BABI NA GOMA

99 9 0
                                    

Da sassafe suka tashi da baƙuncin Mallam Basiru shi da mahaifin Usman Mallam Tukur. A lokacin ta shirya zata tafi makaranta don har sun gama sallama da Usman tana ɗaure igiyar takalminta taji hargowar Mallam Basiru daga soron gidan.

A take gabanta yayi wata irin mummunar faɗuwa don tasan tabbas babu alkhairi a cikin zuwan shi gidanta bare kuma da tasan abinda ke akwai.

Da mamaki Usman ya fito daga ɗakin yana cewa "kamar muryar Baba nake ji yanzu da sassafe haka, to Allah yasa dai lafiya".

"Uhum" kawai ta iya cewa don gaba ɗaya bakinta yayi nauyi bata jin akwai kalmar da zata iya fita daga cikin shi.

Hanyar fita Usman ya dosa don ya tabbatar idan kunnuwan shi daidai suka jiye mishi muryar Mallam Basiru ce yake ji.

Ga mamakin shi tare ya iske su da Babanshi kowanne fuskar nan a ɗaure tamau alamun rayukan su a ɓace suke matuƙa. Cikin sanyin jiki ya russuna yana cewa "Baba sannun ku da zuwa, barka da asuba".

A daƙile Mallam Tukur ya amsa shi da "barkanmu dai" don shi Mallam Basiru baqin ciki bai bar shi ya iya amsawa ba sai cewa da yayi "ina wannan almurar take wajenta muka zo ta faɗa mana abinda ta tura waccan gantalalliyar matar ta faɗa mini".

Duk da cewa ya san ba wata kyakkyawar alaqa bace a tsakanin Hasina da Mallam Basiru yayi mamakin jin furucin dake fita daga bakin shi. Komawa yayi cikin gidan ya kira Hasinar.

Tana ganin shi ta ƙara tsurewa don daga nan inda take tana jin duk abinda Mallam Basiru yake cewa, a take taji cikinta ya murɗa ya bada sautin ƙulululu da ƙarfi.

Ganin yadda ta firgice yasa shi fahimtar lallai ba zata kasa sanin maƙasudin wannan sakko na mahaifin shi da aminin na shi ba.

"Ki fito suna jiranki" kawai ya iya ce mata ya juya duk da yaso ya tsaya ya ɗan rarrashe ta tare da kwantar mata da hankali ganin yadda duk tabi ta firgice to amma iyayen su ne a waje suke jiran su yasan ko giyar wake ya sha bai isa ya bar su suna zaman jiran su ba.

Salalo-salalo haka taja ƙafafu ta bishi a baya, daga bakin ƙofar da ta sada soron da cikin gidan taja ta tsaya.

Wata irin razananniyar tsawa Mallam Basiru ya daka mata har bata san lokacin da ta afka cikin soron ba.

Tana shiga ya ware hannu ya wanka mata mari.

"Wayyo Allah" tace tare da dafe kuncin ta da ya mara ta durƙushe anan wurin tana sakin kuka.

"Subhanallahi, haba Mallam Basiru me zai sa ka daketa saboda Allah, a yanzu Hasina ai ta wuce asa hannu a daketa don tayi laifi" inji Mallam Tukur.

Cikin tsananin fushi yace "rabu da ni Mallam Tukur rabu da ni, wai ace har wannan yarinyar tasan ta ƙulla magana ta turo mini ƙanwar uwarta taje zata yi mini rashin kunya wai ita dama tasan ba banza ba na aura mata Usman ashe don nasan bashi da lafiya ne, don ubanki a gidan uwarki ya gamu da lalurar, idan banda lalacewa ma 'yar ƙaramar ki dake me kika sani da har zaki san wai miji bashi da lafiya".

Gyara tsayuwar shi Mallam Tukur yayi yace "don Allah Mallam Basiru ka nutsu muyi magana cikin lumana, wannan iface-ifacen da kake yi fa ba shi zai sa mu san abinda muke son sani ba illa ma ƙara jagila al'amarin da zaka yi".

Ita dai tana son tace ita bata ce Usman baya da lafiya ba tunda ma ai kullum sai ya fita kasuwa marar lafiya kuwa ai ba zai iya wannan jelen yawon ba ta dai yi shiru ne saboda tsoron Mallam Basiru, tasan kaɗan da aikin shi ya rufe ta da duka yanzun nan.

Gaban Usman sai da ya faɗi jin abinda Mallam Basiru yace. Kallon shi Mallam Tukur yayi da fuskar tausayi yace "meye gaskiyar maganar da muka wayi gari da ita yau Usman? Shin da gaske ne wai baka da lafiya kamar yadda qanwar mahaifiyar Hasina tace?"

Shiru yayi kan shi a ƙasa ya rasa wacce irin amsa zai bawa mahaifin na shi, shin zai fito fili ne ya faɗa mishi abinda yake boyewa tuntuni ko kuwa zai musanta yace sharri suka yi mishi, to amma idan an tambayi dalilin da yasa baya sauke hakkin aure dake kan shi me zai ce.

"Kayi shiru Usman, don Allah kace mini wannan maganar cin ƙanzon kurege ce, ba da gaske ba ne hasashen da suke yi" yayi maganar muryar shi na rawa, hankalin shi idan yayi dubu ya tashi don tunda Mallam Basiru yaje ya faɗa mishi abinda kenan yasan zai yi matuƙar wahala idan har sharri aka yi mishi sai dai yaso ko yaya ne Usman ɗin ya musa zargin da ake yi mishi ko ya samu nutsuwa cikin zuciyar shi.

Da ƙyar Usman ya iya buɗe baki yayi magana bayan da mahaifin shi ya dage da son jin ta bakin shi yace "eh Baba amma ina kan neman magani har yau kuma ban zauna ba duk inda naji mai magani zuwa nake yi ko Allah zai sa a dace".

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" kawai Mallam Tukur ke nanatawa, inda Allah ya taƙaita ma a jingine yake a jikin bango da wataƙila sai ya kai ga faɗuwa don sosai amsar ta Usman ta kaɗa mishi ciki duk kuwa da cewa dama abinda ya tsammaci ji kenan.

Ya daɗe yana maida numfashi kafin ya iya cewa "amma shine kayi shiru baka taɓa faɗawa wani ba Usman sai kai kaɗai kake ta faɗi tashin neman maganin ka kamar wanda baya da gata, to ko ba zamu magance maka komai ba ai ka faɗa mana ko don ka samu wanda zaku raba damuwar ka da shi. Don Allah Mallam Basiru kayi haƙuri wallahi ban taɓa sanin wannan maganar ba sai ɗazu da kazo mini da ita, ai kana ma dai ji da kunnen ka tunda gashi nan a gabanka ya amsa da bakin shi ba tursasa mishi aka yi ba, sai dai wannan ba dalili ba ne da zai sa a raba aure ina ganin ka bamu lokaci mu nemi magani tukunna In Sha Allahu ina ganin za a dace ko dama can don bai taɓa sanar damu ba ne da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba".

Tsaki Mallam Basiru yayi yace "don Allah kada ka ɓata mini rai Mallam Tukur, yanzu wannan har wani dalili ne da zai saka a raba aure saboda Allah, idan ma banda lalacewar zamani har nawa Hasina take da zata san wani abu kwanciyar aure bare har ta damu don bata samu ba banda dai ita ba matar rufin asiri ba ce da har ta iya fallasa irin wannan magana ai da ko ji ma baza mu yi ba. Kuma ki ɗago kai ki kalleni da kyau ni Basiru nace idan ma wasu ke zuga ki to kai ki za suyi su baro ki domin kuwa idan har kika yi nasarar kashe auren ki sai dai ki nemi gidan wani uban amma ba nawa ba, mutuniyar banza mutuniyar wofi wacce bata san halacci ba".

Anan suka tafi suka bar su Hasina tana faman kuka don ita har suka yi maganganun su suka gama bata fahimci inda zancen ya dosa ba duk da taso ta fahimci maganar da suka yi jiya ita da Aunty Hanne ce ta janyo wannan ba in ran.

Da ƙyar ta iya jan jiki ta koma cikin gidan ta bar Usman tsugune a soron ya kasa motsawa ko nan da can don gaba ɗaya jikin shi ne yaji ya saki, shi a yadda yake ganin Hasina bai ɗauka tayi wayon fahimtar halin da yake ciki ba da har zata je ta faɗawa wani sai gashi ta shayar da shi mamaki don kuwa bai taɓa tsammatar fallasuwar maganar nan da wurwuri haka ba.

Yafi minti ashirin a tsugunnen kafin ya iya jajircewa ya miƙe ya koma cikin gidan. Tana zaune akan doguwar kujera a parlour ya iske ta har ta cire uniform din ta ɗaura zani da rigar leshi don a yau dai babu batun zuwa makaranta don tuni lokaci ya ƙure tayi latti, kallo ɗaya yayi mata yasa kai ya shige uwar ɗakan ya kwanta akan gadon kwanciyar rigingine yana kallon rufin ɗakin, ji yake yi gaba ɗaya duniyar tayi mishi zafi ya rasa inda zai sa ranshi yaji daɗi.

Ya daɗe kwance a wurin yana tufka da warwara ya rasa ta yadda zai  ɓullowa wannan al'amarin duk kuwa da cewa yasan yanzu da mahaifin shi ya sani sai inda ƙarfin shi ya ƙare wajen yi mishi maganin damuwar shi.

Sai yanzu yaji haushin kan shi ya kama shi da tun wuri ya sanar da Baban ashe da tuni larurar shi ta zama tarihi sai dai ayi wani zancen ba wannan ba.



UMMASGHAR.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 30, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

QADDARAR MUTUM Where stories live. Discover now