*KUKAN ZUCI....*💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)*NA:SLIMZY✍🏻*
Watpadd@slimzy33*5*
Idanuwansa da suka Kada sukai jajir yake kallonta itama kallonsa takeyi da sauri ya matsa gefe "mammy shin kinsan waye a gabanki kuwa?"
"Sadik Kaine a gabana sadik ina bukatar taimako idona ya rufe tun ranan Dana Fara ganinka nakejin wani Abu game dakai Amma nikaina bansan wani irin Abu bane kawai inaji a jikina cewar Kaine zaka taimakeni"
Kallonta yakeyi cikin rashin fahimta ya mike da sauri yaja da Baya, idonta ya rufe wani irin Abu takeji a jikinta "kadaina guduna domin nadade ina adduar Allah ya Kara hadani dakai sanan karya kakeyi kace zaka gujeni domin ina ganin abinda nakeji kaima kanajinsa ina ganinsa a kwayar idonka"ta lumshe shanyayyun idanuwanta ta Kara budesu Akansa tana kokarin matsowa idanuwanta na Kan jikinsa tana binsa da wani irin kallo Wanda samm mammy bata cikin hayyacinta,
Tana kokarin matsawa akayi sallama cikin parlorn da sauri ta dawo hayyacinta gabanta ya yanke ya Fadi ta kalli lubabatu wadda take binsu da kallo Duka su biyun taso ta fahimci wani Abu Amma sai kawai ta tsugunna "kinyi Baki mammy"
"Baki da sassafen nan?su waye sukazo mana da safe haka?"
Daga bakin kofar dakin aka amsa da "nice nan ko in koma ne bakisan da zuwana ba?au har wani lokacine na zuwa gidanku da Wanda Bana zuwa ba?to ba wajenki nazo ba wajen Dan uwana nazo tsintacciyar mage"
Girgiza Kai mammy tayi Inda sabo ta Saba da halin kanwar alhaji "Baya gari yayi tafiya yaje Germany Ku zauna mana Bari lubabatu ta kawo muku abinci"
"Ba abinci nazoci ba zakiyimun makirci kuna zaune keda gardi a daki Ku biyu waye yasan me kuke kullawa?
Dariya mammy tayi "to sirikinki ne shine Wanda afee keson ta aura"
Tabe baki tayi "ba abinci nazoci ba Zan tafi idan ya dawo gari kice masa inaso mu hadu Dan inba kince ba bazai nemeniba kin Shiga tsakanina da Dan uwana,"tasa Kai ta fice tanata sababi,sosai ran mammy ya sosu Inda sabo ta Saba Amma Wanda akeyi Mata hakan danshi Sam bata gabansa bashida lokacinta lokacinsa na zurga zurgar kasashen duniya ne da Tara dukiya,ya mallaka Mata kudade da dukiya Amma basune bukatarta ba ko hakkin aure Baya sauke Mata,
Jikin sadik sosai yayi sanyi tabashi tausayi take yaji dik baiji dadin yadda akayi Mata ba mikewa tayi ta barshi zaune parlorn ya kalli agogo ya dace ace yanzun Yana sabon office dinsa Amma Yana tafiya yasan rikicin afee sanan Anya zai bar mammy cikin wanan halin kuwa?
********
Zaune yake a Saman mota da bakin glass a idonsa kyakkyawa ne ajin farko lokacin da mota tazo tayi parking can gefensa tsurarun mutane na kaiwa da komowa shiru unguwar,sauke glass din motar afee tayi tanabin gidajen da kallo tana sanye da Maroon din hijabi Mai kamar Riga Wanda Mata ke yayi yanzun,
Ta cikin bakin glass idonsa ya sauka akanta what?dirowa yayi daga Saman motar Yana cigaba da kallon tsantsar kyau da kwarjini uwa uba wani irin mugun kamanni da tayi masa da Ammy tabbas da zaa hadasu da Ammy babu abinda ya rabasu kamanninsu kamar an tsaga Kara take yaji kibiyar Sonta ta sokesa wani irin sanyin dadi yakeji a wanan lokacin,wayar hannunsa ya Maza ya Danna ya seta camera cikin saa ta juyi ya kashe Mata hoto....Cikin takun kasaita ya karasa gaban motar ya zuba hannuwansa a aljihu Yana kallonta ji tayi tamkar an tsaya akanta tana cikin magana da driver "nifa Malam Audi bangane gidan ba gaskiya mujuya kawai Kar mammy taga mun Dade kuma Ruhina Yana jirana"
"Ruhinta?"ya maimaita a Ransa cikin isa yace "kinada wani ruhi Daya wuceni ?nine ruhinki saboda kedin jinina ce"da sauri ta waigo taga wani Dan karankada miyar keyi Mata magana cike da tsiwa tana kallon fuskarsa tasamu kanta da kasa masa magana,zare gilashin idonsa yayi sunana "aliyu Amma haidar wasunke kirana wasu Kan kirani da zaki,ya sunanki?"
YOU ARE READING
KUKAN ZUCI...
General Fictionlabari Mai cike da soyayya hade da sarkakiya labari ne Mai matukar karya zuciya kuma labari ne Akan matsalolin dake faruwa