*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
@hadiza-isyaku2*Wannan shafin sadaukarwa ne ga masoyana guda biyu, Zulaihat (Emilia~SAMHA), da kuma Hauwa'u Salisu (Haupha), ina son ku saboda Allah, Allah ya bar ƙaunar da ke tsakaninmu Amiin*
*KISHIYAR KATSINA FANS ina jin daɗin yadda kuke sharhi mai ma'ana ga littafinnan, ina yi maku fatan Alkhairi dukkanku*
*Shafi na Bakwai*
A tunani irin na Maryam namiji ba zai iya son mace biyu ko ma fin haka a lokaci ɗaya ba, mafarin ta ke gani kamar dama can Khamis na son Aysha, ita kuma romon baka ne yake mata kawai don ya mori jikinta.
Tsaye take a jikin window tana ƙare ma farfajiyar gidan kallo, cikin ranta kuma tana tuna yadda a ɗazu Khamis ya shigo wurinta a gurguje da nufin yi mata sallama, wani irin haushi ne ya ƙara ƙule ta, inda kuma zuciya ta ce mata "Mutumin nan fa ya dena sonki, don haka sai kin tashi tsaye".
Ko zuciya bata faɗa mata ta tashi tsaye ba dama tana da niyya, sai dai ta ina zata fara?, Saboda duk wasu dubarun da take da su ta fiddo su waje, amma hakan bai hana Khamis nuna farincikinsa ga ƙoƙarin Aysha ba.
Waya ta ɗauka ta shiga WhatsApp domin duba wasu sirrikan mallar miji da ta ga ana turowa a group ɗinsu na Matan Aure Zallah. Saƙon causin Sister ɗinta ne ta ga shigo, da hanzari ta buɗe ta ga ta rubuta "Gamu a hanyar gidanki, na kira ki ban samu ba".
Cike da jindaɗi ta yi mata reply da "Wayyo murna, Allah ya kawo ku lafiya Yaya Hauwa".
Fasa shiga group ɗin ta yi tare da kashe data. Fitowa ta yi ta zauna kan wani benci a parking space, lokaci ɗaya kuma idanunta na kan gate ɗin gidan tana jiran shigowar su.
Bata fi minti goma da zama ba kuwa ta ji tsayawar Napep a waje, da hanzari ta miƙe, kafin ta kai bakin gate ɗin har sun shigo.
Ya Salam, kada ka ga murna a wurin Maryam saboda hada Yayarta mai suna Zulaihat, wadda kuma uwa ɗaya uba ɗaya suke da ita.
Wata irin maƙalƙalewa ta yi musu tare da faɗin "Kai Aunty Zulaihat, irin wannan ba zata haka?".
Yadda take ta murna ne ya ba su dariya, Hauwa'u, wadda suke ma laƙabi da Yaya Haupha ta ce, " Sai da na ce a faɗa maki ta zo ta ce a'a", saboda ita Hsupha a nan garin suke, kuma Mamanta Twin Sister ɗin Mamansu Maryam ce.
Aunty Zulaihat ta ce "Na san halinta fa, muddin ta san da zuwan mu toh ko bacci ba zata yi ba", Maryam ta san hakane, don haka ta dubi kowannen su tana dariya.
Da murnar ganin juna suka ƙarasa cikin falo, inda suka zauna a nan suka gaisa, bayan gaisuwar kuma suka dasa hira suna ta kwasar dariya.
Rashin jin motsin Aysha ne ya sa Haupha tambayar Maryam, "Wai ina kishiyarki ne?, Mun kusa rabin awa a nan amma bata fito ba".
Aunty Zulaihat da ta tuna wulaƙancin da Aysha ta yi musu ranar walima ta ce "Ƴar banzar ba", Haupha na dariya ta ce "Da wofi ma wallahi, ai ban taɓa ganin jaka kamar wannan ba", duk murya ƙasa-ƙasa suke maganar saboda Maryam ta musu alama da Aysha na nan.
Tashi Maryam ta yi ta ce "Bari na yi mata magana".
Kwance ta samu Aysha tana ta shirgar bacci, knocking ƙofar ɗakin ta yi da ɗan ƙarfi.
Cike da magagin bacci Aysha ta tashi tare da tambayar ta "Ya aka yi?", kamar Maryam zata shaƙaro ta ta ce "Yayyena ne suka zo za ku gaisa".
Kamar Aysha ba zata yi magana ba, daga bisani ta ce "Toh gani nan".
