KISHIYAR KATSINA 5

7 2 2
                                    

*KISHIYAR KATSINA*
  *(Kissa ko Asiri)*

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*

https://m.facebook.com/Hadeeza-Isyaku-Novels-107323887468827/
*Shafi na Biyar*  

Ruƙo hannunta Khamis ya yi a lokacin da take yunƙurin sauka daga kan gadon, cikin dagewa akan son fahimtar da ita ya ce "Aysha don Allah ki saurare ni, wallahi ko kusa ban faɗa maki haka don in wulaƙanta ki ba, kuma..."

"Na ce ka sake mani hannu", ta faɗa tare da fizge hannunta.

Direwa ta yi daga kan gadon sannan ta ɗora da "Kuma wace magana ce zan ji daga bakinka?, bayan ka tabbatar mani da butulcinku na ƴaƴa maza. A baya har cewa kake idan akwai matan aljanna duniya to ina ɗaya daga cikinsu, amma sai gashi ƙarin aure ya sa ka ƙaryata kanka,
don haka ka riƙe kalamanka.
Kuma itama ƴar gold ɗin ta tanadi mai hure mata ƙasar da zaka watsa mata a idanu idan ka gama yayinta"  Kuka mai tsuma zuciya ne ya ci ƙarfinta, ba don ta so ba ta dakata da maganar duk da akwai sauran raddi ma zafi a bakinta.

Sosai kukan da take ya ɗaga hankalin Khamis. Manufar kalamanta ce ta cigaba da bayyana zuciyarshi, wato tana nufin ya gama yayin ta shi ya sa ya faɗa mata haka. 

Ya buɗe baki zai yi magana ne ta juya, rufe bakin ya yi tare da raka ta da idanu har ta fice gami da banko ƙofar da ƙarfi.

Dafe kansa ya yi haɗe da lumshe idanu,  "Yanzu fassarar da Aysha zata yi mani kenan? Yanzu ni Khamis ne na gama yayin ta?" cikin ransa yake wannan maganar, lokaci ɗaya kuma yana jin wani irin ƙunci na taso mashi a ƙahon zuciya.
"Kai ya zama wajibi na faɗa mata ba haka bane tun kafin ta ɓata mani suna a wurin danginta", a gaggauce ya sauko daga kan gadon ya nufi ɗakinta. Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi, sai dai bai samu zarafin shiga ba saboda key ɗin da ta sa bayan ta shiga. 

Sautin kukanta da yake jiyowa ne ya ƙara ƙuntata mashi zuciya, kamar shi ma zai yi kukan ya ce "Kai, Inna li Llahi wa inna laihi raji'una, Allah kana gani". Saboda shi bai ga wani abin da rayuka zasu ɓaci a nan ba.

Knocking ƙofar ya shiga yi a hankali saboda dare ne, kuma bai son Maryam ta jiyo motsinsa, kasantuwar sauti na sauƙin karaɗe wurare a irin wannan lokacin.

Ita kuwa tana jin shi, sai dai bai da ƴancin da zata buɗe mashi ƙofa don a ganinta ya gama wulaƙanta ta.

Ƙin buɗewar ne ya fara fusata shi, a hasale ya ce "Aysha kina ji na amma ba zaki buɗe ba ko, to ba damuwa, ni dai Allah ya san zuciyata, ko kaɗan ban yi nufin wulaƙanta ki a maganata ba, amma tunda haka kika sa a ranki matsalarki ce",

Jiki ba ƙwari ya dawo ɗakinsa, jagwab ya zauna a gefen gado tare da furzas da iska mai zafi. Shi ba fushin ne damuwarshi ba, muguwar fassarar da suɓul da bakarshi ta ja mashi ita ce damuwa, tabbas duk wanda ya ji asalin maganar zai ce ya wulaƙanta ta ne saboda ya yi sabon aure.

Tsaki ya ja tare da faɗin "Matsalar duk wanda zai ce haka ne" don ko kusa bai tsoron zargin mai zargi madamar a kan gaskiya yake.

Duk irin zafin da yake ji a ransa, amma bai bari damuwa ta samu mazauni azuciyarsa ba bare har ta hana shi bacci. Don haka ne ma ya kashe fitilar ɗakin sannan ya dawo ya kwanta. Sai dai bai san Maryam ta fara saba mashi da rashin bacci shi kaɗai ba sai da ya ji ba kowa a gefensa, Idanunsa a lumshe ya cigaba da laluben gefe. 
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke saboda koda hannunsa zai ƙara tsayi ba zai ji kowa ba. Ƙumshewa ya yi cikin bargo, ƙasan ransa kuma yana hasaso Maryam kwance a gefensa. Wanda yake ji a jikinsa itama shi take tunani a halin yanzu, don ta faɗa mashi ba zata iya bacci ba idan ba a gefenshi ba.

Tabbas tunanisa a kan Maryam gaskiya ne, domin tunda ya fito daga ɗakin ta nemi walwala ta rasa. Ba komai ya tafi mata da wannan walwala ba sai zazzafan kishin da ya turnuƙe mata zuciya, saboda ko shakka babu irin kulawar da yake bata ce zai ba Aysha, "Illar auren mai mata kenan, komai na shi sai ya raba biyu ya bata rabi", cike da takaici Maryam ta faɗi haka sannan ta kashe fitilar ɗakin.

KISHIYAR KATSINA Kde žijí příběhy. Začni objevovat