6

34 5 2
                                    

*KUKAN ZUCI....*💔

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)

        *NA:SLIMZY✍🏻*
      Watpadd@slimzy33

                        *6*
Share hawaye mammy tayi ta kakalo murmushi ta shafa gefen fuskar afee cike da kaunar yartata tace "bakomi afee babu abinda yake damuna kawai ina kewar abbanki ne gashi yau antynki tazo nemansa ta zazzagamun halin"kallonta kawai afee keyi badan ta yarda da abinda mammy ke fada Mata ba Sam bataga gaskiyar zancen a kwayar idonta ba ai mammy bata zubarda hawaye Akan ummah Zainab saidai kawai tace Inda sabo ta Saba dole akwai wani Abu dake damunta,

"Mammy kiyi hakuri kifadamun matsalarki nice yarki Daya tilo dik duniyar nan bakida kowa saini sai abbah na kifadamun inyi Miki maganin damuwarki",

Wani sabon kuka ne ya kwancewa mammy Jin furucin da afee tayi ta rungume yartata yanzun shikenan saita fadawa afee cewar saurayinta takeso take shaawarsa? subhanallahi ta fashe da kuka wace irin mummunar jarabawa ke Shirin faruwa a rayuwarta?Yarta Daya tilo ta yaya zataji idan ta fahimci HK?dago Kai afee tayi ta fashe da kuka "mammy inhar Baki fadamun ba bazansamu sukuni ba zuciyata Zata wuni da tsananin kunci karki manta fa ke mahaifiyata ce Bana boye Miki Komi meyasa ke zaki boyemun?"hawaye ke zuba a idon mammy tausayin afee ya kamata ta sake kallonta Ido cikin Ido take taji gabanta ya Fadi Wanda batasan dalili ba "afee Zan fada miki amma ba yanzun ba nayi Miki alkawari nan gaba kadan Amma Zan daina kuka kinji?karkimun gaddama kuma"

Gyada Mata Kai afee tayi ta sharewa mammy hawaye sanan ta kwantar da kanta jikinta "mammy kinsan me?"

"Ah ah saikin fada yar mammy"

",Hmmm wani Dan rainin wayau na hadu dashi sunansa haidar wai sai cewa yayi wai Shi jinina ne"dariya mammy tayi "to me kikace masa?"

"Banko ce masa komiba banza dashi nayi...."zatai magana Kiran sadik ya shigo wayarta tayi saurin dubawa "la mammy na mance sadik na jirana zai tafi aiki"ta Mike da sauri ta dira daga Kan gadon ta fito Bata gansa a parlorn ba a mota tasameshi ya kifa Kai da sitiyarin mota tunanin mammy kawai yakeyi ta bude motar ta Shiga yayi furgigit.....

*******
  Haidar kuwa a parlor ya samu Ammy tana zaune kamar koda yaushe ta Lula duniyar tunani sallamarsa ce ta katse ta,
"Ammy kina nan kina tunani ko?haba Ammy Ba likita yace kidaina tunanin da kikeyi ba hakan zai hafarwa da lafiyarki matsala?"

"Ba tunani nakeyi ba saidai ina kukan zuci haidar kullum ina tunanin Yata daya tilo Dana Haifa da ranta likita yace ta mutu kuma gawar yar da aka bamu ba ita bace yar Dana Haifa haidar na Haifa maka Mata Amma an halaka ta,gashi inaso kayi aure"

Murmushi yayi ya kamo hannunta "Ammy albishirinki na samo Miki suruka yau fitar nan da nayi da safen nan nahadu da ita"

Da sauri Ammy ta kallesa cike da murna da farin ciki "a ina take?yar wacece a garin nan?haidar naso ace yar Dana Haifa a cikina itace matar taka,saidai nasan ko nan gaba Zata dawo kuma Zan aura maka ita a ta biyu"dariya kawai yayi domin Abubuwan Ammy kamar wata wadda tasamu matsalar kwakwalwa yau shekara sha takwas Kenan har yau bata hakura ba,

"Tou naji Zan aureta Ammy Amma yanzun zanfara auren wanan saidai bansan yar waye ba bansan a ina takeba saidai tafadamun sunanta ummulkhairi"

Kafesa da Ido Ammy tayi tana saurarensa "ta yaya zakasan gidan nasu?bayan Baka tambayi address ba?"

"Wanan ba matsala bace na tabbatar zan sake haduwa da ita Ammy Komi daren dadewa inada number motarsu akaina"

Murmushi kawai Ammy tayi ta kalli jikin labule tabbas taga inuwa alamar ana musu labe da sauri aka juya sai kawai tayi dariya "tashi kaje kayi Shirin aiki"

KUKAN ZUCI...Where stories live. Discover now