*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
https://m.facebook.com/Hadeeza-Isyaku-Novels-107323887468827*Shafi na Uku*
Khamis kuwa ɗakin Maryam ya koma. Sai dai bai bari ta lura da damuwar da ya fito da ita daga ɗakin Aysha ba. A gefen gadon da ya bar ta zaune a nan ya same ta, bai kuma yi mamaki ba don ya san motsi mai ƙarfi ma wahala yake mata.
"Baiwar Allah, har yanzu kina nan?", ya tambaye ta cikin sigar zaulaya, lokaci ɗaya kuma ya tsugunna suna fuskantar juna.
Sosai ya bata dariya, sai dai zazzaɓi da murar da ke damun ta ne suka hana ta dariyar, sai ma ta shasshaɓe fuska kamar zata yi kuka.
Yana na ganin haka kuwa ya marairaice fuska tare da faɗin "Sorry ƴar gidan Khamis, har yanzu ƙafar?", kai ta girgiza "A'a".
Sai da ya koma gefenta da zama ya sake tambayar ta "Toh miye ke damunki?", sannan ya kwantar mata da kai a faffaɗan ƙirjinsa.
Hannunsa ta kamo ta sa a wuyanta, murya can ciki ta yi magana "Zazzaɓin nake ji kamar zai dawo"., Idanunsa a lumshe, yayin da kuma hancinsa ke shaƙar ƙamshin dake fitowa a ƙananun kitson dake kanta ya ce "Oh Sannu! Yanzu zan fita sai in karɓo maki magani kin ji, hada na tarin da ke damunki ma"."Uhmm" kaɗai ta iya cewa tare da lumshe idanu, saboda ɗumin jikinsa dake ratsa duk wata gaɓa ta jikinta, cikin ɗan lokaci ta ji kamar ba zazzaɓi take ba.
Khamis ma har yanzu Idanunsa a lumshe suke. Sai dai nutsuwar da yake ji a yanzu bata hana shi mamakin abin da Aysha ta yi mashi ba, a hankali ya sauke numfashi tare da tambayar kansa "Shin kishi ne ya sauya Aysha, ko wani daga gefe yake zuga ta?".
Kafin ya samu amsar tambayarshi ne ya ji Maryam na shirin zame jikinta daga nashi, buɗewar idanunsa kuwa ta yi daidai ta fitowar tari mai kartar ƙirji daga bakinta.Sannu ya riƙa yi mata, bayan tarin ya lafa ya ce "Bari dai in tashi".Miƙewa ya yi, sannan ya taimaka mata ta gyara kwanciya, bargon dake ƙasan ƙafafunta ya ja mata har zuwa kafaɗa.
Zuciyarsa cike da ƙaunarta ya duƙo saitin fuskarta tare da faɗin "Honey, kada ki yi bacci, yanzu zan dawo Insha Allah". Ɗan ɗaga kai ta yi tare da jifar shi da tattausan murmushi, shima murmushin ya maido mata, lokaci ɗaya kuma ya manna mata kiss a goshi.
"A dawo lafiya" ta yi mashi, sannan ta raka shi da idanu har ya fice daga ɗakin.
Duniyar tunani mai cike da farincikin samun Khamis a matsayin miji ta lula. "Shin akwai abin da ya kai kasancewa da masoyi daɗi?", a cikin zuciya ta jefa ma kanta wannan tambaya. Sanin "Babu" ita ce amsar ya sa ta yin godiyar Allah a fili, sannan ta ɗora da "Allah kada bari wani ko wata a cikin bayinka su hanani jin daɗin rayuwa da mijina". Saboda ta san a gabanta akwai ƙalubale mai girman gaske, don yadda Aysha ta fito da kishinta a fili da wahala su zauna lafiya da ita. Ita kanta a yadda take jin ina ma ita kaɗai ke da Khamis, sai ta yi da gaske sannan zata dena ƙin duk wani abu da zai raɓe shi.
A nashi ɓangaren kuwa, kai tsaye gidansu ya nufa, inda ya samu mahaifiyarshi, ƙannensa da kuma jikokin gidan a katafaren falonsu suna hira.
Tun kafin ya zauna yaran suka gaishe shi, lokaci ɗaya kuma suka zura idanu kan blue ɗin food flask dake hannunsa, tsammanin kowanen su girkin Amarya ne a ciki.Ummansa ma wadda kana ganinta zaka gane ita ya biyo a wurin kyau da kwarjini ta ce "Ango ne da kansa".
Bai wani ji kunyar cewa "Ni ne Umma" ba, tunda ba wannan ne aurensa na farko ba.
Baki a washe ya zauna kan kujerar dake kallon wadda take zaune. Cike da ladabi ya miƙa mata gaisuwa.
Amsawa ta yi tare da tambayar sa Amarya da Uwargida. Bayan ya tabbatar mata da lafiyarsu ne suka cigaba da hira jefi-jefi.
Ƙananun yaran dake falon kuwa ƙagare kowannen su yake ya ji Khamis ya ce ga girkin Amarya, Musamman autansu mai suna Salim da ke mutuwar son abincin maƙota.
