Zaman Hasina da Innarta a gidan Kawunta Basiru kadaram kadaham karatun dan kama wato dai babu yabo babu fallasa don Mallam Basiru yana qoqarin ganin ya basu kulawa hakan kuma baya rasa nasaba da irin matsanancin son da yake yiwa Habiba duk da dai yana qoqarin dannewa don kada a gane.
Ba'a dauki wani dogon lokaci ba matan gidan wato Yaha da Murja suka murda kambunsu na uwayen gida suka ce basu yarda da rashin adalcin da yake gwadawa ba a tsakaninsu dole ne Habiba ta shiga cikin hidimar gidan kamar yadda suke yi ko kuma suma ya dauke musu larurorinsu kamar dai yadda yake yi mata.
Wani hali na Mallam Basiru da ban sanar muku ba shine sakarwa iyalinshi ragamar kula da gida, kama daga kan cefane, sabulun wanka da wanki, omon wanke-wanke, kudin nika, kudin pensir zuwa litattafan makarantar 'ya'yansu duk sune, kai hatta da dinkin sallah tsananin rabo ke sawa yayi musu idan bai yi ba kuwa sai dai iyayen yaran mata su yi musu don haka ne ma suke tanadin su da wuri ba tare da sun jira shi ba idan yayi wala ba'asa idan bai yi ba ma sammakal, shi dai nashi ya bada hatsin da za'a dafa kawai kowa tasan yadda tayi ta sarrafa shi.
A hakan kuma har kuji yana balokokon masifa yana cewa anyi wani abu ba daidai da yadda shi yake son shi ba.
To zuwan Habiba sai ya zamanto duk wadancan hakkukuwa da baya iya sauke wa iyalinshi ita yana qoqarin ganin yayi mata su don haka suka yi tsallen albarka suka ce basu yarda ba ai suma mata ne basu ga da me Habi ta fi su ba da zai fifita al'amuranta akan nasu.
To dai ba'a je ko ina ba Habi da 'yarta Hasina suka tsinci kansu a cikin wata irin bakuwar rayuwa da da can basu san da irinta ba, a wannan lokacin kuwa Habiba na dauke da ciki watanni bakwai kenan. Koda ta nemi ta botsare ta nemi da ya sauwake mata aurenshi dake kanta don ba zata iya rayuwar ci da kai ba sai Mallam Basiru yayi mata ta malaman zamani ya kafeta a gidanshi yadda idan ba shi ya bata izinin fita ba ko kofar gida bata isa ta leqa ba bai kuma barta haka nan ba sai da ya hada mata da mallaka ta yadda duk abinda yace bata iya musa mishi ko da kuwa zuciyarta bata yi na'am da abin ba.
Dole kanwar naki tasa Habiba kama sana'o'in hannu, inda Allah ya taimaketa ta iya dinki tana kuma da keken dinkin don haka ta kama sana'ar dinkin ka'in da na'in ga kuma ruwan sanyi da lemon zoborodo da take sakawa a freezer, sosai kuwa take ciniki don har cikin gida ake zuwa sayen zobo da ruwan sanyi.
Alkawari ne kullum akwai kason Mallam Basiru a cikin zobon da Habiba take kullawa ba tare da ko sisin shi ba don idan ma bata bashi ba ya dinga bala'i kenan yana masifa yana cewa sai ya hana sana'ar yaga ta tsiya sai kace ba shi take rufawa asiri ba.
Ruwan sanyi kuwa dama ai sai dai idan bai ji kishiruwa ba yanzu ne zai je ya bude freezer ya dauka yana muzurai duk don kada a kawo mishi wargi.
A cikin wannan halin ne Allah ya sauki Habiba ta haifi danta namiji aka sa mishi suna Bello, cikin hukuncin Allah ba sai haihuwa ta budewa Habiba ba don bayan Bello sai da ta qara haihuwar wasu yaran uku duka maza wato Habibu, Kamal da Sa'id.
Hasina na aji hudu na babbar sakandire Mallam Basiru ya bullo da zancen yi mata aure da dan amininshi Mallam Tukur wato Usman.
Suna zaune a tsakar gida kowa tana harkar gabanta tare da 'ya'yanta. Hasina dai kullin zobo take taya Innarta anan kofar dakinsu, sai Murja wacce ke da girkin ranar dake ta kujiba-kujiba wajen ganin ta kammala hada sanwa kafin hadarin dake gabas ya kai ga sauko da ruwa. Ita kuwa Yaha kullin kayan miya da take sayarwa take yi itama anan kofar dakin nata.
Shigowa yayi cikin gidan ba tare da yayi sallama ba ko da shike dama hakan al'adar shi ce baya taba shiga gidanshi da sallama wai a cewarshi ai gidanshi ne don haka bai ga dalilin da zai sa shi yin sallama ba don zai shiga.
Yana muzurai yana ciccin magani ya dubi Hasina dake taya Innarta kulla zobo yace "Ke Hasina ki shirya in anjima yaron nan Usman dan wajen aminina Mallam Tukur zai zo ku gana don nace mishi yazo ya ganki idan kin yi mishi to na bashi ke".
Tsit tsakar gidan yayi don mutanen gidan sun mayar da hankali wajen maganar da Mallam Basiru yake yi.
Ai bata san lokacin da ta saki ledar zobon dake hannunta ba ya tsiyaye a kasa, tuni idanunta suka fara tsiyayar da ruwan hawaye, cikin rawar murya tace "Baba karatuna fa?"
"Ungo nan" ya hada hannayen shi duka biyu yayi mata dakuwa. "Ke nan har kin isa nace ga abinda za'ayi ki gardama mini, ko ubanki Abubakar bai yi isar da zance ga abinda nake so yayi mini gardama ba bare ke".
"Mtsew..." yayi tsaki yasa kai ya wuce zuwa dakinshi.
Anan a tsakar gidan ta durkushe ta fara gursheken kuka.
Innarta da maganar ta mijinta ta daketa fiye ma da yadda ta yiwa 'yarta Hasina ta daka mata tsawa tace "sakarcin banza da wofi kai, da kika zauna anan kina kuka maganin me zai yi miki, dauke mini ledar sikarin ki shige dashi daki ni na karasa aikin".
Habiba tayi dabarar tura Hasina daki don ta lura kamar matan gidan murna suke yi da halin da suka tsinci kansu a ciki ita da 'yarta.
A gaggauce ta gama aikin ta kakkauda kayan aikin nata sannan tasa tsintsiya da ruwa ta share wurin da suka yi aikin ta dauki bokitin da zobon da suka kulla ke ciki ta shige daki.
Sai da ta shirya zobon tsaf a cikin freezer kafin ta wuce uwar dakinta inda take jiyo kukan Hasina na tashi kasa-kasa.
Dakin ta shiga ta zauna a bakin gado ta dafa bayan Hasina data dunkule a waje daya tana kuka kamar curin kayan wanki, tausayin 'yarta ya kamata don tasan cewa tunda Mallam ya ambaci batun auren nan to fasa shi sai dai wani ikon Allah.
Ita kanta tana mamakin yadda a yawancin lokuta ake yi musu shiga hanci da kudundune ita da 'yarta amma bata iya katabus a kai koda kuwa ta yunquro don ta magantu sai abin ya gagareta sai dai yayi ta cinta a zuciya.
"Kiyi hakuri Hasina, shi bawa baya taba tsallake qaddararshi, idan kika ga anyi aurenki da Usman to dama can Allah ya qaddara shi din mijinki ne idan kuwa har baya rubuce a cikin qaddararki to fa ko an taru don a daura aure za'a fasa saboda Allah bai rubuta shi din zai zamo abokin rayuwarki ba. Don haka kiyi hakuri ki cire damuwa daga zuciyar ki, ki mika dukkan al'amuranki ga Ubangiji shi ne zai iya miki".
Tashi tayi zaune tana goge hawaye da bayan hannunta tace "Inna tsoron auren nan nake don kuwa Baba bai taba nufa ta da wani abu na alheri ba, ni nasan da ace alheri ya hango a cikin wannan auren ba zai soma tunkarar mu da zancen ba sai dai ya hada A'ilo ko Hadiza da shi don sune 'ya'yanshi su yake so kuma sune suka gama makaranta suke zaune a gida babu cigaba amma bai yi hakan ba sai ni da ko karatun sakandiren ban samu na gama ba zai bullowa da zancen aure".
Tasan cewa gaskiya 'yar tata ke fada don ko ita sai da wannan tunanin ya darsu a ranta to amma tasan cewa babu wanda yasan mai gaba zata haifar sai Allah, tana iya yiwuwa da wata manufa aka shirya auren idan Allah yaso kuma sai kaga ya maida shi mafi alheri ga rayuwar 'yarta zai kuma iya yiwuwa da kyakkyawar niyya aka kulla auren, Allah shi ya barwa kanshi sani don haka tsakanin ta da 'yarta addu'a ce kawai, fatanta Allah yayi mata zabi mafi alkhairi ga rayuwarta.
Don haka tace mata "addu'ar nan dai da nace miki ita zaki yi tayi don baki san me Allah ya shirya wa rayuwarki a gaba ba, karatu kuma idan har kina da rabo sai kiga ko a gidan aurenki kin samu kin cigaba idan kuma iya bakin rabonki kenan sai kiyi fatan Allah ya albarkaci abinda kika samu, dama ai albarkar ake yiwa ba yawan kwalin ba".
UMMASGHAR.
YOU ARE READING
QADDARAR MUTUM
RomanceRayuwar MUTUM tana tafiya ne a bisa bigire na QADDARA haka nan kuma bawa bai isa ya kauce mata ba. Shi yasa ma yarda da ita yake daga cikin shika-shikai na imani. Ku biyo ni cikin labarin Hasina don jin tarin qaddarori da ke bibiye da rayuwarta.