BABI NA TARA

47 4 4
                                    

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, babu laifi tana cikin kwanciyar hankali fiye da yadda suka tsammata don ta murmure ta cicciko alamun tana samun kulawar ci da sha da kuma nutsuwar zuciya, idan har tana da wata matsala a zamanta da Usman to ta rashin nemanta da baya yi ne shima kuma sai lokaci zuwa lokaci abun yake fado mata a rai tana tunanin dalilin da yasa har zamansu ya doshi shekara bai taba nuna yana da wata buƙata a wajenta ba, idan ta tuna makarantar da ya maida ta kuma sai tace watakila baya son ɗaura mata nauyi biyu a kanta ne ga hidimar karatu ga kuma ta aure don haka sai ya zamanto damuwarta ƙalilan ce akan hakan.

Yau a makare ta shigo gidan daga makaranta saboda tsayar dasu da Malaman su suka yi anyi musu bayani akan jarrabawar fita da zasu zana a bana kasancewar su 'yan aji shida, inda Allah ya taimaketa ma tayi sallah kafin ta baro makarantar don haka tana zuwa ta fara ƙoƙarin ɗora girki.

Kayan makarantar da ta cire ta ɗauko ta wanke bayan ta hada sanwar, tana gamawa ta fada banɗaki tayi wanka don har an fara kiran sallar la'asar a masallacin kusa dasu. A gaggauce tayi wankan ta shirya cikin atampa ɗinkin doguwar rigar da tabi ƙirar jikinta ta kwanta gwanin sha'awa.

Tana idar da sallah ta ɗebo abinci ta dawo tsakar parlour ta zauna tana ci, wata irin yunwa take ji don ko karyawa bata samu tayi ba kafin ta tafi makaranta saboda tashi da tayi a makare.

Ta kusa gama cin abincin lokacin da taji ana buga ƙofar gidan.

Ajiye farantin tayi ta tashi taje taga waye, tasan dai ba Usman ba ne don bai cika shigowa ba sai bayan magriba.

Aunty Hanne ta gani a tsaye, matsawa tayi ta shigo soron kafin ta daka tsalle ta rungume ta tana ihun murna.

Itama Aunty Hannen dariya take yi don ta kwana biyu bata ga Hasinar ba, sai taga duk ta canja mata ta ƙara cikowa fiye da kwanan baya da ta ganta.

Sosai Hasina ke murna don ba kasafai ta cika yin baqi ba dama 'yan gidan su ba zuwa suke yi ba itan ma sau daya taje ta yini tun bayan bikin A'ilo.

Kitchen ta shiga ta haɗa lemon tiara a cikin jug ta haɗa da ruwa ta dora akan tray ta kaiwa Auntyn, bata zauna ba ta koma kitchen din ta haɗo abinci ta kawo.

Sai da ta ajiye sannan ta zauna tana cewa "Aunty ina yini, yasu baby? Me yasa baki zo mini dasu ba Aunty".

Dariya Auntyn tayi tace "lafiya lau Hasina, su baby na islamiyya basu san zan zo ba da cewa za suyi sai sun biyoni".

"Ai kam dai da anzo mini dasu don na daɗe ban gansu ba".

Ruwan kawai Aunty ta sha tace ba zata ci abincin ba don bata tare da yunwa.

"Daga gidanku nake nace bari dai yau nazo na ganki tunda ke baki iya zuwa ki gaida mutane ba, koda yake naga ma kin fara nauyi, kice da sai dai naji haihuwa banda Allah ya kawoni na ganewa idona".

Kallonta tayi galala kafin tace "Aunty waye zai haihu? Wallahi bani da labari".

"Hmm" kawai Aunty Hanne tace "ashe dai har yanzu kina nan da wautarki sai ma abinda ya ƙaru, waye kuwa zai haihu idan ba ke ba, ga nan duk wasu alamu na ciki sun bayyana a jikinki".

Dariya ta saka kafin tace "kai Aunty Hanne don Allah, cikin lafiya ana zaune ƙalau".

Sosai Auntyn ta kalleta tace "ban gane cikin lafiya ana zaune ƙalau ba, wai nufin ki kice mini babu cikin kome".

Tace "wallahi bani da komai Aunty, ni nayi zaton ma wata ce a dangi ta kusa haihuwa har ina murna ashe wai nan da ni kike, tabdijam shi da yana parlour ina daki ta ina za'a... Au" tayi maza ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta bibbiyu, shaf ta mance da Aunty Hanne suke magana ta saki baki zata yi ɓaranɓarama.

Kallonta Aunty Hanne tayi kafin tayi magana hankali a tashe tace "bangane wa kina ɗaki yana parlour ba, kina nufin tunda aka yi auren haka kuke zaune ko kuwa dai yanzu ne abun ya fara, ko kuma saɓani kuka samu shine ya ƙaurace miki ya dawo kwana a parlour?"

Jikinta ne yayi sanyi ganin yadda hankalin Auntyn ya tashi daga 'yar wannan maganar "Allah yasa dai bani na bata mata rai ba" tace a cikin zuciyarta.

Tsawa ta daka mata tace "ya ina yi miki magana zaki tsaya kina kallona ba zaki bani amsa ba".

Cikin rawar murya tace "don Allah Aunty kiyi haƙuri wallahi suɓutar baki nayi, ban yi niyyar faɗar maganar nan kowa yaji ba Allah tunda duk kun faɗa mini babu kyau fallasa sirrin cikin aure, Allah yayi hani da hakan".

Ɗan sassauta yanayin fuskarta tayi lura da tayi sam Hasina bata fahimci dalilin tashin hankalinta ba hasalima wani waje daban tunaninta ya kaita.

Cikin murya irinta mai lallashi tace "kinga ki kwantar da hankalin ki ba laifi kika yi ba, kawai dai ina so ne nasan me ke faruwa don mu san ta inda zamu ɓullowa al'amarin, tun yaushe ne kuka raba shimfiɗar ko tun farko dama  haka kuke zaune?"

A hankali ta ɗaga kanta alamun 'eh'.

Shiru Aunty Hanne tayi tana nazarin amsar da Hasinar ta bata kafin tace "amma shine kika yi shiru da bakinki kika kasa faɗawa kowa, idan ma ba zaki iya faɗawa Innarki ba ni zaman me nake yi da ba zaki faɗa mini ba, ai ba irin wannan maganar ake boyewa ba Hasina tunda dai ba kawoki muka yi don mun rasa abincin da zamu baki ba bare ace ya ɗauke miki ci da sha, idan don wannan ne da bamu kawar dake daga gabanmu ba tunda dai Alhamdulillah bakin gwargwado muna da abin ɗaukar ɗawainiyar ki, yanzu dai dole na koma gidanku na samu Yaya Habiba muyi magana idan ma ita ba zata iya faɗawa Mallam din ba ni zan faɗa mishi a kira yaron nan a tuntube shi abinda ke akwai idan ma ba yada lafiya ne gara tun wuri mu sani amma sam zaman ku a haka ba zai yiwu ba".

Bayan tafiyarta Hasina ta daɗe zaune anan inda Aunty Hanne ta barta tana tunanin me zai sa Auntyn tayi tunanin Usman bashi da lafiya alhalin babu alamar dake nuni da hakan a tattare dashi tunda dai kullum sai ya fita wajen harkar kasuwancin shi baya dawowa sai anyi sallar magriba, to mara lafiya ta ina zai fara fita nema bare har yayi irin wannan daɗewar da yake yi a waje.

Har aka yi kiran sallar magriba tana wurin a zaune ta kasa taɓukawa kanta komai, kiran sallar ne ma yasa ta tashi ta tattare kwanukan abincin da ta kawowa Aunty Hanne da ko buɗewa bata yi ta gani ba tace ta koshi, kitchen ta mayar da kayan kafin ta wuce banɗaki ta ɗauro alwala ta fito ta tada sallar anan tsakar gidan kasancewar babu wutar nepa.

Bata tashi daga wurin sallar ba sai ma carni da ta dauka tana istigfari dama kuma sabonta ne yin hakan, zai yi wuya kwarai ta tashi daga abun sallah daga idarwarta ba tare da ta zauna tayi azkar ba.

Tana zaune a wurin Usman ya shigo cikin gidan da sallama hannun shi dauke da baƙar leda, tashi tayi tana yi mishi sannu da dawowa ta karbi ledar da ya shigo da ita ta kai kitchen, kayan miya ne ya riqo mata dama kuma sabon shi ne taho mata da duk abinda zata buƙata daga kasuwa.

Sai da ta juye kayan miyar a cikin roba sannan ta ɗauki tray ɗin kayan abincin shi ta fitar mishi dashi, ganin shi tayi a zaune akan sallayar da ta tashi don haka tace "yau anan zaka ci abincin kenan ganin baka shiga ɗakin ba".

"Gara kawai na zauna anan ɗin tunda cikin babu wuta kuma naga kamar wurin akwai iska".

A gabanshi ta ajiye tray ɗin ta koma kitchen ta ɗauko kujera ta zauna, yana cin abincin yana janta da hira jifa-jifa ita dai jin shi kawai take yi tana kuma kallon shi a ƙoƙarin ta na son gano ko akwai wani abu dake damun shi daya kasa sanar mata.

Har lokacin da suka tafi suka kwanta Hasina bata cikin nutsuwar ta sosai saboda zullumin abinda kaje yazo idan maganar da Aunty Hanne tace zata kai gida ta fasu, ita tasan babu me ƙwatar ta a hannun Baba sai Allah, tabbas gamon su ba zai taɓa yi mata daɗi ba.

UMMASGHAR.

QADDARAR MUTUM Where stories live. Discover now