*KUKAN ZUCI....*💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)*NA:SLIMZY✍🏻*
Watpadd@slimzy33*4*
Tare suka jera suka fito itada sadik wani kallo sukeyiwa juna Mai cike da so da kauna kallo Daya zakayi musu kasan cewar sun matukar dacewa da juna Shi kansa yanason afee Amma akwai wani Abu dayake damun zuciyarsa daga jiya zuwa yau Wanda baisan ko menene shi ba,Tsaye mamy tayi a balcony tana hangensu murmushi tayi tana kallon yartata yadda take cikin nishadi kaida Ka kallesu kasan suna cikin farin ciki,girgiza Kai tayi Jin wani Abu ya taso Mata a kirjinta ya tokare ta idanuwantane suka kawo ruwa,taso ta Kara magana dashi saidai alamu sun Nuna tafiya zaiyi baiko dawo yayi sallama da ita ba,juyawa tayi ta koma ciki,
"Bansamu nayi sallama da mammy ba Ruhina?"yace Yana kallonta,
"Laaa hakane tabbas mammy zatayi fushi katafi bakayi Mata sallama ba Amma kayimun alkawarin zaka dawo fa daddare ko?"ta shagwabe fuska yabi pink lips dinta da kallo yasa hannu yadanja "I love dis pink lips"murmushi tayi tanajin wani Abu na yawo a jikinta "ni inason Komi naka Ruhina Dan Allah kadawo inaso muyi hira please?"
"Zan dawo kinji dole ma indawo Kodan inbawa mammy hakuri natafi yanzun banyi muku sallama ba"
Gyada masa Kai tayi ya Shiga mota tabisa da kallo har Mai gadi ya bude masa gate ya fice.....a harabar wajen gidan kuwa mamakine ya kashe sadin ganin jamian tsaro ta ko INA sun zagaye cikin layin ko wanne da bindiga a hannunsa kome yake faruwa oho kawai yasa Kai ya figi motar a guje yabar unguwar.....
Cinyar mamy tayiwa kanta masauki ta kwantar da kanta a jikinta "mammy ina sonki fiye da Komi a rayuwata kefa abbah dagaku sai sadik"
Murmushi mammy tayi tanajin son Yarta cikin zuciyarta tanajin Anya zanta iya rayuwa batare da afee ba kuwa "afee AI son da mahaifiya keyiwa Yarta ya wuce dik tunaninki naki kikasani ko kin mance jinina ke yawo a cikin jikinki?""Mammy nasani ina sonki sosai Amma abbah na Yana Sona sosai kuma kema Yana sonki"cije lebe mammy tayi wani takaici da taji Kiran sunan abbah da tayi "yana sonki yanayi Miki dik abinda kikeso Amma tunda na haifeki be taba Zama Damu na cikakken sati Daya ba"
Dagowa afee tayi daga kwanciyar da tayi jikin mammy tana kallon kwayar idon mammy yadda Suka cicciko da kwalla "haba mammy kome abbah keyi yanayi ne Dan saboda mu ki daina fadin haka banajin dadi ko Kada"shafa Kan yartata tayi tasani afee nasonta Amma batason laifin abbanta,
Sallamar ummulkurtum ce ta katse musu maganarsu tsaye tayi Bakin kofa tana kallon afee tana harararta "uwar shagwaba dama nasan a cinyar mammy Zan taddaki kin Gama koke koken naki?dik kin dagamun hankali ummahna tace inzo insameki Dan tanajin wayar da mukeyi"
Dariya mammy tayi "au ummah dama kuka afee keyi bansaniba meyasata kuka?"
Zama ummah tayi tana harararta tace "mammy kuka takeyi saboda sadik takirashi call waiting shine take zargin da budurwarsa yake waya ko kuma watace ta kirasa"ummah ta kwashewa mammy yadda sukayi a waya,
Take mammy taji babu dadi tabbas lokacin sadik da ita yake waya sanan yaki katse wayarta ya dauki ta Afnan?meyasa zai batawa Yarta Daya tilo Rai?wani iri taji mikewa tayi kawai tace "Ku kuka sani Ku karata can kunga tafiyata"ta fice tana murmushin karfin Hali nan ta barsu sunata hira.....
********
Washe gari.....
Saddik dakyar ya iya baccin kirki saboda tunani dayake damunsa waishin me mammy take nufi wani irin kallo ne takeyi masa ranan Daya Fara zuwa gidan?sanan jiya gabaki Daya kallo Daya zakayi Mata kasan bata cikin natsuwarta Anya kuwa?soyayyar afee ke dawainiya da zuciyarsa Amma ganin farko da yayiwa mahaifiyarta da irin kallon da take masa ya rudasa gashi kwana yayi a zaune,
YOU ARE READING
KUKAN ZUCI...
General Fictionlabari Mai cike da soyayya hade da sarkakiya labari ne Mai matukar karya zuciya kuma labari ne Akan matsalolin dake faruwa