*KISHIYAR KATSINA*
*(Kissa ko Asiri)**HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*Hadiza Isyaku* *_(Mai Awara)_*
https://m.facebook.com/Hadeeza-Isyaku-Novels-107323887468827/
*Na faɗa, kuma zan sake faɗa _wannan littafi ƙirƙira ne, hanyar da kuma mai karatu zai ji daɗinsa ita ce ya kalle shi da sunan Kishiyar garinsu, misali KISHIYAR KADUNA, kuma ban yi don cin zarafin kowa ba_*
*Sannan duk abin da na saka, kamar littafin da Haupha ta ba Maryam, da kazar Nonon rakumi duk don mata su nema kuma su yi ne, na san an sansu da daɗewa, amma kamar an manta da su, saboda haka ne na tuna mana*🤗
*Shafi na Goma*
Lokaci mai ɗan tsayi Khamis da Maryam suka ɗauka ba tare da rabuwa daga jikin juna ba. Faɗin irin farincikin da kowannen su ya samu kansa a ciki ma ɓarnar baki ne, musamman Maryam da idan kewar sa ta motsa mata sai dai ta rungumi pillow, shi kuwa yana da wata matar da yake ɗebe kewa da ita.
A hankali Khamis ya buɗe idanunsa da suka fara ƙanƙancewa saboda shauƙin da raɓar jikinta ya saka shi, ɗan janye jikinsa ya yi tare da dafa kafaɗunta duk a lokaci guda.
Hakan ne ya yi sanadiyyar buɗewar fararen idanun Maryam gami da sauke su a kan fuskarsa dake ɗauke da mayalwaciyar fara'a. Sosai suka ga ƙaruwar kyawun junansu fiye da can baya.Kallon fuskar Maryam kaɗai bai wadatar da Khamis ba, hannunsa ya ɗauke daga kafaɗunta ya maida su a saman kanta tare da yaye mayafin da ta lulluɓa da shiya ajiye shi a kan kujerar da ke gefensu.
Take cikakkiyar surarta ta bayya na a cikin riga da skirt na red ɗin sweez less "Masha Allah" ya furta a fil, cikin ransa kuma yana jin ƙaruwar shauƙin son ta ya na ɗibar shi.
Itama irin abin da yake ji a zuciyarshi ne take ji a tata zuciyar lokacin da ganinta ya haɗu da nashi.
A hankali ta lumshe idanu tare da buɗe su lokacin da ya da ya tallabi kumatunta ya ce "Haka kika ƙara kyau?".
Murmushi mai sauti ta yi tare da faɗin "Kai ma ai ka ƙara kyau", ɗan rau ya yi da idanu tare da faɗin "Da gaske na ƙara kyau?", ta ce "Allah kuwa".Murmushi jin daɗi ya yi sannan ya ce "Ba zan maki musu ba, amma na san soyayyarki ce ta sa na ƙara kyau Maryo.
Ni kaina na san tunaninki shi ne lafiyayyen abinci ga ruhina, shi ya sa na ɗauke shi abin yi a dukkan dare da rana. Don haka ina ƙara tabbatar maki da ina son ki, son da ake kira so", hannayensa a kan kafaɗarta ya ƙarashe maganar, lokaci ɗaya kuma ya sumbaci ɗan ƙaramin bakinta da farinciki ya hana ta rufe shi.Maryam ta rasa sirrin da ke cikin lafuzzan Khamis, saboda duk lokacin da ya furta mata su sai ta ji kamar ta fi sauran mata sa'a a rayuwa, cikin murya mai jan hankalin mai sauraro ta ce "Na fahimci kasancewa da kai shi ne mafi farincikin lokaci a wurina, don haka nima ina sonka mijina".
Sake maida ta ya yi a jikinsa, kalmomi masu nuna soyayyarta a gare shi ya cigaba da raɗa mata a kunne.
Sun ɗan ɗauki lokaci a haka sannan suka rabu da juna. A ƙasan carpet suka zauna, abincin da Maryam ta kawo mashi ne ta yi serving ɗinshi, sinasir ce da miya, ɓangare ɗaya kuma ga pepper chicken nan sai tashin ƙamshi yake.
Sosai ƙamshin girkin ya tafi da Khamis, ce mata ya yi "Hala ke kika yi girkinnan?", kai ta girgiza "A'a Hajiyarmu ce, ta ce ba wanda zai ma surukinta girki sai ita".
Khamis na dariyar samun matsayi a wurin Hajiyarmu ya ce "Wow! Sai ni ɗan gatan Hajiyarmu", Maryam na dariya itama ta ce "Ai tana ji da kai".
Ya ji daɗin samun wannan matsayi a wurin Hajiyarmu, ya san ba ita kaɗai ba kowa na gidan ma yana son shi, duba da irin farincikin da ahalin gidan suka yi lokacin da ya zo.