part 1

169 9 5
                                    

*FRIENDSHIP*
        *_(A BOTA)_*

     *_SHOT STORY_*
*[GAJEREN LABARI]*

*(E.W.F)*

By
Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461.

_NASAN DA YAWA ZASU DAUK'A ABUNDA YA SHAFI SOYAYYA KAD'AI NE ACIKIN LABARIN, TO BA HAKA BANE KAI MAI KARATU IDAN KA KARANTA ZAKA BAMA KANKA ANSA, DOMIN DARASIN YANA DA MUTUK'AR MUHIMMANCI MUJE ZUWA..........._

       Page.......1

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un, wannan wace irin musiba ce haka? Duka-duka shekarar ku nawa da aure yusra? Amma ace har irin wannan case d'in ya soma faruwa daku! Banji dad'i ba kuma wallahi usman yayi disappointing d'ina ban zaci haka daga garesa ba, duk da irin matsalar da aka samu tsakanin ku aka samu aka shawo kan Abbyn ku kan batun auren ku, amman shine zai mana wannan sakayyar? ban san me zance miki ba yanzu daya wuce kiyi hakuri ki cigaba da addua saboda inba hakurin ba da adduar babu abunda zan iya maki, tunda ke kika siyo ma kanki Yusra ke kika jawo komi ga irin ranar da ake jiye maki, ni banda abunyi yanzu tunda kince duk da wannan abun kina son mijinki kince kuma kar nakai maganar bakin Abbyn ku, to saiki kara hakuri akan wanda kike yi don wannan ba karamar magana bace"

Kuka sosai Yusrar keyi na zallar bak'in cikin dake cikin zuciyarta, tana tunanin idan ta gaya ma wani damuwar ta zataji nauyin da kirjinta yai mata ya ragu, amman sai taji ya k'aru ya zatayi wai? Tana son mafita amman sanar da Abby wannan maganar kamar ta janyo rabuwarta da usman, kuma ahalin yanzu bata jin xata iya rayuwa babu shi.

Ya koyar da ita abubuwan da ba zata iya jin zata samesu ga wani mijin ba inba shi ba, soyayyar da take masa banda k'aruwa babu abunda take duk irin wulakancin da yake mata.

"Kibar wannan kukan haka karki cuci kanki da abunda yake cikin ki, kuka baya maganin damuwa saima karata da zai, bari na wuce zanyi tunanin yadda zamu b'ullo ma lamarin insha Allah komi zai dai-daita, kici gaba da addua karki fasa ai baifi karfin Allah ba."

Tana kukan ta ce, "To Ammi nagode sosai don Allah karki sanar da Abby, inso samune ko Noor kar kuyi maganar da ita Ammi don Allah, kinsan halin ta duk halin su d'aya da Abby"

D'an murmushi Ammin tayi ta ce, "In banda abunki Ina ni ina sanad da noor wannan maganar, ai bata yara bace insha Allah bamai jin maganar Yusra, kedai ki k'ara hakuri zaman Aure ya gaji matsaloli,ba kamar idan kun aikata kuskure kafi aure, to kau dole zaki runtse idonki."

Ta rakata wurin mota inda guard d'in da suka rakota suke tsaye, har saida taga ficewar motatocin sannan ta dawo ciki tana ta jan ajiyar zuciya, batai tunanin zata iya sanar da Ammi wannan maganar cikin sauk'i haka ba, duba da nauyin abun.

*SARDAUNA ESTATE*

"Wa iyazubillah sham ki refa ma kanki asiri tun kafin na juye miki masifar dake bisa kaina Aah, nace bana sonji dole ne? please ki kyale ni da maganar *ANNUR* ya dad'e bai kashe kansa ba karewar ya shiga wani hali, inhar don haka kike son addaba ma rayuwata kiyi ma Allah ki shafa mun lafiya, watau ga *NOOR* sakarya bata san meke mata ciwo ba sai ya shukani a cikin sanyi shi yana can yana zancen sa hankali kwance bai damu da illar da sanyin zai mun ba, idan mura ta kamani kinga ai bashi da wata damuwa nice zan ji ajikina, to ya rik'e ilimin sa bana so na gode Allah da baiyyo ni dak'ik'iya ba dana shiga uku.
Kuma sadda Abby ya kawo ni nikad'ai na ya kawo ba tare dashi ba, don babu shi yanzu bazan kasa cigaba da rayuwa ba, in kina son zaman lafiya dani karki sake ambata mun ko Alphabet din sunan sa"

Danne dariyar ta kawai sham keyi saboda dai ta lura NOOR ta gama kamu wa, ba komi ke damun ta ba face tsantsar kishi inbacin haka ita bata ga wani abun daukar zafi acikin lamarin nasu ba, ita ta tanka ne ma don kar taga tana ta fushi bata bata baki akai ba, inbacin haka babu mai shiga tsakanin *NOOR DA ANNOR* nan take zakaji kunya shiyasa duk fad'an da zasuyi inba abun yai zafi sosai ba bamai shiga.

FRIENDSHIP (A BOTA)Where stories live. Discover now