46-50

1.4K 85 6
                                    

(AUREN HADI)
:

:

Tunda safe haka Ummi ta tashi sukuku jiki babu kwari, Jawahir ce ta fada ma Khamis halin da take ciki, kiranta yayi tana zuwa da kanshi ya zuba mata abinci a plate ya aje mata tare da fadin" maza cinye ki bani plate d'in"

Kallonshi tayi tace" yaya Khamis ko zanci ba zan iya cinye wannan ba" yanda ya hade rai yace" Ummi ina wasa dake?" kai ta girgiza tace" kayi hakuri yaya Khamis wallahi yamin yawa"

"Ke, ina wasa dake ne, za kici ko saina takaki?" tsawar daya mata ce tasa tayi saurin jan plate din a gabanta ta fara kai loma baki, Jawahir ma 'yan cikinta ne suka kada, Ni kaina sai da na saki birona amma cikin zafin nama na cafe shi sannan na CI gaba da dauko muku rahoto,

Tana ci tana kuka tana rokonshi ya isa haka, amma ya tsareta saida ta cinyeshi duka ta bashi plate din tunda uwar Ummi ta haifeta bata taba cin abinci mai yawan haka ba, shiyasa Khamis na fita Ummi ta fara tsula amai, abin ya daga hankalin Jawahir dan da farko tayi tunanin idan ta amaye abinci zata daina, amma sai taci gaba da shekashi.

Cikin tashin hankali ta fara kiran Khamis ta fada mashi halin da ake ciki, cikin tashin hankali yace da ita "gani nan zuwa saimu kaita asibiti"

suna cikin jiranshi,sai  Salman ya kiran Jawahir dan tunda ya tashi bai fita ba, gaba dsya hankalinshi ya koma gida, hakan yasa ya kira iyaye maza da mata da kakannin amma saiya ji baibar kewa da damuwa na gidan ba, dole ya kira Jawahir ya tambayeta Ummi.

Tana dauka cikin damuwa tace "assalama alaikum, ina kwana yaya Salman?" gabanshi yaji ya fadi da kyar ya daure yace "lafiya lau, kun tashi lafiya?"

Kamar zata fashe da kuka murya na rawa tace "yaya Salman da sauki dai, kaga Ummi nan tana ta amai wallahi, nifa na fara jin tsoro" cikin daga sauti yace "amai kuma, me yasa meta to?"

Cikin kuka tace "yaya Salman daga taci abinci fa shine take amai "innalillahi wa'inna illaihir raju'un, kinga bata wayar" ya fad'a tare da nuna tsantsar damuwarshi a fili.

Mika mata wayar tayi, wata harara ta wurga mata tare da kau da kai, maida wayar tayi a kunne cikin sanyin murya tace "yaya taki karbar wayar" abun mamaki na dauka Salman zaiji haushine, amma sai naji yace "Jawahir karki min karya, ki fad'amin abinda ke damunta?"

"Yaya Salman nima bansan me yake damunta ba, amma dai jiya ta fadamin wani abu wanda nake tunanin kaine silar shigarta wannan halin" cikin rashin fahimta yace "bangane ni nasa taba?"

"Eh yaya Salman amma kayi hakuri nima zato ne nake, amma banda tabbaci hakan, cikin jin haushi Salman yace "naji ni fadamin me ta fad'a maki?"

Duk da tana dar dar dashi haka ta daure ta fada masa duk abinda Ummi ta fada mata jiya, dariya yayi yace "Jawahir lallai yarinya ce ke, waya fada maki ana kishin wanda ba'a so?"

Saida ta sauke ajiyar zuciya tace "yaya Salman ai macen kenan, tsamar dake tsakaninku ba zata hana zuciyoyinku fallasa sirrin dake cikin taba, ko bata sonka zata iya kishinka saboda akwai aure tsakaninku, kamar yanda da zaka ganta da wani namiji za kaji zafi a zuciyarka,, amma idan aka fahimci hakan zaka iya wayancewa ta hanyar cewa kana san kare martabar aurenka ne dake kanta, kaga kenan dan tayi kishinka ba abun mamaki bane."

Shiru yayi yana tunanin abinda ta fada, murmushi yayi kamar yana gabanta yace "Jawahir ban taba jin alamun haka a raina ba, ko zanyi soyayya zanyine da wata daban amma ba Ummi ba, yarinyar da idan naganta sai gabana ya fad'i saboda tunanin abinda zata min musammam idan ina cikin mutane"

Dariya tayi cike da jin karfin gwiwa tace "Yaya Salman ai faduwar gaba alamune na so" dariya yayi yace " ke Jawahir banasan sharri, ke har kinsan alamomin so?"

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now