*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
@hadiza-isyaku2*Shafi na Takwas*
Aysha kuwa ɗakinta ta koma tare da ɗaukar waya, duk don ta rage ma kanta zafin hana ta zuwa kitso da Khamis ya yi.Jerin gwanon missed calls ɗin Zuzee ta gani a duka layikanta dake cikin wayar.
Zama ta yi a gefen gado lokacin da ta danna kira ga number Zuzee, "Haba baiwar Allah, ba zuwa ba aike, ko mun maki laifi ne?", abin da Aysha ta faɗa bayan Zuzee ta amsa kiran.
Dariya Zuzee ta yi daga cikin wayar sannan ta ce "Yi haƙuri ƴar'uwa, wallahi tun washegarin walimar Amaryarki wayata ta ɓace, kuma ko ba wannan ma ai gidanki yanzu bai zuwuwa, don ana ganin mutum na zarya za a ce munafunci ya kawo shi".
Ƴar guntuwar dariya Aysha ta yi tare da faɗin "Haba don Allah, ke dai baki yi niyyar zuwa ba kawai".
Zuzee da ta fi ta iya zaman duniya ta ce "Ke dai".Gaisawa suka yi, Aysha kuma ta jajanta mata ɓatan wayarta, daga nan kuma suka cigaba da hirarsu ta ƙawaye, sai da labari ya nisa ne Aysha ta ce mata "Toh yaushe zaki zo don Allah?".
Zuzee ta ce "Ba rana", ɗan marairaicewa Aysha ta yi "Akwai labari fa", Zuzee na jin haka ta ce "Bari mu gani nan da jibi Insha Allahu zan shigo".
Jibi ne ranar da Aysha zata je kitso, saboda haka ta ce mata "Zan fita kitso a jibin".
Da yake ƴar tazara ce tsakanin gidansu Zuzee da kuma inda Aysha ke zuwa kitso, Sai Zuzee ta ce "Toh ki biyo ta gidanmu sai na raka ki, kin ga mun haɗu kuma kin yi zumunci"
Aysha ta ce "Haka ne, toh Insha Allahu zan biyo", da wannan ne suka yi sallama. Aysha na aje wayar ta ji zuciyarta sawai ba wata damuwa. Fitowa ta yi ta shiga kitchen domin girka abincin rana.
Khamis ya yi zaton zai dawo ya taras da ita tana fushi, saboda ba abin da ta tsana irin ya hana ta fita, saɓanin haka da ya gani ne ya ce mata "Su Sholy dai an chanja", ta ce "Wurin me?", ya ce "Na ɗauka zan taras kina fushi".
Ƴar harara ta yi mashi saboda ta fahimci inda ya dosa, ce mashi ta yi "Toh ya zanyi tunda ka hana, kuma jibi ai kamar gobe ne ko?", ya ce "Hakane". Jin daɗin haka ne ya sa shi sakar mata jiki suka sha hira. Ƙarfe taran dare na bugawa kuma ya baro mata ɗakin saboda ma'abocin kallon News ne.
Wayarsa da ya bari a kan stool ta ɗauka, "Kai Inna li Llahi wa Inna laihi raji'un!" ta furta a fili lokacin da ga hoton Maryam a lock screen wallpaper ɗin Khamis. Gabanta na cigaba da faɗuwa ta ce "Kai ni wannan jarababbiyar yarinya, Allah ka yi mani maganin ta in huta". Saboda daidai da jin sunan Maryam ɓata mata rai yake, bare kuma hotonta ko ta ganin ta a fili.
Shiga gallery ta yi da nufin chanja wani hoto, sai dai hotunan Maryam ɗin da suka cika kowace folder ne ya kusa tarwatsa mata zuciya.
Folder WhatsApp ta fara shiga, wasu irin picturse masu zafi ta gani na Maryam cike da folder, bata yi wata-wata ba ta yi delete ɗinsu all, cikin ranta kuma tana faɗin "Wato duk inda yake yana manne da ita".
Sai dai ba pictures ɗin WhatsApp ne suka fi taɓa mata zuciya ba saboda su da gani Maryam ɗin ce ta ɗauke su da kanta.
Vedion data gani a camera, wanda Maryam ɗin ke sanye da wata farar vest da tsawonta bai kai guiwa ba, Khamis kuma yana mata waƙar "Oya shake body" ita kuma tana ta kwasar rawa suna dariya. Sosai vedion ya sanya ma Aysha baƙincki a zuciya, kamar zata yi kuka ta ce "Ƴar iskar banza", tare da cigaba da kallon pictures ɗin dake folder, wanda majority da english gami da night wears ta yi su, wani wurin ma towel ne take ɗaure da shi, kuma da gani duk Khamis ne ya ɗauke ta.
