BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
DUKKININ YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DA YA BANI IKON DAWOWA CIKIN SABON LITTAFINA MAI SUNA QADDARAR MUTUM. YADDA NA FARA RUBUTUN NAN LAFIYA ALLAH KASA NA GAMA LAFIYA KASA MU AMFANA DA DARUSSAN DAKE KUNSHE CIKIN LABARIN.
Tunda ta tsuguna a wurin da sunan gaishe shi yake jifanta da wani irin wulakantaccen kallo, abinda ya qara kashe mata jiki yasa ta tunanin makomar rayuwarta.
Tsawon mintuna biyar tana zaune a wurin jiran jin hukuncin da zai yanke mata tunda tasan abinda kenan, gabanta sai matsanancin faduwa yake yi, ta qagara yayi magana ko tasan makomarta.
Sai da ya mula ya mule sannan yace "kin kwaso kafafu ne kin dawo mini gida don ki nuna mini ban isa dake ba ni ba a bakin komai nake a wajenki ba ko me? Kin mance yadda muka yi dake kafin a kaiki gidan miji cewa in har kika kara kashe aurenki to ki san wajen zuwa amma ba gidana ba? Raini ne yasa kika sa kafa kika ture maganata? Tun muna shaida juna ki san inda dare yayi miki domin kin bar kashe aurenki ki zo kina yin mafaka a gidana, mutane nayi mini kallon tsohon banza wanda ya gagara bawa 'yarshi tarbiyyar zaman aure, kin bace mini da gani ko sai na tashi na karairaya ki a wajen nan". Ya qarashe maganar cikin matsanancin fushi.
Tunda ya fara fada take sharar hawaye, ita tasan abinda yafi haka ma zata iske in dai wajen Baba ne, to sai dai ya kamata ya fahimci cewa ba'a son ranta aurarrakin da tayi suke mutuwa ba, qaddarar tace tazo a haka.
Cikin kaskantar da kai take faman bashi hakuri duk da tasan cewa ba lallai ya aminta da hakurin da take bashi ba, to amma babu yadda ta iya don bata da wani wurin zuwa daya wuce gidan nashi.
Bata ankara ba sai ji tayi ya jefeta da butar karfe dake ajiye a gefenshi, sauran ruwan da yayi alwala ya jika hijabin dake sanye a jikinta, cikin rashin kuzari ta mike tana kakkabe jikinta.
Ganin da tayi babu alamun sassauci a tare da Baban yasa ta juya da niyyar barin unguwar tana tunanin inda ta dosa. Abin takaicin ma shine ko kudin da zata hau mota bata da shi.
Tafe take tana tunanin inda ta dosa, kiran sallar magariba ne yasa ta takaita tafiyar da take yi. Dan gajeren tunani tayi ta juya zuwa gidan makociyarsu Aunty Zulai wacce kuma ta kasance aminiya ga mahaifiyarta Inna.
A bakin kofar da zata sadata da cikin gidan daga soro ta tsaya tana sallama, jin ba'a amsa ba yasa ta shiga ta samu wuri a tsakar gidan ta zauna tana jiran ganin ta inda Aunty Zulai zata bullo.
Bata jima zaune a wurin ba ta fito tana cewa "wa'alaikissalam, bakuwa muka yi, na shiga sallah kenan kika shigo".
Daga bakin kofa ta tsaya tana kare mata kallo da son tantance bakuwar tata kasancewar duhun dare ya fara shigowa gashi kuma babu wutar nepa a gari "au Hasina ce? wallahi ban dauki muryarki ba, Sannu da zuwa" tace tana mai zama akan tabarmar da Hasina ke zaune akai.
"Eh Aunty nice, ina yini" ta gaisheta tana mai russunawa.
"Lafiya lau Hasina. Ya wajen naku da abokiyar zaman naki duk lafiya dai ko?" ta amsa mata gaisuwar hade da jeho tambayar duk a lokaci daya don tayi mamakin ganinta a daidai wannan lokacin, duk da cewa Hasina na yawan shigowa ta gaisheta a duk sadda ta kawo ziyara gida to amma ba a irin wannan lokacin ba.
"Lafiya lau Aunty, dama cewa nayi bari na shigo nayi sallah sai ki kira mini Inna a waya, nazo gidan Baba ya hanani shiga".
" Subhanallahi, shi kuwa Mallam me yasa yake haka? Tashi kiyi alwalar ga buta nan kin san lokacin magriba gajere ne".
Kafin Hasina ta idar da sallar har ta shirya mata abinci akan tabarmar, tuwon alkama ne miyar danyar kubewa.
Koda ta idar bata bari sun yi magana ba tasa ta a gaba har sai da taci abincin sosai sannan ta kira mata Innarta a waya ta tashi ta bata wuri don ta samu sararin yin magana da mahaifiyarta don ganin nan da tayi mata tasan bana lafiya bane.
"Assalamu alaikum, Auntyn yara barka da dare" Innar ta amsa a daya bangaren.
" Wa'alaikissalam, Inna nice Hasina" tayi maganar muryarta na rawa da alamun son yin kuka.
"Hasina? Lafiya da daren nan kuma baki shigo gida ba?" tayi tambayar gabanta na faduwa don bata son Hasinar ta sanar da ita abinda zuciyarta ke zargi.
"Nazo gidan ai Baba ne ya hanani shigowa yace tunda na sake kashe aurena ba zan zauna mishi a gida ba, Inna Sagir ya sakeni kuma wallahi ba laifina bane matarshi ce tace lallai sai ya sakeni don ta gaji da zaman namu haka" ta karashe maganar da kuka.
Shiru Inna tayi don ta rasa kalmomin da zata yi amfani dasu wajen lallashin 'yarta. "Kinga kiyi hakuri ki bar kukan haka nan, na san akwai ciwo mutuwar aure to amma ya za muyi tunda hakan yazo a cikin kaddararki, dole muyi hakuri mu sanyawa ranmu dangana Allah yasa hakan ne mafi alkhairi ya baki wanda yafi shi.
Zan roki Auntyn Yara ki kwanan nan wajenta kafin nayi magana da Auntynku gobe sai ki tafi can wajenta ai dama ta dade tana son rikonki ya koma hannunta ni nake ki saboda sanin halin Mallam da nayi, yanzu kuwa tunda da kanshi ya koreki ya hana miki zama gidanshi sai ki koma wajen Hannen".
Ta cigaba da lallashinta tare da kwantar mata da hankali har sai da ta fahimci ta samu nutsuwa kafin suka yi sallama akan cewa gobe Hasina zata koma gidan kanwar Inna wato Aunty Hanne ta zauna acan har sai yadda hali yayi.
UMMASGHAR.
YOU ARE READING
QADDARAR MUTUM
RomanceRayuwar MUTUM tana tafiya ne a bisa bigire na QADDARA haka nan kuma bawa bai isa ya kauce mata ba. Shi yasa ma yarda da ita yake daga cikin shika-shikai na imani. Ku biyo ni cikin labarin Hasina don jin tarin qaddarori da ke bibiye da rayuwarta.