*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
@hadiza-isyaku2
*Shafi na Tara*
Zuzee na jin Aysha ta ce Khamis ya kusa dawowa ta yi saurin faɗin "Eh a bari sai jibi ma, ko wani lokacin kafin ta dawo", tana rufe baki ta shiga haramar tafiya a ƙasan ranta saboda bata so Khamis ya iske ta a gidan.
Aysha da ta ƙagu ta ga me ke cikin ɗakin Maryam ta ce "Goben dai don Allah", don rabon ta da ɗakin tun ranar walima da ta raka Khamis.Ɗan jum kaɗan Zuzee ta yi, daga bisani ta ce "Gaskiya gobe ba zai yiwu ba, ni tsoro nake kada muna cikin buɗe ɗakin mijinki ya dawo mu shiga uku".
Sai da Aysha ta nazarto lokuttan dawowar Khamis sannan ta ce "Shi fa idan ya fita da safe, bai ƙara dawowa sai yamma, don haka kada ki ji komai".
Zuzee ta ce "Toh bari mu gani", ƴar hira ce suka taɓa, a ciki suka yanke abar buɗe ɗakin sai idan Khamis ya yi tafiya, saboda Zuzee hankalinta bai kwanta ba, tsoronta kada suna ciki ya dawo, tunda gidansa ne, babu kuma mai iya yi mashi shamaki da dawowa a duk lokacin da ya ga dama.
Shirin tafiya Zuzze ta fara. Aysha da ke jin ko kwana za su yi suna hira ba zata gaji ba, saboda wurin da ya fi yi mata ƙaiƙaiyi ne Zuzee ke taya ta sosawa "Kai Zuzee ba dai yanzu ba".
Ɗan yamutse fuska Zuzee ta yi sannan ta ce "Ke wallahi tafiya zan yi, Aysha ta ce "Duka fa ƙarfe biyar", idanunta a kan fuskar wayarta ta ƙarashe maganar.
"Ni fa mijinki ne bana so ya taras da ni gidannan", Zuzee ta faɗa tare da yafa mayafinta da ke hannunta.
Abin da Zuzee ke gudu ne ya afku, domin ƙarar buɗewar gate suka ji, wanda ko shakka babu Khamis ne ya dawo.
Damuwa bayyane a fuskata ta dubi Aysha "Kin ga abin da nake gudu ya afku".
Sosai Aysha ta yi mamakin yadda Zuzee take kyarma don Khamis ya shigo.
"Toh wai don Allah sau nawa yana iske ki a gidan nan, sai yanzu zaki tsiro da bakya son ya iske ki, haba don Allah", karɓar mayafin Zuzee ta yi ta aje tare da jawo mata hannu alamar ta zauna.Zuzee na jin maganar Khamis shi da yara ta zauna tare da ɗan kama kanta.
Khamis kuwa tuni Haneefa ta faɗa mashi wai Aunty Zuzu ta zo. Sosai "Zuzu" da Haneefa ke cewa ya bashi dariya, don bata iya faɗin Zuzee ba.
Da sauran dariya a bakinsa ya shigo falon. Zuzee na ganinsa ta ƙara kame kanta, tsoronta kada Aysha ta yi wani abu, wanda ko shakka babu za'a ce ita ce, tunda tare ake ganin su.
Tun kafin Khamis ya zauna ya dubi Zuzee ya ce "Aaa! Malama Zuhura ce a gidanmu", zama ya yi a hannun kujera, lokaci ɗaya kuma hannayensa na cikin na Haneefa tana jujjuya shi.
Ƴar dariya Zuzee ta yi tare da ɗan russuna kai "Wallahi kuwa ni ce, Ina wun?".
Ya ce "Lafiya lau, kwana biyu", Zuzee ta ce "Alhamdulillahi".
Kusan a tare suka miƙe shi da Aysha da fuskarta ke ta annuri, sannu da zuwa ta yi mashi, ya ce "Yauwa madam", sannan ya nufi ɗakinsa, ba tare da damuwa da lamarin Zuzee ba kamar yadda take tunani.
Ɗan duban Zuzee Aysha ta yi "Ina zuwa", sannan ta bi bayan Khamis.
Wayarsa da key ɗin motarsa ya aje kan gado. Duban Aysha da ta shigo yanzu ya yi, sai ya ga wani irin nishaɗi kwance a fuskarta.
"Madam irin wannan nishaɗi haka?" ya faɗa lokacin da yake cire agogon hannunsa.
Ƴar guntuwar dariya ta yi ta ce "Kai Abban Haneef ina nishaɗin anan", dariya ya yi sannan ya ce "Gashi nan kwance a fuskarki".