Kafin karfe goma na safe ta buga har Hasina tayi wanka ta kimtsa ta kuma karya kumallo da kunun gyada da kosai da Aunty Zulai ta ajiye mata tana zaman jiran ji daga Innarta tare da fatan Allah yasa Baba ya hakura ya amince ta cigaba da zama a gidansu don har ga Allah bata son abinda zai rabata da zama wurin Innarta sai dole kamar dai aure to shi kuma sai ya kasance bata yi dace ba don duk inda taje bata taba rufa shekara biyu ba auren yake mutuwa.
Abinda Hasina bata sani ba shine a daren jiya har karfe sha daya Inna ta kai tana zaman jiran shigowar Baban don ta tuntube shi akan batun Hasinar, koda ya shiga dakin nata tayi shiru ne tana jira taji ko zai yi mata magana akan zuwan na Hasina da kuma korar da yayi mata, a so samu ma har ya lallasheta tare da bata hujjarshi akan yanke wannan danyen hukunci.
Sai dai kuma bai yi hakan ba sai ma shirin kwanciya da taga yana yi don haka cikin kwantar da murya tace mishi "ashe Hasina tazo dazu ka hanata shigowa?"
" Eh tazo na kuma koreta sai akayi yaya? Kin ga fa Habi ki kiyayeni, ki fita idona na runtse, gama naga nema kuke yi ku kure hakurina ke da 'yarki, ta yaya za'a ce a kasa da shekara bakwai yarinya tayi aure har hudu kuma babu inda tayi zama cikakke na sama da shekara biyu, don haka ta nemi wajen zama amma ba gidana ba bani da wajen ajiye bazawara inyi dawainiyar kannenta nayi nata".
Duk da cewar taji haushin maganarshi don a ganinta duk wani hali da Hasina take ciki shine sanadi tunda duka mazajen da take aure shi yake kawo su ba tare da ya duba nagarta ko cancanta ba yake daukar auren ya basu ba kuma tare da yaji ra'ayin ita Hasinar ba tana so ko bata so sai kuma idan auren ya mutu ya dauki dukkan laifi ya dora mata a cewarshi ita take yin sanadin da mazan nata suke korota, kara kwantar da murya tayi tace "to amma Mallam ai ka binciketa kaji abinda ya hada su da mijin kafin ka yanke hukunci ba wai daga zuwanta tun baka ji ta bakinta ba kayi mata korar kare".
A hasale ya mike daga kishingidar da yayi don har yana buge babban dan yatsan kafarshi da katakon gado amma bai kula ba saboda masifar dake cinshi duk kuwa da radadin da yatsar take yi mishi "ban tsaya na binciketa ba uwata kinji nace ban binciketa ba akwai abinda zaki iyayi ne?"
Zuwa yanzu ranta ya kai makura a baci don haka cikin bacin rai tace "saboda Allah wacce mace ake yiwa abinda ake yi mini a gidan nan, duk hakurina da kauda kaina akan irin bambancin da kake nunawa a tsakanin yaran nan baka gani, zawarcin nan naga dai ba ita kadai take yi ba tunda yanzu haka akwai zawarawa a cikin gidan amma banga ana yi musu abinda ake yiwa Hasina ba, ban sani ba ko don ita ba 'yar gida bace yasa ake yi mata hakan" ta karashe maganar tana goge kwalla da gefen zaninta.
Duk da jikinshi yayi sanyi da maganarta ta karshe amma bai russuna ba sai ma cewa da yayi "wannan kuma fadar kice ba tawa ba, ni banga wani bambanci da nake nunawa a cikin iyalina ba kuma wallahi idan kika ce zaki na yi mini katsalandan a harkar gidana zamu saka karfar wando daya dake, atoh" har yana tsirto da yawu wajen furta 'atoh' din.
A haka suka kwanta kowa rai babu dadi, don haka da safe ta aiko Bello kanin Hasina wanda yake bin ta da kudin mota tace taje gidan Aunty Hannen don ta riga ta sanar da ita batun zuwanta wajenta ta zauna.
Bayan ta gama shiri tayi sallama da Aunty Zulai tare da yi mata godiya ta fita dama kuma bata fito da komai ba daga gidan Sagir sai kayan jikinta kawai.
Har bakin titi Bello ya rakata don bai tafi ba har sai da ya tsayar mata da a daidaita sahu ya kuma ga tafiyarsu kafin ya juya.
A wajen gate din gidan ta sauka, bayan ta biya mai a daidaitan kudinshi ta karasa jikin gate din ta kwankwasa, jim kadan bayan kwankwasawar tata Mallam Adamu maigadin su Aunty ya leko ta 'yar kofar dake jikin gate din don ganin waye.
Yana ganin ita ce ya bude karamar kofar gate din yana washe baki yace "a'a Hasina yau kece a gidan namu? Sannu da zuwa".
Itama cikin fara'ar data kirkiro tace " eh nice Baba Adamu, ina yini, Auntyn dai tana nan ko?" Yace mata " eh" don haka ta wuce zuwa cikin gidan.
Ta kofar baya wato kofar kitchen ta shiga gidan, ai kuwa dai Auntyn ma na kitchen din tana aikin abincin rana.
Da murnarta ta tari Hasina tana cewa "Yanzu dama nake tunaninki cikin raina nace ko kin fasa zuwa ne?".
"Ban fasa ba Aunty, kin san halin Baba ai tunda yace bazan zauna a gidanshi ba ni nasan babu abinda zai saka shi canja ra'ayinshi. Ban san me nayi mishi ba ya tsaneni, duk rayuwata nayi ta wajen kokarin ganin na kyautata mishi amma baya gani, tunda na taso bai taba bani 'yancina ba a komai alhalin ba haka naga yana yiwa sauran 'ya'yanshi ba" ta karashe maganar cikin kuka.
Sai da tayi kukanta ma'ishi ba tare da Aunty Hanne ta rarrasheta ba sannan ta hakura tayi shiru.
"Sai ki wanke fuskarki ki tafi daki ki kwanta ki huta, babu wani abu bako a cikin halin Babanku da baki sani ba, hakurin nan dai da kika saba shi zaki cigaba dayi har Allah ya ganar dashi gaskiya ya fahimci cewa ke din amana ce a wajenshi".
Dakin Aunty Hanne ta shiga ta kwanta sai dai ba bacci take yi ba sai tunanin rayuwarta dake ta kawo mata farmaki tana faman yaki dashi.
Hannu ta kai ta shafa cikinta dan wata hudu daya soma turo riga ya tasa, cikin da shine sanadin tonuwar asirinsu a wajen Baraka har tace ta gaji da auren nata haka nan tayi wa Sagir umarnin ya datse igiyar auren dake tsakaninsu duk da alkawarin da yayi mata na cewa zai tsaya tsayin daka yaga ya bawa auren nasu kariya ya rike igiyoyinshi gam ba tare da ya bari barazanar uwargidan nashi ta raba su ba.
UMMASGHAR.
YOU ARE READING
QADDARAR MUTUM
RomanceRayuwar MUTUM tana tafiya ne a bisa bigire na QADDARA haka nan kuma bawa bai isa ya kauce mata ba. Shi yasa ma yarda da ita yake daga cikin shika-shikai na imani. Ku biyo ni cikin labarin Hasina don jin tarin qaddarori da ke bibiye da rayuwarta.