*KUKAN ZUCI....*💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)*NA:SLIMZY✍🏻*
Watpadd@slimzy33*3*
"GA dakin nan ranka ya dade "ta Nuna masa da hannu ta juya har takai wajen matakala ta waigo Yana tsaye,girgiza Kai tayi ko me zaijeyi dakin mammy oho?suruki da Shiga dakin suruka inba a birni ba a inane suruki zai Shiga har uwar dakin suruka saboda rashin kunya?harta sauka bene tana Mita,daga Kai tayi ta dubi dakin afee dake kulle ta girgiza Kai,
Idonta na lumshe kamshin turaresa ya bugi hancinta da sauri ta bude Ido gabanta ne ya Fadi ganin sadiku a dakin baccinta,mikewa tayi da sauri tana binsa da kallo cike da tambayoyi hade da waige waige,
Harde hannuwansa yayi a kirjinsa yana karewa mammy kallo,shekarunta sunja Amma tamkar yarinya yar shekara ashirun da uku idan ba kwayar idonta Ka kalla ba Sam bazakace babba bace,wani kallo yake bin ta dashi,itama samun kanta tayi da kallonsa take wani Abu ya tsarga Mata cikin jikinta wani maganadisu ke yawo a jinin jikinta tamkar shocking,runtse idonta tayi dakyar ta motsa harshenta da yayi Mata nauyi "Ka shigo mana ya Ka tsaya a kofa?a matsayinka na d'ana kuma sirikina?"
Gyada Kai tayi ya saki murmushi ya shigo yaja kujerar dake gefen makeken gadonta ya zauna ya zura Mata idanuwa,
Samun kanta tayi da daga masa Gira Daya "ya dai nayi maka kyau ne kake kallo na d'an mammy?"tace cikin zolaya dikda wani shauki da takeji a wanan lokacin,
"Sosai kinyimun kyau mammyn mu hakan yasa nakasa dauke ganina daga gareki domin ba karamin saa Abbah yayi ba samun mace kyakkyawa wadda Bata tsufa kamarki na tabbatar abbah naji dake shiyasa ya damkamun amanarku a hannuna"yace Yana cigaba da watsa Mata wani irin kallo Wanda hakan ba karamin kasala ya haifar Mata ba,wani irin dadi kalamansa sukai Mata tabbas ya iya kalamai dole Yarta afee ta zauce Akan soyayyarsa uwa uba GA kyau da zati Wanda ba kowani namiji Allah ke bawa ba,inama ace Abbah yanaji da ita Yana kulawa da ita kamar yadda sadik ke Mata tattausan lafazi babu soyayya ko kalami Mai dadi tsakaninsu to kwanciyar aure ma rabonsu da ita yau wata shida Kenan dik ko da irin magungunan Mata da take tsuma kanta Amma a banza saidai yabi iska,
Idanuwanta sukai jajir ta dubi sadiku ta karabin halittarsa da kallo ji takeyi inama ace Abban afee ne da wanan halittar kuma Yana Kula da ita?da tabbas batada wajen Daya wuce faffadan kirjinsa tabbas sadiku namiji ne na kerewa saa.....runtse idonta tayi tunawa da soyayyar da yarta Daya tilo wadda takejin Zata iya mallaka Mata Komi a duniya Shi takeso gashi tanajin wani yanayi game dashi,"Kaga afee kuwa?tana dakinta ina ganin"
"Ba ita nazo ganiba ke nazo gani mammy saboda muryarki da kallon da kikemun dazun ya bayyana mun damuwar da kike ciki"
Inama ace kasan menakeji game dakai?da kayi gaggawar nisanta kanka daga gareni....murmushi ta kakalo ta kauda maganar "banida wata damuwa data wuce kewar mijina wato Abbanku inajin kewarsa sosai"
Murmushi yayi kawai ya girgiza Kai Mai zai Hana in debe Miki kewarsa da hirarraki da labarai masu dadi?"
Murmushi tayi yaro Kenan Basu nake bukata ba, ganinka kadai inajin wani nishadi a tare Dani tun daga ranan Dana Fara ganinka,
Mikewa tayi "to muje parlor ko?"bata Jira cewarsa ba ta Mike tayi gaba yabita da kallo numfashinsa kamar zai dauke,daskarewa yayi a wajen zamansa....
Kuka sosai afee takeyi idanuwanta sunyi jajir tana makale da waya Wanda tun fitowarta wanka take waya da aminiyarta "ummah wallahi akwai matsala kawai dai kinaso ki kwantar mun da hankaline Amma tabbas sadiku da wata yakeyin wayar nan wallahi ji nakeyi kamar Zan kashe kaina saboda tsananin kishi,ko kinsan har yanzun be kirani ba tunda ya Gama wayar ko yanzun na kirasa da dayar wayata dake gefena still Bai dauka ba"
YOU ARE READING
KUKAN ZUCI...
General Fictionlabari Mai cike da soyayya hade da sarkakiya labari ne Mai matukar karya zuciya kuma labari ne Akan matsalolin dake faruwa