ba dan haka tana gani yasata cikin aljihun rigarshi sai ko tasa hannu, cabke hannun yayi ya murďe mata yan yatsu yana fadin "mara kunyar banza, sai ki saka ma mutum hannu cikin aljihu wannan salin halin b'era kenan" duk da tana jin zafin murďar da yake ma hannun ta bai hana tace " b'eraye ai kaine babban b'era gashi kamin gaba da waya "tsaki yayi ya gifta ta ya wuce ya bar gidan, su abba ne zaune suna cin abinci kallan La mamma yayi yace " wai ina ummi take ne?" Tab'e baki tayi tace "tana daki mana tunda ta dora ma kanta lalura"girgiza kai yayi yace "ki dinga hakuri mana kema, kiyi la'akari da yanda nata auren ya kasance ba kamar na kowa ba, itace ta farko a familyn nan da aka mata aure babu saka rana bare goro kiyi mata uzuri koh" kara tab'e baki tayi tace" amma miye na damuwa aciki Salman dan uwanta ne tasan shi tunda tare suka tashi toh miye sabon abu aciki?" Hakane amma kinfi kowa sanin tsakanin ta dashi, ba shiri suke ba "to ai auren da ka haďa su kaga sai su fara shirin watak'ila ma su fara son junan su nan gaba kaďan" to Allah yasa haka, idan haka ta faru ai zamu fi kowa jin dadi" gaskiya ne allah ya tabbatar da alkhairi, ya basu zaman lafiya" Amin inji Abba.

Haka aka k'ara wani kwana ukun ana gobe ummi zata tare an gama kintsata yanda ya kamata kama daga kunshi kitso gyaran jiki har dama gyaran daki,gobe ake jira tayi saidai duk abinda allah ya tsara zai faru to babu makawa, ummi ce da kewa da damuwa tai mata yawa ta dauki wayar La mamma ta kira Jamal sabida irin soyayyar da yake mata tana jin daďi dan shine na farko da ta fara soyayya dashi, hira sukayi sosai har saida yace mata "kinsan wani abu a gaskiya ina son na sake ganinki"? Gabanta taji ya faďi sai ta dake tace "um a gaskiya bazai yiwuba" da sauri yace "miyasa ummi bakisan gani na ne"? Cikin i'ina tace "ba haka bane kawai dai akwai matsala ne" matsala kuma ta mi? Rasa abinda zata faďa mashi tayi don haka yace "zanzo gidanku yanzu ruwan ki ne ki fito ko ki'ki fitowa amma kisani ko baki fito ba ni har cikin gidan zan shigo inda na ajeki a ranar da muka fara haďuwa da ke" kashe wayar yayi ya bar ummi baki buďe gabanta ya tsananta faďuwa.

Minti talatin kenan Jamal ya kira Ummi yace gashi nan kofar gida ta fito ko ya shigo tunda shi da aure yake santa, cewa tayi ya jira ta a bayan gidansu tana zuwa, duk da tace mishi tana zuwa amma ta ďauki kusan minti sha biyar sannan ta fito ba tare da kowa yaga fitar ta ba, tana so ta fada mashi akanta da auren da auren da aka ďaura mata dan taba shi hakuri suyi sallama.

Alhamdulillah 🙏

Sorry for not updating ina exams ne amma yanzu everything is normal i will update everyday😍


Please show some love by voting and comments 🙏💖

Love you all❤

Maaemerh♡

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now