*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
https://m.facebook.com/Hadeeza-Isyaku-Novels-107323887468827/*Shafi na Huɗu*
Dangane da Aysha kuwa, wunin ranar kaɗai ya fara tabbatar mata da gadarar 'ƴa mace ba ta cika tasiri a wurin namiji idan yana da wata matar ba, domin tunda Khamis ya fito daga ɗakinta bata sake jin motsinsa ba bare har ya shigo inda take.
Saɓanin lokacin da take ita kaɗai, idan suka yi faɗa dole ta gan shi, sannan dole ya buƙaci wani abu a wurinta tunda bai da wata matar sai ita. Kuma a halayyar Khamis ma bai cika tsananta fushi ga iyalansa ba, a kullum ya kan horar da kansa jure duk wani zafi da mace zata sa mashi, domin mahaifinsa ya taɓa ce mashi, "Jajirtaccen namiji ne ke iya jure raɗaɗin dafin 'ƴa mace", shi ya sa ba kowane ɓacin rai ne yake maida hankali a kansa ba. Idan kuma har ta kama, toh ya kan yi nisan da bacci kawai ke maido shi gidan.Ya zaɓi haka ne domin ta wannan hanyar ce kaɗai yake hora Aysha.
Saboda a rayuwarta ba abin da ta tsana irin Khamis ya yi nisa da ita, hakan na sa ta damuwa sosai. Kamar yadda yanzu ta rasa inda zata sanya kanta saboda baƙincikan da suka mamaye mata zuciya. Gaba ɗaya ji take duniyar ta mata kaɗan, daidai da abinci wunin ranar bata ci shi ba.
Kuka kuwa cikin yin sa take, a ƙasan rantar kuma tana faɗin "Duka kwana biyu da yin aure amma har Abban Haneef ya maida ni saniyar ware", ko kusa bata yadda laifinta ne ya ja mata ba, sai ma take ganin ita ma aka raina ma wayau.
Zaune take akan abin Sallah ta na jan carbi, muryar yaranta ta ji sun nufo ɗakin da gudu, duba ta kai ga ƙofa tana jiran shigowar su, cikin ranta kuma tana tambayar kanta "Wa ya dawo da Haneefa?".
Bayan sun shigo ne ta samu amsar a bakin Haneef, inda ya ce "Mammy daga Masallaci muka wuce ɗauko Haneefa ni da Abba".
Ita kuma Haneefar ta ce "A kan hanya kuma Abba ya sai mana nama da Ice cream", miƙa mata ledar dake hannunta ta yi. Jiki a mace ta karɓa tare da tambayar ta "Ina Abban?", saboda shi kawai take son gani. Haneef ya fi kowa sanin inda Khamis yake, don haka ya ce "Ya tafi ɗakin Aunty ya kai mata nata".
Ido Aysha ta rumtse, cikin ranta tana jin idan akwai ranar baƙinciki to yau ce, domin tunda suka yi aure Khamis bai taɓa nisa da su ba alhalin yana cikin gidan, Ɗabi'arsa ce ma zama cikin iyalansa, hatta abinci idan yana nan tare zasu ci su duka a tray ɗaya.
Haneefa ce ta yi sanadin buɗewar idanunta da suka ƙanƙance saboda kuka, "Mammy bari na kira Abba ya zo mu sha Ice cream ɗin".
Kai Aysha ta girgiza tare da faɗin "Ko kin je ba zai zo ba Haneefa" kamar Haneefa zata yi kuka ta ce "Saboda me?","Saboda ya yi sabuwar Amarya". Sosai take son yin kuka, amma saboda bata son yaranta suga hawayenta sai ta haɗe.
Lallaɓa su ta shiga yi, daƙyal suka ci gasasshen naman da Ice cream ɗin, cikin ransu kuma suna jin ba daɗin rashin ganin Abbansu a tare da su.
Ita kuwa da ta ji yunwa na shirin taso mata da Ulcer sai ta haɗa Tea mai kauri ta sha, daga bisani kuma ta kwanta.
Washegari kuwa Maryam da ƙarfinta ta tashi, don haka bata tsaya jiran sai wani ya girka ya bata ba. Suna gama gaisuwar safiya ita da Khamis ta miƙe da nufin haɗa musu breakfast.
Khamis ya so ta ƙara warwarewa sannan ta shiga kitchen, amma ta ce "Zan iya".
Bata ɗauki dogon lokaci ba ta haɗa musu breakfast mai sauƙi.Tana gamawa suka yi wanka tare da shiryawa cikin shiga ta alfarma, doguwar riga ce ta sanya Maroon colour, wadda grey ɗin mayafinta ya samo asali daga zaren da aka ɗinka rigar. Shima Khamis grey ɗin yadi ne marar nauyi, sai kuma maroon ɗin hula, turaruka masu sanyaya zuciya suka feshe jikinsu da shi.