A yammacin ranar ne Aunty Hanne taje ta debo mata sutturunta daga gidan Sagir, a sonta su tafi tare sai dai kuma ta dage akan cewa bazata ba don bata so ko hanya ta qara hadata da wannan unguwar.
Sakin da Sagir yayi mata ba karamin dukanta yayi ba don bata tsammaci hakan daga wajenshi ba, duk a tunaninta wahalarta ta yanke tunda Allah ya hadata da shi bare kuma da ya kasance duk cikin mazajenta yafi kwanta mata a rai.
Kwananta uku a gidan Aunty Hanne ta dauketa suka je asibitin da suke zuwa aka bude mata folder taga likita akan harkar cikinta da kuma larurar dake tare da ita.
Bayan ya dubata ya bata shawarwari akan yadda zata kula da kanta da irin abincin da zata ke ci don inganta lafiyarta data abinda ke cikinta.
Kudi sosai Aunty Hanne ta kashe wajen sayen magungunan da zata yi amfani dasu da kuma allura.
Babu laifi ta samu kwanciyar hankali don aqalla yanzu ta samu sati uku a gida, a kwance take a wajen da tayi sallar la'asar a dakin da ya zamo nata a gidan na Auntyn ta, tunanin yadda rayuwa take buga kwallo da ita take yi har bata san sadda ta fara zubar da kwalla ba.
Tattausan hannun Aunty Hanne wanda bata rabo da shafa mishi man saka taushin hannu wato hand cream na kamfanin Oriflame dake kasar Sweden ne ya sauka a fuskarta tana goge mata hawaye, har kullum Hasina na mamakin gayu da son kyale-kyale irin na Auntyn tata, komai da take amfani dashi mai kyau ne da inganci.
Ada Hasina bata da wani buri a rayuwa irin na ganin tayi aure ta mallaki gidan kanta har ma take tafiyarta da rayuwarta kamar yadda taga Auntynta nayi cikin tsari na ilimi da wayewa, sai dai kuma kash rayuwar bata zo mata a yadda ita ta tsara ta ba sai ma tazo mata da tarin qalubale da jarabawoyin da take fatan Allah ya iyakance mata su yasa ta cinyesu da maki mai kauri.
Murmushin yake ta kirkiro ta dora a saman fuskarta. "Kin san dai masu irin larurarki basa son yawan damuwa amma ke naga abinda kika sa a gaba kenan ko damuwa da lafiyarki ba kya yi, akwai wani daya isa ya yaye miki damuwarki banda Allah, me yasa ba zaki mika mishi al'amuranki ba kiyi fatan yayi miki kyakkyawan sakamako mafi alkhairi ga rayuwarki".
"Ba haka bane Aunty wallahi na fauwala dukkan lamurana ga Ubangiji ina kuma fatan yasa na cinye jarrabawar da yayi mini, to amma tunanin ne yin kanshi yake don bana sanin sadda yake zuwa mini sai dai na tsinci kaina nayi zurfi a cikinshi"
"Ba dole tunani ya aure ki ba tunda kin tsame kanki daga cikin mutane kin zama daddawar daka" Aunty Hanne ta mayar mata."Yanzu tashi zaki yi mu shiga kitchen ki tayani hada abinci don nasan idan ma na kyaleki cigaba zaki yi da tunane-tunanenki na fama".
ASALIN LABARIN
Mallam Abubakar malami ne a makarantar secondary ta 'yammata dake unguwar giginyu a cikin birnin Kano. Su Biyu iyayensu suka haifa shi da dan uwanshi Basiru.
Shi Basiru Allah bai sa zai yi karatun boko ba don makarantar allo mahaifinsu Mallam Ghali ya kaishi a garin kura, shi kuwa Abubakar da yake Allah ya tsaga hanyar cin abincin shi ta sanadin bokon ne sai Mahaifinsu ya hakura ya saka shi a makarantar primary dake nan unguwar su bayan naci da kwawa da Abubakar din ya kafa mishi don shi da a son shi ya kai shi can kura inda ya kai dan uwanshi Basiru shima yayi karatun allo.
Tun bayan kai Abubakar makarantar boko kyashi da hassada ya darsu a zuciyar Basiru a game da dan uwanshi saboda yaso karatun na boko sanin da yayi mahaifin su baya ra'ayin karatun boko yasa shi hakura, a ganinshi shi ya dace a saka a makarantar ta boko ba Abubakar ba saboda shine babba.
Tun daga wannan lokacin Basiru ya debi idanu ya zuba akan Abubakar, duk wani cigaba na Abubakar baya son shi haka nan yana bakin cikin duk wani alkhairi da zai samu dan uwanshi koda kuwa ace shi ya samu mafiyin abinda Abubakar ya samu.
A lokacin da Abubakar ya samu ya kammala karatun shi na nce ne makwabcin su Mallam Isa ya nema mishi aikin koyarwa anan makarantar da yake principal ya kuma dauki 'yarshi Habiba wacce a lokacin ta kammala aji uku na karamar sakandire ya bashi saboda yabawa da nutsuwa da kamalar shi da yayi.
Wannan abu da Mallam Isa yayi wa Abubakar sai ya qara rura wutar qyashi da hassada a zuciyar Basiru don ashe wai ya dade yana son Habiba, sanin da yayi ba lallai ne ta kula shi ba tunda ita yarinya ce 'yar boko shi kuwa ko zo in kashe ka bai sani ba da yaren na nasara yasa ya hakura ya bar wa zuciyar shi bai furta mata ba sai kuma gashi ba tare da Abubakar ya nema ba an dauka an bashi.
Tuni 'yar sauran kaunar da yake yiwa dan uwan nashi ta bi ruwa don ya lura duk wani abu da yake so ko ya taba ayyanawa cikin zuciyarshi yana sha'awa sai ya zama mallakin Abubakar, a ganin shi Abubakar din yana sane yake raba shi da duk wani abu da yake so bayan ya manta cewa koda wasa ko a cikin hira ya nuna yana son wani abu da ya kasance mallakin Abubakar din a take yake bar mishi ba tare da wata damuwa ba.
Anan cikin gidansu Abubakar ya yanki fili yayi ginin dakunanshi falle-falle guda uku da bandaki da kitchen da dan madaidaicin tsakar gida.
Aurensu da wata biyu Allah yayi wa mahaifinsu Mallam Ghali rasuwa dama kuma tun Abubakar bai gama secondary ba mahifiyarsu ta rasu.
Ko wata guda ba'a rufa ba da rasuwar Mallam Ghali Basiru da matarshi Yaha suka tasa Abubakar da Habiba a gaba da kyara da tsangwama abinda yayi sanadin da ana yi musu rabon gado Abubakar ya sayi gida anan gaba dasu kadan ya tashi ya bar mishi nan din.
Shekararsu biyu da aure Allah ya azurtasu da haihuwar Hasina, tun bayan nan kuwa Habiba bata kara haihuwa ba sai bari da take yawan yi, hakan ne yasa suka dauki dukkan so da kulawa suka bawa Hasina kasncewarta 'ya daya tilo ya tsoka daya a miya da Allah ya basu.
UMMASGHAR.
![](https://img.wattpad.com/cover/191950062-288-k837892.jpg)
YOU ARE READING
QADDARAR MUTUM
RomanceRayuwar MUTUM tana tafiya ne a bisa bigire na QADDARA haka nan kuma bawa bai isa ya kauce mata ba. Shi yasa ma yarda da ita yake daga cikin shika-shikai na imani. Ku biyo ni cikin labarin Hasina don jin tarin qaddarori da ke bibiye da rayuwarta.