*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
@hadiza-isyaku2
facebook.com/Hadeeza-Isyaku-Novels-107323887468827*Shafi na Biyu*
Caa! Matan dake cike da falon suka yi ma Aysha, wanda mafi yawansu danginta ne da kuma na Khamis. Kalmar rashin kyautawa ce ta riƙa fitowa a bakin mafi yawansu, domin ba haka ake siyasar karɓar kishiya ba.
Aunty Rahama wadda ƙanwa ce ga Khamis ta ce "Aysha kina tare da wahala, tunda har ki ka ƙallafa ma ranki baƙin kishi".
Duk mutunta junan dake tsakanin Aysha da dangin Khamis bai hana ta murje ido tare da duban Aunty Rahama ta ce "Ji Aunty Rahama da wata magana, to wallahi ku kuka ga wahala ba ni ba, kuma amarya da danginta basu ga komai ba tunda har suka shigo gonata".
Shewa falon ya ɗauka, ɓangare ɗaya kuma duk aka bi ta da kallon mamaki, wasu na faɗin ta kyauta, wasu kuma na faɗin ta kwafsa.
Aunty Rahama kuwa ɗan taɓe baki ta yi tare da faɗin "Maida wuƙar ƙanwata, na san wutar kishi ce ke ruruwa azuciyarki, don haka dole mu yi maki uzuri kafin ki gane babban kuskuren da kika tafka"
Aunty Rahama na rufe baki wata daga cikin dangin Ayshar ta ɗora da "Yo Rahama kishi hauka ne, in banda sakarci da ɗaukar zugar ƙawaye me zai sa ta wannan katoɓarar?".
Faɗa sosai suka yi mata, suka nuna mata girman kuskuren da ta aikata, wanda ko shakka babu ya zubar mata da ƙima a idon Amarya da danginta. Sannan suka nuna mata kishi fa ba hauka bane, iyaka tsakanin ta da amarya duk wadda ta iya allonta ta wanke.
Duk surutun da suke yi Aysha bata ɗauki ko ɗaya ba, asali ma gani take suna faɗin haka ne don ba su aka yi ma kishiyar ba.
Miƙewa ta yi tare da duban Zuzee da duk ta sha jinin jikinta, saboda ta lura da kallon tsanar da dangin Khamis ke jifarta da shi. Bakomai kuma ya ja wannan kallo ba sai fahimtar da suka yi ita ce babbar ƙawar Aysha, kuma duk rashin mutuncin da Ayshar ke yi da sa hannunta a ciki.
"Zuzee ta shi mu je ciki" Idanun Aysha a kanta ta faɗi haka.
Amsa Zuzee ta bata da "Ki je zan shigo", saboda bata son su zarge ta, Aysha bata yi tunanin komai ba ta yi gaba, Zuzee na ganin ta shige ta ɗan riƙa sa baki ana tsigar Ayshar.
Aunty Rahama ma babbar ƙawarta mai suna Hajjo na zuwa ta bar falon. Ɗakin Amarya suka shiga, aikuwa suka taras ana ta zagin Aysha, kuma ganin su bai sa an fasa ba.
Rahama ta ji ba daɗi, sai dai tunda Ayshar ce ta ja ma kanta ba yadda ta iya.
Matsawa suka yi a gefen gadon da Amarya ke zaune, Aunty Rahama ta ce "Maryam ga ƙawata ku gaisa".
Cike da kunya Maryam ta ɗan yaye mayafin da ke kanta tare da gaishe da Hajjo.
Amsawa ta yi sannan ta yi musu Allah sa Alkhairi. Bayan sun fito Hajjo ta tambayi Aunty Rahama "Ni kam wacece mutanen can ke cewa ta rako mata?".
Aunty Rahama ta ce "Waa ce fa idan ba Aysha ba, ai ta gama bamu kunya". Abin da Ayshar ta yi ta labarta ma Hajjo.
Ran Hajjo a ɓace ta ce "Kanta ta wulaƙanta, amana kuma ko ta karɓa, ko kada ta karɓa duk ɗaya, tunda aikin gama ya gama", ɗakin Aysha suka nufa, lokaci ɗaya kuma suna tattauna maganar cikin ɓacin rai.
A ɗakin Amarya kuwa yadda zata zauna da Aysha suka shiga kitsa mata, don sun fahimci mugun abu ne ke cike da ran Ayshar, wanda kuma idan ba tsaye suka tashi ba, to ƴarsu zata sha wahala.
Da yake Amaryar ba kanwar lasa bace ta ce "Ai wallahi ta gama yawo tunda har na auri mijinta, baƙin kishi kuma mu zuba ni da ita". Daga yara har tsofaffin dake wurin ba wanda ya kwaɓi Maryam, sai ma ƙara zuga ta da suke akan ta yi ƙoƙarin zama tauraruwa a wurin Khamis, basu suka fara shirin tafiya ba sai da suka ga zamanta ya daidaita akan dokin huɗubar da suka ɗaura ta akai.
