BABI NA BAKWAI

494 50 5
                                    

Shi ya tasheta da asuba don tayi sallah kafin ya wuce masallaci. Lokacin da ya dawo ya samu har ta idar da sallah tana dan kikkimtsa gidan duk da ba wani datti ne a cikinshi ba.

Ajiye tsintsiyar hannunata tayi ta durkusa ta gaishe shi. "Lafiya lau Hasina, kin tashi lafiya? Ya kwanan bakunta?"

A kunyace ta amsa mishi da "lafiya lau" ba tare da ta dago kai ta kalleshi ba.

Wucewa yayi ciki ya barta a tsakar gidan tana karasa sharar da take yi.

Tana gamawa ta janyo ruwa a rijiya ta cika robobin ruwanta kafin ta koma dakin.

Yana kwance akan doguwar kujera yana daddana waya ta shigo, sa kai tayi zata wuce uwar dakinta ya tsaida ita ta hanyar kiran sunanta.

Dawowa tayi ta zauna akan kujerar zaman mutum daya tace mishi "gani".

Tashi yayi zaune yana kallonta sai dai ya rasa ma me zai ce mata don samun kanshi kawai yayi da kiran sunanta ba tare da ya shirya abinda zai ce mata ba.

Murmushi yayi hade da sosa kai kafin yace "bari naje na samo kananzir ko sai ki dafa mana ruwa mu sha shayi".

"To" kawai tace ta mike ta koma cikin dakin.

Bata zauna ba ta wuce bandaki ta hada ruwa tayi wanka, a gaggauce ta shirya cikin atamfar flora batik mai zanen ganye kalar blue da yarfi-yarfin yellow a jiki dinkin A shaped gown, bata daura dankwalin kayan ba sai wani siririn mayafi kalar yellow da ta yafa a kanta.

Komawa tayi parlour ta zauna, bata jima a wurin ba taji yana kwalo mata kira daga waje ashe ya dawo ma bata sani ba.

Tashi tayi ta fita bayan ta amsa kiran, anan tsakar gidan ta iske shi yana saka lagwani a cikin risho.

Gefe taja ta tsaya tana kallon abinda yake yi, sai da ya gama sannan ya dura kananzir din a ciki. Kitchen din ya maida mata ya ajiye kafin ta shiga ta fito da butar dafa ruwan zafi da kofuna da cokali ta dawo nan tsakar gidan daga bakin rariya ta debi ruwa ta wanke sannan ta debi ruwa a butar ta koma kitchen din ta dora.

Bata fita ba har sai da ya tafasa ta juye a cikin qaton flask dinta na ruwan zafi ta shirya kayan akan tray don ta samu ya shigo da kayan shayi da biredi ya ajiye akan kanta anan kitchen din ta dauka ta nufi daki.

A tsakar parlour ta ajiye tray din akan carpet din dake shimpide a tsakiyar parlour ta samu waje kan kujera ta zauna don bata iske shi cikin parlour ba koda ta shigo.

Daga cikin dakin ta jiyo shi yana ce mata "kin gama ne?"

"Eh" ta amsa mishi, "ok gani nan".

Koda ya fito sai taga ashe wanka yayi shima don yayi shirin shi tsaf cikin shadda kalar ash dinkin tazarce da aka yiwa adon surfani da zare kalar ash mai turuwa sai kamshin turare yake yi.

Zama yayi a kasa tare da janyo tray din gabanshi, tana ganin haka tayi maza ta sauko ta dauki kofi ta hada mishi tea din ta ajiye a gabanshi sannan ta koma gefe ta zauna.

Kallonta yayi da alamar tambaya kafin yace mata "aa ina naki shayin kika koma gefe kika zauna, ungo wannan ni bari na hada wani" ya miko mata kofin shayin dake hannunshi.

"A'a ka barshi ai naka ne wannan bari na hada nawa" tace tana daukar wani kofin tare da tsiyaya ruwan zafin a ciki ta hada shayin dan dai-dai don ba wani damunta shayi yayi ba.

Cikin shiru suka yi karin kumallon, bayan sun gama ne ta tattare kayan da suka yi amfani dashi taje ta wanke.

Zamanta tayi a kitchen din don bata san me zata yi ba idan ta koma dakin.

Aqalla zata yi minti goma a ciki tana tunane-tunanen da inda za'a tsareta ba zata ce ga takamaimai tunanin me take yi ba.

Alamun tsayuwar mutum taji a kanta don haka ta dago ta kalli bakin kofar.

QADDARAR MUTUM Where stories live. Discover now