BABI NA HUDU

558 53 7
                                    

Hasina ta taso wata irin yarinya mai wauta ko wacce irin magana tazo bakinta zata fadeta ne ba tare da ta tauna ba, hakan baya rasa nasaba da yadda ta taso a sangarce don ko kadan Abubakar baya son laifinta har gara ma Habiba ta kan tsawatar mata lokaci zuwa lokaci.

"Kacora ina zaka kai hakora? Saran kashi nake wa mahauta. Kacora ina zaka kai hakora? Saran kashi nake wa mahauta.." Hasina ce ta tara yara tana basu waka suna yi mata amshi suna bin mutumin suna tsokana, da sunga alamun zai juyo sai su kwasa a guje suna dariya.

Ba tare da ta ankara ba kawai sai ganinta tayi a gabanshi, juyawa tayi da niyyar gudu yace "Hasina Abubakar kenan miye na gudu bayan zamu hadu ranar litinin a makaranta".

Tuni cikinta ya bada sautin kululu don tsoro, shaf ta manta da cewa malamin su ne na makarantar boko da bata fara tara yara sun yi mishi iya shege ba.

Bahaushe yace wai a bakin wawa akan ji magana, malamin maths din su ne na makarantar boko hakoranshi irin masu gatso din nan ne to shine yaran suke yi mishi wakar amma fa a boye, sai gashi yau Hasina ta tona musu asiri.

Kwanciyarta tayi a safiyar litinin tace wai bata da lafiya duk don kada taje makaranta don haka Babanta yace tayi kwanciyarta ta huta ba sai taje ba.

Inna na jiyo su daga tsakar gida don haka ta mike ta isa kofar dakin tasa hannu ta daga labulen bakin kofar tace "wannan ne kuma karya yarinya, makaranta ce kamar kin je ta kin gama don dama Tasiu ya fada mini kince rashin lafiyar karya zaki yi saboda kin tara yara kun tsokani malaminku kin san idan kika je dole a hukuntaki, dama na zuba ido ne naga iya gudun ruwanki na kuma gani don haka tun muna shaida juna ki tashi kiyi shirin makaranta ki tafi".

Baba ne yace "asha amma ban ji dadi ba Hasina, ashe ban hanaki tsokanar mutane ba?"

Kuka tasa tana cewa " Baba kayi hakuri wallahi idan naje makarantar zane ni zai yi".

"Ai gara ya zaneki din tunda ke ba kya jin magana" Inna tayi maganar a hassale.

Lallashinta Baba yayi tayi har ya samu ta hakura tayi shiru bayan yayi mata alkawarin rakata makarantar ya bawa malamin nasu hakuri.

Tare suka je makarantar, suka kuwa taki sa'a don Mallam Sabi'u wato malamin data tsokana ne a bakin gate yana taron 'yan latti.

Hannu Baba ya mika mishi suka yi musabaha kafin yace "ayi hakuri Mallam, Hasina ta fada mini tayi maka laifi shi yasa ma ta kwanta a gida tace ba zata zo ba don tasan idan tazo dukanta zaka yi, nayi mata fada tace ba zata kara ba don Allah ayi mata hakurin wannan karon idan ta kara ni da kaina zan kawota ku hukuntata".

Kunyar Mallam Abubakar ce tasa Mallam Sabi'u ya hakura ya kyale Hasina amma da yaci alwashin sai yayi mata dukan kawo wuka yadda a gaba ko da kudi aka ce tayi tsokana ba zata kara ba.

A haka Hasina tayi ta girma har Allah yasa ta shiga aji biyu na karamar sakandire wato jss2 anan makarantar da Babanta yake koyarwa wato GSS Giginyu.

Har zuwa wannan lokacin bata rage komai ba kama daga rashin ji, wauta da kuma tsokana sai ma abinda yayi gaba.

A ranar wata alhamis ne bayan sun taso daga makaranta take ta zuba sauri, so take ta isa gida taga yaya jikin Babanta don yau a gida ta barshi bai je wajen aiki ba saboda ciwon kai da ya sako shi gaba a cikin 'yan kwanakin nan.

Tun daga nesa ta hango kofar gidansu dankare da mutane, bata kawo komai cikin ran ta ba don haka koda ta iso kofar gidan kokari kawai take yi ta ratsa mutanen ta wuce cikin gida don ta lura ashe mutanen ba a wajen gidansu kadai suke ba har ma da cikin gidan mata ne dankam.

Tunda ta shiga take ware ido tana neman ta inda zata ga Innarta. Ganin bata a tsakar gidan yasa ta tsallakawa don ta wuce dakin Innar don ta fara tsorata da yawan mutanen da ta gani a cikin gidan nasu.

A tsakar kanta taji muryar Yaha matar Kawunta Basiru tana ce mata "Allah Sarki Hasina yau gatanki ya fadi, Abubakar kuma kwana ya kare".

Bata san lokacin data fada dakin Innarta ba tana kwala mata kira, ganin da tayi mata a zaune akan sallaya a tsakar dakinta tana jan carbi tana kuma share hawaye da gefen hijabinta ya tabbatar mata da maganar da Yaha ta fada mata gaskiya ce.

Wani irin ihu ta saki tana birgima a kasa tana cewa "wayyo Allahna, wayyo Baba me yasa zaka yi mini haka? Yaya zaka tafi ka barni Baba? Na shiga uku na lalace".

Yi take tana karawa duk cikin dakin an rasa mai lallashinta sai zuwa can kakarta mahaifiyar Inna ta shigo dakin daga waje inda suke zaman karbar gaisuwa ta dagata tana bata hakuri.

"Kiyi hakuri Hasina, Abubakar kwanakin daya debo sun cika, hakan ba yana nufin yayi gaggawa bane haka nan mu da muke nan ba muyi garaje ba kowa lokacinshi yake jira, babu abinda yake bukata daga wajenki a yanzu face addu'a don itace karshen soyayyar da zaki nuna mishi, ihunki da hargagi ba zai kareshi da komai ba don haka ki bari bashi da wani amfani".

A haka ta lallabata ta shigar da ita dakinta ta zauna, sai dai duk yadda taso taci abinci ki tayi don haka ta kyaleta.

Haka aka share zaman makoki kowa ya watse aka bar Hasina da Innarta sai wata Goggon Innar da aka bari don ta taya su zama.

Tun bayan mutuwar Babanta Hasina ta koma wata shiru-shiru bata um bata um-um, sosai mutuwar Baban ta doketa sai ta koma wata salaha wacce magana ke mata wahala.

Da kyar Inna ta lallabata ta koma makaranta a cewar Innar karatun zai debe mata kewa tunda idan ta zauna a gidan ma babu abinda take yi.

Ko kwana arba'in Abubakar bai cika da rasuwa ba Basiru ya bullo da maganar rabon gado, a cewarshi gara a raba don a saukewa mamacin nauyin dake kanshi, Inna bata ki ba don tasan neman magana yake yi sai dai ta roki alfarmar a barta tayi takaba a dakinta.

Bayan anyi rabon kuma sai yace sai ta tashi daga gidan don shi ke da alhakin kulawa Hasina da dukiyarta tunda gidan ya fado a kasonta ne zai kuma zuba 'yan haya ne a ciki yadda zai samu abinda zai dauki dawainiyar ta dashi.

Bata qi tashi ba don haka ta hau kimtsa kayanta don komawa gidan mahaifinta, ganin da yayi wannan ba zata kai mishi ba sai ya bullo da cewa wai bai yadda ta tafi da Hasina ba sai dai ta tafi ita kadai ita kuma Hasinar ta koma gidanshi cikin iyalinshi.

To anan ne tayi tsallen albarka tace bata yarda ba don bata ga dalilin da zai sa yace sai ya rike 'yarta ba, dukiya ya nema sun kuma bashi.

Rigima sosai aka yi tsakaninta da Mallam Basiru shi ya dage akan sai ta bashi riqon Hasina ita kuma tace bata ga mai rabata da 'yarta ba, rigima taki ci taki cinyewa a karshe sai cewa yayi idan har tana son ta rike 'yarta to sai dai ta amince ta aure shi idan ba haka ba kuwa tayi sallama da kara zama da 'yarta. To dama dai abinda yake yiwa kenan yake ta wannan kwane-kwane.

Nan ma Habiba tayi tsallen albarka tace bata yarda ba, hasali ma ita bata da niyyar yin sure kwana kusa kuma ko auren zata yi ma to ba da Mallam Basiru ba. To anan ne mahaifiyarta tace "ko dai ki yarda ki aureshi son ki samu ki riqe 'yarki a gabanki ko kuma ki haqura ki bashi ita don na gaji da wannan rigimar taku ke da Mallam Basiru shi yaja ke kin ja an rasa wanda zai saki ya barwa dan uwanshi, amma ni a shawarata gara ki aureshi kine ki riqe 'yarki ko kya samu ta taso da irin tarbiyyar da kike mata don kin san dai yaran gidan ba tarbiyya ce ta wadace su ba".

Dole kanwar naki Inna ta yadda ta auri wan mijinta Mallam Basiru ta tare da 'yarta Hasina, a wannan lokacin kuwa matanshi biyu da 'ya'ya goma sha daya.

UMMASGHAR.

QADDARAR MUTUM Where stories live. Discover now