KISHIYAR KATSINA 6

2 1 0
                                    

*KISHIYAR KATSINA*
  *(Kissa ko Asiri)*

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
@hadiza-isyaku2

*Wannan shafin naki ne ~Nana Aicha my Jikalle, ki yi yadda kike so da shi*

*Godiya da fatan Alkhairi a gareki My Emily, Allah ya bar ƙauna Amiin*

*Shafi na Shida*

Dogon nazari Khamis ya yi, sai ya fahimci ƙyale Aysha da ya ɗaukar ma ransa zai yi idan har ta ƙi haƙura ba mafita bane, saboda zaman ba zai ɗore ba alhali suna jin haushin juna, dole ne wani abu marar daɗi ya biyo baya wanda kuma bai fatan faruwar sa.

Sosai jikinsa ya yi sanyi, har ta kai ga Maryam dake maida kaya a wardrobe ta lura. Ɗabi'arsa ce taya ta yin duk wani aiki da ta jawo a ɗakin, amma sai gashi yau bai taya ta ba, bugu da ƙari kuma ya yi shiru ba tare da yi mata magana ba.

Zuciyarta cike da damuwar sauyin yanayinsa ta rufe wardrobe ɗin. Ɗan dafa shi ta yi lokacin da ta zauna gefensa a kan sofa ta ce "Yau kamar baka cikin walwala, ko wani abu ya faru?", "Me kika gani" ya tambaye ta bayan ya sakar mata gajeren murmushi.

Ɗan shagwaɓewa ta yi gami da kwantowa a jikinsa ta ce "Na ga yau baka taya ni maida kaya ba, kuma ƴar hirar nan mai daɗi da muke duk babu ita".
Kasa faɗa mata damuwarsa ya yi, sai dai yayi mata hannunka mai sanda ta hanyar faɗin "Kin san yau da gobe sai Allah", ta ce "Haka ne", ya ce "Toh ina da ƴar damuwa, ina kuma son ki taya ni da addu'a".

Cike da damuwa ta ce "Insha Allahu zan taya ka mijina, Allah ya yi maka maganin abin da ke damun ka".

"Amiin" ya faɗa a taƙaice, saboda zuciya na ta ƙara tsoratar da shi a kan lamarin Aysha.

Ko kaɗan Maryam bata matsa mashi da surutu ba, sai dai ta lahe a gefensa, saboda ta san hakan na mashi daɗi.

Ƙarar wayarsa ce ta katse musu shirun da ya ratsa su, idanunsa da ke rufe ya buɗe tare da faɗin "Wayata Mairo", da hanzari ta ɗauko mashi wayar akan gado.

"Waye ya kira?" ya tambaye ta, idanunta a kan fuskar wayar ta ce "A Umar ne", lokaci ɗaya kuma ta ɗaga kiran tare da kanga mashi wayar a kunne.

Hannunta da wayar ya haɗe ya riƙe, sannan kuma ya zaunar da ita a jikinsa. 

"Kana sha'aninka ango, wato tunda ka ƙara aure ko wayarmu baka son ɗagawa ko",  daga can cikin wayar A Umar ya faɗi haka bayan sun yi ma juna sallama.
Dariya Khamis ya yi "Sorry Abokina, wallahi na ga kiranka, na so na sake kira kuma sai na shafa'a".

Daga cikin wayar ya ce "Okay, to ina Amarya?".

Idanun Khamis a cikin na Maryam ya ce "Ga ta a tare da ni tana saurarar ka".

A Umar ya ce "Kai da kyau, toh ta shirya mana girki mai daɗi, don yau a gidanku zamu wuni".

A wannan karon Maryam ce ta yi magana, cewa ta yi "Lallai muna da manyan baƙi, toh Allah ya kawo ku lafiya".

A Umar ya ce "Amiin Amarya". Cigaba da magana suka yi da Khamis, daga bisani suka yi Sallama.

A Umar shi ne babban abokin Khamis, wanda suka haɗu tun a primary school har zuwa University, sai dai suna yin Degree suka rabu, saboda Khamis ya fi maida hankali ga sana'ar saida motocin da suka gada a wurin mahaifinsu. Shi kuma A Umar ya cigaba da karatu ne inda a yanzu yake koyarwa a Jami'ar Maryam Abacha da ke Niger, a can kuma ya haɗu da matar da yake aure mai suna Nana Aicha.

Cefane mai rai da lafiya Khamis ya fita kasuwa ya siyo. Cikin ransa kuma yana gode ma Allah da ya sa girkin Maryam ne saboda bata da gandar aiki.

A kitchen ya same ta har ta yi boiling shinkafa tana tacewa "Da kyau Mairo, rashin son jikinki na ta'azzara soyayyarki a zuciyata".

KISHIYAR KATSINA Место, где живут истории. Откройте их для себя