BABI NA TAKWAS

647 53 8
                                    

Babu laifi zamansu kadaram kadaham wai karatun dan kama don bata nemi komai ta rasa ba, bakin gwargwardo yana kokarin ganin ya sauke hakkokinshi dake kanta.

Hakkin aure ne dai har yau ya gagara saukewa hakan kuma bai taba damunta ba sai ma dadi da take ji don ita tsoron faruwar hakan ma take ji, nutsuwa da kwanciyar hankalin da ta samu yasa ta murmure tayi 'yar kiba hasken fatarta ya qaru ga wani irin girma da ta qara.

Basu rufa watanni hudu da aure ba ya mayar da ita makaranta inda ta cigaba a aji biyar wato ss2 dama kuma anan abokan karatunta suke wato dai zata cigaba tare da sa'o'inta abinda yayi matukar dad'ad'a ranta ganin kawayenta basu wuce ta ba.

Wanke-wanke take yi tare da rera Karatun Al-Qur'ani mai girma cikin qira'arta mai dad'i da saka nutsuwa ga mai saurare, Suratur Rum take karantawa.

Har ta kammala tasa tsintsiya da ruwa ta share wurin bayan ta kawar da kayan wanke-wanken nata. Girki ta d'ora sannan ta dawo tsakar gidan ta zauna inda ta shimfid'a tabarma ta baje littattafan makarantar ta tana yin aikin da aka basu a makaranta wato assignment.


Sallamar su Bello ce shi da abokin shi ta sata d'agowa daga aikin da take yi ta amsa musu tare da basu izinin shigowa.

Tattare littattafan tayi a gefe ta basu wajen zama ta koma kan kujerar tsugunno ta zauna. Bayan sun gama gaisawa ne suke fada mata cewar Inna ce dama ta turosu su fad'a mata gobe ne za'a amshi kayan lefen A'ilo.


"Allah ya kaimu goben" ta amsa da murnarta. "Amma na A'ilo kawai banda Hadiza? Ai nayi zaton tare za'a had'a auren nasu ganin samarin nasu tare suke zuwa".

"Ban san me ya faru ba aka fasa na Hadiza duk da cewa da zancen na su biyun ake yi sai da magana tayi karfi ne kawai muka ji na A'ilo kawai za'a yi, ban san dalilin fasa na Hadiza ba kin san kuma Inna ba fada mana zata yi ba ni kuma bazan je ina tambayarsu Idris dalilin fasuwar auren ba kin san halinsu yanzun nan sai su juya magana suce da wata manufa na tambaya shi yasa naja bakina nayi shiru".

"Hakane kam Bello, gara kasan irin maganar da zata ke hadaku dasu duk da suke 'yan uwanmu amma taka tsantsan ya zama dole duba da yadda yanayin zaman gidan namu yake kowa 'yan dakinsu shine nashi saura kuma 'yan uba ne, sun maida 'yan uba tamkar wasu maqiyansu, Allah ya kyauta ya shiryar damu".

" Ameen Ya Rabbi, bari mu wuce Aunty Hasina sai kuma an kwana biyu".

"To Bello nagode, kuce wa Inna ina gaisheta, In Sha Allahu zan zo goben idan an barni, da wanne lokaci za'a amshi kayan ne?"

"Kamar karfe hud'u naji ance" Bellon ya amsa mata.


Kafin su kwanta da dare ne take shaidawa Usman batun zuwa karbar lefen A'ilo, kamar yadda ta zata kuwa be hanata ba don haka ta kwanta da d'oki da murnar zuwanta gida taje taga Innarta don kuwa tayi kewarta ba 'yar kadan ba, tunda aka yi aurenta sau d'aya taje gidan ta gaishesu ko shima ba yini tayi ba fisha suka je ita da Usman bayan sallar isha'i suka gaishesu suka dawo.


Kasancewar ranar ta asabar bata zuwa makaranta yasa da wuri ta gama kimtsa gidan tayi wanka ta shirya sannan ta sallami Usman da har lokacin yake nad'e akan doguwar kujera bai kai ga tashi ya fita kasuwa ba tukun ta fice zuwa gidansu.

Tun daga soro take kwad'a sallama sai dai babu wacce ta amsa daga cikin matan dake zaune a tsakar gidan, sai da ta shigo har tsakar gidan ta qara yin sallamar a karo na hud'u kafin Yaha ta amsa da "haba da kece kika ishemu da sallama tamkar sabuwar marokiya sai kace gidan bakonki ne, da kika yi sallamar farko kika ji ba'a amsa ba ai sai ki shigo kawai ba sai kin kashe mana kunne ba da wannan muryar taki mai amon tsiya kamar gangar makad'i".

Wato dai sallamar ce ba za'a amsa ba tunda ai ba'a amsa mata ba sai binta da akayi da bakar magana tamkar dai ba'a yi maraba da ganinta ba.

Ganin irin tarbar da ta samu yasa bata tsaya gaishesu ba tayi wucewarta d'akin Inna inda ta taddata akan keke tana d'inki.

Durkusawa tayi ta gaisheta kafin ta samu wuri ta zauna suna hira jefi-jefi ita da Innar.

Ita dai Inna Habi sai satar kallon 'yarta take yi tana mamakin sauyin da ta gani a tattare da 'yar tata ga dukkanin alamu dai hankalinta a kwance yake duba da yadda ta murmure tayi qiba.

Sai yanzu taji hankalinta ya kwanta da auren 'yar tata har taso ta kasa boye halin da zuciyarta take ciki na farin ciki abinda ya janyo hankalin Hasina har ta kai ga tambayarta "Inna wani abu ya faru ne na ga kamar kina murna ko farin ciki ne zance?"

Murmushi Innar tayi tare da kawar da kanta gefe kafin ta amsa mata da " eh farin cikin ganin ki ne kawai, naji dad'in ganin ki a haka ga alama kina cikin kwanciyar hankali ba sai an tambaya ba ga kuma karatunki da Bello yace mini kin cigaba, shi yasa yake da kyau bawa ya amshi qaddara a duk yadda tazo mishi don bai san me Allah yake nufi da hakan ba, kinga da kina ta kuka kina ganin kamar Babanku ya cuceki da irin mijin da ya zabo miki sai gashi shi d'in da kike gudu ya zamo alkhairi ga rayuwarki".

"Haka ne Inna, shi yasa na kasance a kullum cikin godiyar Ubangijina da irin zabin da yayi mini domin na samu Usman fiye da yadda na tsammace shi" tayi maganar cikin jin kunya fuskarta d'auke da murmushi.

Hira suke yi mai dad'i irin ta 'ya da uwa sai dai mafi akasarin hirar nasiha ce Inna take yi mata akan muhimmancin hakuri a cikin zamantakewa.

A cikin hirar ne take gaya wa Inna yadda suka yi da Yaha a tsakar gida har ma da rashin gaisuwar da bata yi musu ba don sosai taji haushin abinda suka yi mata.

A take yanayin fuskar Innar ya canja daga fara'ar da take yi. Fad'a ta rufeta da shi akan dalilinta na qin gaishe su, wacce irin tarbiyya take so ta nuna musu ta samu a irin hakan da tayi, duk yadda Hasina taso ta kare kanta Inna ba ta bata dama ba, a takaice ma dai cewa tayi Hasina ta fitar mata daga d'aki idan har ba zata je su gaisa da mutanen gidan ba.

Tashi tayi ta fita don su gaisa d'in kamar yadda Innarta take so. Dakin Murja ta fara shiga da sallamarta, sai bayan an amsa sannan ta shiga ciki.

Daga bakin kofa ta tsuguna tana gaisheta, babu yabo babu fallasa haka ta amsa, da ta tashi zata fita ne Murjar ke ce mata "wannan irin fari naki haka Hasina ba dai mai kika fara shafawa ba ko? Ko dai har na kai ga jika ne na fara tanadi?"

Murmushi kawai tayi mata ba tare da ta amsa ba ta fice daga d'akin.

A d'akin Yaha kam da kyar ta iya bud'e baki ta amsa gaisuwar da Hasinan ke yi mata don haka nan take jin haushin yarinyar dad'in dad'awa kwanciyar hankalin data lura Hasinar ta samu a gidan aurenta abinda ba haka hasashensu ya nuna musu ba.

Ita kam da tasan abinda Hasina zata tarar a gidan aurenta kenan ai da duk yadda zata yi sai tayi don ganin ba'a yi wannan auren ba koma ya juye akan 'yarta kawai. Amma babu komai ko a yanzun ma ai bata makara ba tunda don Usman na auren Hasina ba shine zai hana shi auren Hadiza ba, ai ba haramun bane don ya had'asu su biyun ya aura tunda ba ciki d'aya suka fito ba.

UMMASGHAR.

QADDARAR MUTUM Where stories live. Discover now