106-110 (LAST PAGE)

1.3K 68 3
                                    

(AUREN HAD'I)
Finale

Salman ne zaune k'asa ya mike k'afafu yasa robar wankan yara tsakiyar k'afafunshi da Taufik' a hannunshi yana masa wanka sai lumshe ido yake alamar bacci yake ji, Ummi kuma na gefensa da Rafik' tana shiryasa cikin k'ananan fararen kaya masu kyau, masha Allah yaran sun girma dan har sun iya zama suna k'ok'arin fara rarrafe, wasa take masa shi kuma yanata dariya yayin da kumatunshi keta lotsawa ciki kamar na Ummin, doguwar hammar da Salman yayi ce yasa ta kalleshi amma ba tace dashi komai ba, saida ya k'arasa sannan tace "haba 'yallab'ai irin wannan doguwar hamma haka, duk ta kwanan ce?"

Cikin muryar bacci yace "Eh mana, ya kike so nayi to? tunda kin kasa barina nayi baccin."

Tab'e baki tayi tace "hum, to nidai ka kula karka sakawa yarona kunfa a hanci, dan in haka ta faru ba yarda zanyi ba." ta k'arashe tana murguda baki.

Kallonta yayi yace "ke yanzu ko kunya ba kiji ba da ki kace d'anki, to d'anki dawa ya baki?"

Cikin kuri tace "Allah ne ya bani."

Ci gaba yayi dayi masa wankan yana fad'in "hum, amma kuma har yanzu baki san yanda zakiyi kiyi masu wanka ba, watansu biyar a duniya amma bana jin kin tab'a masu wanka ko sau d'aya."

Turo baki tayi gaba tana fad'in "to ai dai zan iya nima, kuma ae kaine kace kun d'auki alhakin yi masu wanka , dan haka ni kuma bana masu."

Kallonta yayi yace "shi yasa kenan kike tayar dani daga bacci yanzu dan nayi masu wanka?"

"Eh mana." ta fad'a tana sumbatar kumatun Rafik' data gama masa shirinsa.

Yana gama d'auraye ma Taufik' jikinshi ya sakashi cikin towel ya mik'a mata ta karb'a dan ta shiryashi, mik'ewa yayi tsaye yana fad'in "dan Allah kiyi zuciya ki iya yi masu wanka da kanki, sannan zanje na kwanta kiwa Allah karki tasheni ki bari na k'arasa hantsewa."

Hararan sama da k'asa tayi masa kafin tace "sannu, na barka kuyi bacci?ai bazai yiyu ba tunda baku gama dani ba."

Dafe k'ugu yayi da duka hannayenshi biyu yace "duk ni kad'ai keda wannan hararan? to na gode, amma dan Allah ki barni na huta, kefa kinfi kowa sanin gajiyar dana deb'o kuma ban shigo garin nan ba sai cikin dare har kunyi bacci, amma shine duk da haka kin kasa barin mijinki ya huta."

Dariya tayi tace "shikenan kaje ka kwanta, ba zan tayar dakai ba, amma zan shigo kai min wanka ka shiryani saboda lokaci yayi na tafiya gidan Alhaji, ko ka manta yau k'arshen wata ne?"

Wucewa yayi yana fad'in "to ni dai zan kwanta ba yanzu zanje ba saina huta gajiya."

Tana gama shirya Rafik' cikin shiga irinta Taufik' ta ajiyeshi kusa da Taufik', ita kuma ta d'auke robar da akayi masu wankan ta gyara wurin sannan ta aje masu kayan wasa a gabansu ta sunkuya tace masu "zanje wajen papanku yamin wanka, kuyi wasa kafin na dawo."

Tana fad'a ta shiga ciki, kwance ta sameshi cikin blanket, yaye blanket d'in tayi ta haura kan gadon ta hayeshi ta fara mashi magana cikin kunne "ka tashi kafin na tayar dakai"

Saida ya k'ara dunk'ulewa yace "um um, ba zan tashi ba, dan Allah ni ki d'agani kin wani zo ki sakar min nauyinki."

K'ara mak'alewa tayi a jikinshi tace "wallahi ku tashi kafin na tayar dakai kasan dai zan iya ko?"

"Nak'i d'in, kiyi abinda za kiyi." ya fad'a yana tutsa kanshi tsakiyar pillow.

Dagewa tayi iya k'arfinta ta fara k'urma mashi ihu cikin kunnen b'arin dama, k'ok'arin rufe kunne ya fara dan haka ta rik'e hannayenshi duka biyu, haka suka dinga turmushe turmeshe akan gadon saida yayi sarander ya d'aga hannayenshi yana fad'in "shikenan nayi sarander."

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now