Part 16

35 4 1
                                    

*FRIENDSHIP*
            *(ABOTA)*

*_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_

*E.W.F*

By
Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461.

    Page......16

Sai gab magriba muka iso Abuja gidan kanwar Abby ce ba yadda banyi da shi ya tsaya ya kwana ba yace tafiya zaiyi, duk raina ajagule saboda dai tsoro nakeji kar wani abu ya same sa ga dare yayi, hanyar ba kyau gareta ba daker ya tsaya ma yaci wani abu yai sallar magriba sannan na rakosa zai tafi, idona yayi kwal-kwal kamar zanyi kuka na tsaya gaban sa ina wasa da yatsuna, shi kuma sai aikin kallona yake ban san kukan kona miye ba amman ni araina nasan ba zai wuce na kewarsa ba, da kuma tafiyar dare da zaiyi sai kokari nake kar kwalla ta tazubo.
Murmushin sa naji sannan ya matso inda nake sosai kamar zai rungumeni, sassanyen k'amshin sa ya ratsani har cikin raina dole na lumshe idona inajin wani sabon abu tattare dani, d'an turo bakina nayi nace, "ka gani dare yana karayi"

Iska ya furzar yana shafa kanshi zuwa fuska yace cikin wata irin sassanyar murya data sake kashe mun jiki, "Besty jinake kamar na dawwama ahaka gabanki, ji nake kamar amaido da auren mu gobe kema kina so ko?"

Wani kallo ma dalla masa da idanuna masu kwallah aciki, na d'an matsa baya ina shagwab'e fuska nace "nidai Aa"

Murmushi yayi yace, "ba sai na b'ata bakina wajen tambayarki ba abunda nakeji kema kina ji, kunya ce kawai zata hanaki nuna mani"

Saurin juya masa baya nayi nace, "ni karka wani mun sharri ba haka bane, kuma kasandai hanyar nan ba kyau ne da ita ba kawuce ka tafi"

Ya rungume hannun sa yana jinsa cikin nishad'i yace, "besty korata kike yi? Shikenan na tafi tunda kin gaji dani"

Yai kamar zai tafi bansan na sha gabansa ba kwalla sharrrrr suka zubo nace da muryar kuka, "nifa ba haka bane, tsoro nakeji katafi ka barni, kuma ga hanya ba kyau"

cikin wani style ya lumshe idonsa ya bud'esu akaina jan hanuna yayi zuwa wajen motar ya bude kofar baya na zauna shi kuma ya durkusa gabana, d'ago hab'ata yayi yana kallon cikin idona yayin da naji wani abu yana tsarga mun, sai wasu suka sake silalowa runtse idonsa yayi yace "ya salam Besty kina son ki haukata ni ne?, pls kibar kukan nan karkija na shanye hawayen bazan iya jure ganin su ba, inda kinsan yadda nakeji dakin tausaya mani"

Na sa hannu zan share hawayen ya rigani, cikin tattashi da soyayya yake goge mun su yana son kallon idona ina nok'ewa, saida ya gama gogewa sannan ya dora d'an yatsan sa saman lips d'ina, ya shafa kadan nai saurin janye fuskata yai ajiyar zuciya yace "Besty haka lips dinke keda taushi, bakiji ba yadda suka biya raina zaki sammun kad'an"

Innalillahi da yasan yadda nakeji da bazai mun wannan maganar ba, runtse idona nayi inajin tsikar jikina tana tashi, na sauke wani gajeren numfashi nace "zan tafi cikin gida ni dai"

Murmushi yayi yana cije gefen bakin sa yace, "Ayya sorry ashe ba Besty na kunya gareta, ba komi kwai randa zaki bani da kanki, inma ban shaba har kuka sai kinyi"

Ai ba shiri dole na tashi zan tafi ya saurin rik'eni yana jawoni ban ankare ba na shige kirjinsa ya rufe dani, ban san ya zan kwatanta yadda naji ba amman tabbas abun babba ne, inda na biye masa abunda zai mun babbane na kwace jikina ban sake tsayawa ba sai dakin da aka saukeni na fada kan gadon ina sauke numfashi, jinake har sannan ina lik'e da jikinsa wayyo Allah gaskiya Annur mayen soyayya ne.

********

Sadda na koma gida na iske anata shirin biki ba kama hannun yaro ashe harda na yaya yusuf dana yaya yusra xa'ai, nai mamaki sosai da naji zatai wani auren saida muka kulle a d'aki take bani labarin irin halin da usman yake ciki akanta.

FRIENDSHIP (A BOTA)Where stories live. Discover now