7

26 2 1
                                    

*KUKAN ZUCI....*💔

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)

        *NA:SLIMZY✍🏻*
      Watpadd@slimzy33

                        *7*
Mamaki sosai haidar keyi ganin motarsu afee ta doshi makarantar su sabreen tabbas makarantar su Daya da sabreen murmushi yayi Allah yasa dai Kar su hadu da sabreen a tare motocinsu suka Shiga cikin makarantar Maza da Mata kowa sai harkarsa yakeyi......

Daga bayan motarsa ya tsinkayi wata murya "laaa sabreen kamar ya haidar din gidanku ko?wallahi shine motarsa ce"

Da sauri sabreen ta kalli Inda kawarta ke Nuna Mata "tabbas shine yanzun fa nabarosa a gida zai tafi wajen aiki kuma kinsan me wallahi inajinsa Yana fadawa Anty wai yayi budurwa"

"Tou kodai budurwar tasa a nan makarantar take?aiko idan anan take Zata gane kurenta"sukace a tare suka kafe Inda yayi parking da Ido,

Fitowa yayi ya harde hannuwansa a kirjinsa Yana kallonta ta cikin glass sun dauki minti goma sanan suka fito a tare dammmm gabanta ya Fadi hada Ido da tayi dashi innahlillahi wa innahilaihi rajiun kardai dazun aljani tayi gamo dashi gashi a gabanta,a tsorace ta matsa Baya kadan tana kallonsa murmushi yayi Mata ya Ciro waya a aljihunsa ya Mika Mata "samun number wayarki da adreshinki"yace Mata cike da isa da iko,

Kasa masa musu tayi ta Mika hannu Zata karba taji an wabce wayar da sauri ta juya sabreen ke tsaye tana numfarfashi suna kallon kallo ita da ita,mamaki sosai ummah tayi kawar afee tana bin sabreen da kallo tana kallon afee tabbas suna kama da juna banbancinsu kawai sabreen Baka ce afee kuma Fara ce sanan afee doguwar fuska gareta kuma waccen siririya ce,

Kawar sabreen Kasa hakuri tayi tace "tabdijan kawata kinga yadda kukayi kama da kishiyar taki kuwa?wallahi kuna kama"sai lokacin haidar ya kare musu kallo tabbas suna kama Komi nasu iri Daya ne kamar Yan biyu to tayaya?kodai abinda yakeji Akan afee ya tabbatar da cewar jinin nasa ce?Anya Kai hasashene kawai,

Tsaki ya ja ya Nuna sabreen da yatsa "ke har kin isa?ina Wasa dakene da zakizo ina tare da matata ki wabce wayar Bani tun ban marekiba kuma wallahi zanyi maganinki zakizo gida"ya karbi wayar a hannunta ta juya tana kunkuni tana hararar afee wani irin kishinta takeji haka kawai taji tsanarta ta darsu a zuciyarta dama can ta tsaneta yadda Ake Mata kirari ubanta Mai kudi tayi tsaki,

Afee kuwa tsaye take kamar mutum mutumi tunani takeyi Kala kala tabi sabreen da kallo,ummah ce ta zungureta "me kike tunani inzaki bashi number kibashi kinga mun kusa Shiga lectures"furgita tayi ta juyo ya kafeta da Ido kamar maye meyasa yake Mata kwarjini?meyasa dik abinda yasata takeyi tsaki tayi a zucuyarta cikin bacin Rai ta karbi wayar tasa masa tayi gaba abinta ya harde hannu Yana kallonta,

Tabbas afee ce waccen tsaye da wani budurwar sadik ce fa?jinjina Kai yayi Yana daga gefe Yana kallonsu....

Mota haidar ya Shiga ya tada samm bashida natsuwa soyayyarta takara mamayesa musamman natsuwarta da hankalinta Inda wata ce yadda sabreen tayi Mata ba karamin rikici zasuyiba saita Kara Burgesa ya shafe sajen bakinsa yayi murmushi Ammy ce ta Fado masa ya nufi hanyar office....

*******
Shiru cikin parlorn sadik ya shigo sai TV dake Kara ko baa fada masa ba yasan tana dakinta sanan afee tayi masa Tex ta tafi makaranta....Ransa yadan sosu saidai gabansa dake faduwa sosai haka ya waiga kamar mara gaskiya babu kowa ya nufi Sama zuciyarsa na darrr darrr

Karar Bude kofar dakin ya tabbatarwa da mammy ya iso hakan ya bata Damar saukar da numfashi tana nishi a hankali Sama Sama sautun nishinta tasa tsigar jikinsa tashi wani irin tsoro ya cikasa ya Shiga waige waige can ya hangeta lullube cikin bargo tun daga kanta, Subhanallahi yace jikin yayi tsanani haka? gabansa na faduwa ya karaso gaban gadon ta dik abinda yakeyi tana kallonsa ta cikin lullubi haka ya karaso ya zauna gefen gadon ya Kai hannu zai yaye bargon yayi saurin kasawa gabansa na faduwa wani irin nishi tayi Wanda ya tsorata ta da sauri yasa hannu ya yaye bargon idonta a rufe yake gumi ya jikata yakai idonsa jikinta towel ne a daure Dan karami cinyoyinta sada sada farare Tass yabi da kallo take jikinsa yayi tsamm numfashi take saukewa "sannu mammy sannu mammy abbah ya turoni muje asibiti "

KUKAN ZUCI...Where stories live. Discover now