BABI NA SHIDA

559 51 2
                                    

Cikin kankanin lokaci maganar auren Hasina da Usman ta kankama har an yanke lokacin aure watanni biyu masu zuwa.

Tuni Inna ta fara fitar da tsohuwar ajiya tana shirin auren 'yarta duk kuwa da cewa ba farin ciki take yi da auren ba.

Hasina kam duk ta kare tayi dan wuya saboda damuwa da tasa a ranta dama kuma gata ba wani jikin kirki ke gareta ba.

Yayin da mutan gida ke murna ganin yadda Mallam Basiru ya ninke hannayen shi yaqi tabuka komai a harkar auren duk kuwa da cewa shi ya kawo mata mijin ya kamata ace sai da ya shirya kafin ya tunkari batun aurar da diya.

Koda Inna tayi mishi maganar kayan gado ma cewa yayi ina yaga kudin da zai iya sayen gado, shi baiga amfanin sana'arta ba idan har bazata iya tallafa mishi ba.

Haka nan ta daure tayi mishi maganar kudin hayar gidan Hasinar da yake karba tace ko zai bata wani abu daga ciki to ta hada da dan abinda ya rage a hannunta ta sayi kayan gadon tunda dama ai saboda amfanin gaba aka zuba 'yan haya a gidan.

Ai ko ida rufe bakinta bata yi ba ya hau surfa mata ruwan bala'i yace ya lura nema take yi ta tutsiye shi, tunda yace baya da hali ai sai ayi mishi hakuri idan dai ba sata take so yaje yayi ba.

Juyawa tayi ta bar dakin tana share hawaye da habar zaninta, kusan karo suka yi da Murja dake labe a bakin kofa tana sauraren tattaunawar su da maigidan.

Kunya ce ta kamata don bata tsammaci fitowar Innar a daidai wannan lokacin ba, ita kam Inna ko kulawa da ita ba tayi ba ta wuce zuwa dakinta don damuwar da take ciki tafi gaban ta tsaya kula da abinda Murjar take yi.

Gudunmawar da 'yan uwanta suka hada mata da dan sauran abin da ke hannunta aka hada aka sayawa Hasina setin kayan gado masu kyau a kan titin gandu da kujeru har da tv stand don har da kayan kallo Inna ta saya mata karamar talabijin da ake makalawa a jikin bango wato plasma tv mai inci 32 da dvd dinta sai karamin fridge.

Komai dai na kayan daki sun kammala tare da jajircewar Inna da tallafin 'yan uwanta, hatta da kayan gara Inna ta tanada ta ajiye babban buhun shinkafar ta daya da katan din taliya biyu makaroni biyu buhun semovita biyu, sai galan din man gyada da na ja sai kuma kayan miya dangin su daddawa, kuka, kubewa, busassun kayan miya da sauran su, sai kuma kayan su dibilan, alkaki da cincin da ta bayar ayi mata.

Hatta da abincin da za'a ci a bikin Inna tayi tanadin kayanta don ga take-taken Mallam Basiru da take gani babu abinda ya ajiye sai afkin nuna iko akan 'yar.

Saura sati biyu a saka Hasina a lalle dangin Usman suka kawo lefen su akwatina uku da kit, babu laifi don sun yi kokari sun zuba mata kaya masu kyau daidai karfinsu, suma kuma su Inna basu bar su haka ba sai da suka bisu da tukuici da kayan tarbar baki.

Su Aunty Hanne sun je sun shiryawa Hasina dakinta tsaf gwanin sha'awa sun jawo kofar sun rufe suna jiran ranar da zasu mika Hasina zuwa gidanta.

Ita dai Hasina da ido take bin kowa tana mamakin wai itace ake shirin aurenta, a wannan lokacin kuwa shekarunta na haihuwa goma sha biyar ne.

Ita dama ba mai yawan kawaye bace don haka ne ma da abokan Usman suka nemi data hada su da kawayenta don su ji tsare-tsaren su na biki tace musu bata da su a ganinta ko ace tana da kawayen ma auren ba irin wanda zata yiwa shiri ba ne tunda ba wai ita ta zabo mijin ba bare ace tana son shi.

Ranar alhamis aka yi kamu a gidan Aunty Zulai, babu wasu 'yammata sai yaran dangi sai kuma kawayen su Hadiza da A'ilo.

Ita dai bata um bata um-um sai bin mutanen bikin da take yi da ido, wani irin ciwo take ji a cikin kirjinta ga wani abu mai daci da ya tokare mata makogoro yaqi tafiya da kyar take iya hadiye yawu, dama ace ta samu ta zubar da hawaye watakila ta dan ji dama-dama to amma idanunta a soye suke kyamas babu alamar digon hawaye.

QADDARAR MUTUM Where stories live. Discover now