*KUKAN ZUCI....*💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)*NA:SLIMZY✍🏻*
Watpadd@slimzy33*8*
Kallon Ammy yayi cikin damuwa yace "Ammy meyasa kika kashe wayar?naji kamar tana magana Amma Baki amsata ba Ammy"
"Haidar kayi hakuri yarinyar nan tanayin magana na tsunci kaina cikin faduwar gaba inajin wani Abu na tsargamun cikin jinina ji nakeyi tamkar yar Dana Haifa nake magana da ita,muryarta tayimun kama data sabreen"
Murmushi haidar yayi hade da Jin dadi yace "AI yarki ce tunda surukarki ce ummulkhairi kinga kuwa Zata Zama yarki nan bada dadewa ba saboda Zan aurota inkawota cikin gidan nan ta zauna tare dake ta dauke Miki kewar Komi"
Hawaye ta share "haidar ta yaya zanga wanan yarinyar?inaso inganta Ka kawomin ita inganta kaji?"tace tana kallon kwayar idonsa,
Gumi ya share tabdijan ta yaya yarinyar da ko daidaitawa Basu Gama ba Ammy ta bukaci ya kawota gidan?a gaskiya bazai kawota ba Amma zaiyi Mata dabara,Dan haka ya ruko hannunta "Zan kawo Miki ita Ammy ki kwantar da hankalinki zatazo ta gaisheki"Wani dadi ne ya lullubeta ta rungumesa ji kawai sukayi an hankado kofa an shigo da sauri Ammy ta juya ganin mahaifiyar sabreen kuma kishiyarta yasata murmushi "ah ah yaayah kece haka?meyake faruwa?"
"Komi ma na Shirin faruwa tunda kina Shirin kulla munafunci tunda yarki batazo da raiba dole ki Hana haidar neman auren sabreen to Bari kiji haidar bashida wata matar data wuce sabreen ita zai aura Dan haka yau Zan sanarwa da alhaji ayi Komi a Gama"
Yar dariya kawai Ammy tayi "haba yaayah idan kuma Shi bashida raayinta fa?haidar bashida raayinta ko kadan yasamu matar da zai aura"
"Karyarsa Tasha karya ko Ince karyarku gabaki Daya saboda bakida yar da zai aura shiyasa kika cusa Mai raayin neman wata daban to bazata sabuba wankan kuturu da sabulu yau Zan sanarwa alhaji"taja dogon tsaki ta fita,
Idon haidar yayi ja ya dubi Ammy "kinajin abinda take fada ko?Tou wallahi bazan aureta ba ummulkhairi nakeso kuma ita Zan aura babu Wanda ya isa Dan haka yanzun ma gidansu zantafi"ya mike a fusace Ammy tabi bayansa da kallo ta girgiza Kai cike da damuwa...
********
Tana saukowa daga Sama ya shigo parlorn,wani kallo yabita dashi cike da tsananin kishi kwal kwal tayi kamar zatayi kuka ta sauko ta tsaya a gabansa "Ruhina......nasan kana fushi Dani Amma idan zaka saurareni ba laifina bane Ka tambayi ummah a gabanta akayi Komi wallahi bakomi..tsaka"ya daga Mata hannu idanuwansa jajir "afee look wanan guy din inbaki basa dama ba bazai bibiyeki har makaranta ba nan kikazo kika Bani labarin kanzon kurege Ashe har makarantarku kika fada masa wato ya biki can Kenan ko?"Hawayen data hadiye ne suka zuraro a idanuwanta inama sadik zaiga cikin zuciyarta ya tabbatar da soyayyar da takeyi masa da Bai farfada Mata magana ya zargeta da cin Amana ba"kallonta yayi take tausayinta ya kamashi Amma bazai Nuna Mata hakan da wuri ba Dan Zata sake hakan yasa ya daure fuskarsa yace "ba wajenki nazo ba wajen mammy nazo"ya gifta ta gefenta ta nufi Sama ta bishi da kallo ta share hawayenta....kawai ficewa tayi daga parlorn ta fice harabar gidan tana hawaye....
Kofarta a bude take kawai ji yayi ya Shiga batare da wata fargaba ba Baya ko kallon gabansa ya rufe kofar duhu ne ya kauraye dakin ya Shiga waige waige tana kallonsa tayi murmushi wani dadi ne ya lullube "na kashe wuta ne saboda inajin kunyar hada Ido dakai dikda nasan kaima haka Amma inaso in tabbatar maka da irin dadi da gamsar Dani da kayi hakan yasa nakasa sukuni nake bukatar Kara kasancewa dakai nakawo kokon barata ina fatan bazaka watsamun Kasa a Ido ba"
Ajiyar zuciya sadik ya sauke kalaman mammy sun Shiga jikinsa sosai hakika Shi kansa yanada bukatarta don wuni yayi tariyo abinda ya faru tsakaninsu hakan yasa ya Shiga takowa a hankali murmushi mammy tayi ta Mika hannunta yaji an rukosa rungumeta sosai yayi ajiyar zuciya ta sauke ya hade bakinsu waje Daya.......

YOU ARE READING
KUKAN ZUCI...
General Fictionlabari Mai cike da soyayya hade da sarkakiya labari ne Mai matukar karya zuciya kuma labari ne Akan matsalolin dake faruwa