*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
@hadiza-isyaku2
*Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su ga tabbata ga masoyinmu kuma masoyin _Sahabi Mus'ab bin Umair_ 😍, Annabi Muhammad S.A.W, Baban Ibrahimul Mu'azzam da Abdallah.*
*_Wannan Littafi Ƙirƙira ne, ban yi don cin zarafin wani gari ba. Asali ma littafin na ƴan kowane gari ne, idan kina kano, toh ki ɗauke shi a matsayin KISHIYAR KANO, na sa jihata ne don ni ƴar Katsina ce, ke ma ki kalli labarin da sunan Jiharki, ta haka ne zaki fahimce shi._*🙏🏼
*Wannan shafin sadaukarwa ne ga kowa ce _Uwargida_, albarkacin Jikalleta ~Nana Aicha*🤝🏼
*Shafi na Ɗaya*
Durƙushe take a gaban mijinta mai suna Khamis, wanda ke zaune a gefen gado yana ƙare mata kallo. Idanunta cike da ƙwalla ta dube shi tare da yin magana cikin raunin murya ta ce "Ni fa ban ce zan hana ka ƙara aure ba, kawai dai Ƴar Katsinar ce bana so".
Ɗago kafaɗunta ya yi tare da faɗin "Tashi ki zauna", ƙasan ransa kuma yana mamakin sauyawarta na lokaci ɗaya, don tunda ya fara zancen ƙara aure take ƙoƙarin danne kishinta, amma da jin ƴar Katsina ce zai aura sai rauninta ya rijayi ƙarfinta.
Bayan ta zauna a gefenshi ne ya jefo mata tambaya cikin taushin murya "Meye aibun matan Katsina da bakya son in ƙara aure da su?".
Kara raunana murya ta yi sannan ta ce "Kowa ya shaida *Katsinawa mugun asiri gare su* yanzu kana auro ta sai ta raba mu da kai, ni kuma shi ne bana so".
Ko da jin hujjar da ta bayar ya gane ƴan zuga ne kawai ke son rikita mata lissafi, saboda ba inda ta san Katsinawa bare ta yi musu wannan muguwar shaidar. Cewa ya yi "Kin taɓa ganin wanda suka yi ma asiri?".
Shiru ta yi saboda bata taɓa gani ba.
Ya ce "To Aysha ki dena kula 'yan zuga, don ba inda zasu jefa ki sai cikin rudani".
"Wallahi ba wani ƴan zuga a nan" ta faɗa tare da sake fashewa da kuka, saboda ta fahimci ƙorafinta bai karɓu ba.
Yadda take kukan ne ya ba shi tausayi, lallashin ta ya shiga yi da maganganu masu tausasa zuciya. Ya ce "Aysha ki kwantar da hankalinki, bana jin ƙarin aurena zai rage ko da ƙwayar zarra na son da nake maki, kuma yarinyar da zan aura kowa ya shaida bata da matsala, don haka nake da yaƙinin ba zata taɓa zama matsala a gare ki ba".
Ido ta lumshe tare da
haɗe gululun da ya tokare mata zuciya, a ɓangare ɗaya kuma tana ganin tunda har zai mata kishiya alhalin haihuwarta biyu, to ba wani sauran sonta a ransa, kawai dai yana faɗin haka ne don ya kare kansa.Ba zata iya fitowa kai tsaye ta ƙaryata shi ba, sai dai ta yi mashi hannunka mai sanda ta ce "Ba zan yi maka musun so ba, amma ba sai ka ɓata lokacinka wurin faɗa ba", rufe bakinta ya yi daidai da fitar siraran hawaye a Idanunta, bayan hannu ta sa ta cigaba da gogewa.
Kai kawai ya girgiza, don ya san kishi ne ke ta ɗawainiya da ita. Bai fasa lallashin ta ba, don ba zai so ta ce ya wulaƙanta ta saboda ƙarin aure ba.
Jin shi kawai itama take, mafarin yana fita ta kira Aminiyarta mai laƙani da Zuzee a waya, labarta mata yadda suka yi da Khamis ta yi, saboda ita ke tsara mata komai.
Tsaki Zuzee ta ja tare da faɗin "Ke rabu da shi, ƙaryar so yake maki, kuma don yana son yarinyar ne yake wani kare ta, amma waye bai san mugun halin Katsinawa ba".
Tsoro bayyane a fuskar Aysha ta ce "To Zuzee ya zan yi da shi, wallahi tsoron asiri nake".
"Ki kwantar da hankalinki, muma ai mun iya shige-shigen".
