*KUKAN ZUCI....*💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)*NA:SLIMZY✍🏻*
Watpadd@slimzy33*2*
Zaune suke Duka a dining suna breakfast juya cokali kawai mammy takeyi Anya hukuncin da alhaji ya dauka Akan yaron nan daidai ne?tayaya bakayi bincike Akan mutum ba kadau yarda Ka bashi sanan kusancinsu da yaron nan bazai haddasa matsala ba kuwa nan gaba?afee ce ta dubeta "mammy ina kallonki tun dazun bakici Komi ba juya spoon kawai kikeyi mamy why?"
"Bakomi yar mammy auta shalele kawai dai banajin dadin jikina sanan banajin Zan ma iya breakfast din nan"kawai saita janye ta Mike tana Shirin tafiya ya shigo da sallamarsa shadda ce Fara sol a jikinsa sai kamshin turare yakeyi zubewa yayi a Kasa "barkanku da safiya abbah"
"Mashaaaa allah sadik shine bakaje office Ka jirani ba?Ka biyo ta gida?"
Shafa keyarsa yayi Yana Dan murmushi,afee kuwa idonta na kansa ko kiftawa batayi wani dadi ne ya mamayeta hade da shaukin soyayyarsa dake ratsa jijiyoyin jinin jikinta....wani Abu ne yake tsargawa a kwanyar kanta hakika sadik Bai taba Mata kyau kamar yau ba,
Shiko dago Kai yayi Yana satar kallon mammy dake tsaye tun daga Sama har Kasa yake Mata kallon Kasa Kasa,lumshe idonsa yayi domin yanajin wani sabon yanayi a jikinsa kamar yadda bacci ya gagara daukarsa,"Yauwa sadik kuje Sama hajiya ta Baka makullin mota da wasu takaddu dake gefen gado Ka kawomin Kasa Dan inajin kiwar hawa Saman"
Gaban mammy ya Fadi tayi Maza ta kalli abbah da ya maida hankalinsa GA afee da yake tsokanarta suna dariya wace irin yarda ce haka jiya jiya zai aiki yaro bedroom dinsa? kuma tare da ita?bayan ga afee nan a zaune?
Gaba sadik yayi domin haka yakeso ya soma taka matakala ya tsaya alamar Yana jiranta saboda rashin sanin Kan gidan,
"Alhaji Amma kana ganin ya dace Ka aiki sadiku dakin baccinka dakin baccinmu ma zance?wani irin abune haka?wani irin yadda kayi dashi haka Baka gudun wani mummunan alamari?"
"Haba hajiya ki rinka kyautata zato wanan yaron Dan cikina nadaukesa kamar yadda na dauki afee saboda haka kema ki daukesa haka kuma ki rinka kyautata zato Dan haka babu abinda zai faru yi sauri kibashi saiki kwanta tunda kince bakijin dadi zanyi Miki transfer din dubu Dari biyar kafin indawo ina sauri zamuje office in gabatar dashi Shi zai kaini airport"
Girgiza Kai kawai tayi ta cije lebe Sam hakan beyi ba toya zatayi?meyasa batason kebewa dashi samm jiya data rufe idonta zati irin nasa take gani hade da wata matsananciyar damuwa,haka ta juya tayi gaba Yana binta a Baya yadda take taku tana sarrafa jikinta ba karamin saukar masa da kasala hakan yayi ba,
Duban afee abbah yayi "mekikace kinaso afee?kikace kinaso a siyawa sadiku mota da kayan Sawa?"
"Ehh abbah saboda iyayensa Basu kaimu karfi ba abbah kuma inasonsa sosai ni abbah wallahi da zai dawo gidan nan ma inaso saboda in rinka ganinsa kullum"ta karasa maganar tana rufe Ido,
Dariya abbah ya kyalkyale dashi Yana girgiza Kai message ne ya shigo wayarsa cikin sauri ya duba,
*Cikin minti biyar ina bukatar kudi Million goma da mukayi dakai idan ba haka ba Zan fallasa sirrinka kuma Zan rabaka da wanan yarinyar data kasance farin cikinki,idan mintunan Dana Baka Suka cika Baka turoba zanzo in dauketa in rabaka da ita harabada*...
Gumi ne ya tsattsafowa abbah cikin sauri ya Shiga Mobile app idonsa ya rufe gumi kawai yakeyi yayi pesting account number ya tura kudin,yasa Hankici ya goge gumi,ita kuwa idonta na kansa,.....
Mika masa takardun tayi tana murmushi samun kanta tayi dayi masa wani kallo Wanda ita kanta batasan tayi ba yanajin Ake tsigar jikinsa ta tashi hannunsa na rawa ya karbi takardun ya juya har yakai kofa ta tsaidashi "saurin me kakeyi haka?"
ESTÁS LEYENDO
KUKAN ZUCI...
Ficción Generallabari Mai cike da soyayya hade da sarkakiya labari ne Mai matukar karya zuciya kuma labari ne Akan matsalolin dake faruwa