*FRIENDSHIP*
*(ABOTA)**_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_*E.W.F*
By
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461.Page.......5
"Har kin k'araso sannu da zuwa, feedy wannan ce Noor"
Wani banzan kallo ta sake jifata dashi tana tab'e baki bata ce komi ba ta juya ga kawarta da suke tare tana ce mata, "muje suwaiba"
Raina a b'ace na ce masa, "miye had'ina da waccen da take hararata"
Shafa kanshi yake hannunsa d'aya cikin aljihu sannan ya ce, "don mine her pls, ina zamu zauna karki gaji da tsayuwa ko mota zamu shiga"
Na dalla masa harara na ce, "Allah ya rufa asiri na shiga motar ka"
Dariya yayi yana cewa, "naji ke ai hukuma ce sai lalashi bari ga hamid nan ya samar mana wajen zama"
Daidai isowar sa na d'an saki fuskata muka gaisa yake cewa, "ka iya zab'en wajen da ya dace mu zauna ina zamuje, tace ba zata shiga mota ta ba"
Hamid ya ce, "kaima kasan ai ba zata shiga ba koni ce bazan shiga ba, yanzu abunda za'ai mu k'ara gaba akwai inda ya dace ku zauna"
Gaba mukai muna tafiya sai surutu yake mun nai banza dashi Hamid saidai yayi dariya kawai har muka iso wani waje mai kyau, akwai wasu can gefen mu amman sunyi nisa komi zamu ce bazasu jimu ba Hamid daman akwai darduma hannunsa ya dauko a mota ya shimfid'a mana ba laifi babba ce na zauna gefe guda nesa da Annur, sannan Hamid d'in ya ce "zanga dr ado bari naje na dawo, karki tafi zan bada sak'o akaima mutuniya ta"
Nai masa murmushi na ce, "inka dad'e tafiya zanyi fah"
Ya ce, "no bazan jima ba insha Allah, Abokina asha fira lafiya"
Dotsi ya dauka ya jefesa shikuma ya ruga yabar mu nan, duk sai naji wani iri ina ta wasa da yatsuna duk da ba kallon sa nake ba tabbas kallona yake yi don jikina ya bani, na kasa cewa komi shima kuma duk surutun baice mun komi ba, na du a agogon hannu na naga har shad'aya tayi na d'ago na dube sa still yana ta kallona na murgud'a bakina na ce, "bana son ana kallo na haka"
Ajiyar zuciya yaja ya ce, "I'm sorry to, naga kinzo gani gaki kuma kinyi shiru kar inyi magana kuma ki burkice kice kin ma fasa fad'ar abunda kikazo dashi"
Na ce, "kuma ba zaka tambaye ni ba saikai mun banza"
Had'e hannuwan sa yayi duka alamun ban hakuri ya ce, "don Allah Noor kiyi hakuri ban san shirun zata b'ata miki ba ai"
K'unshe dariya ta nayi inajin dad'i araina don alamu sun nuna bazai wahalar gyaruwa ba, na ce masa "rannan ka bani chocolate kana neman amuncewata muyi *FRIENDSHIP* ko?"
Ya ce, "eh haka nace amman kika k'i yarda"
Na ce, "yanzun ma ba yarda nayi completely ba, zan yarda ne da sharad'i guda"
Kallona yayi da alamun tambaya kafin ya ce, "wane irin sharad'i ne wannan zanyi koma miye"
Na ce, "sab'awa ko karya sharad'in na nufin hannun riga nida kai, inhar kayi alk'awarin ba zaka sab'a ba zan yi *ABOTA* dakai ANNUR"
Huci ya saki yana shafar sumar sa datasha gyara sai ya kalleni saiya sauke kai, sannan ya ce "na amunce ki fad'a zanbi inhar bai sab'a sharia ba"
Na ce, "Alhamdulillahi, Annur ni bazan ABOTA da wanda bazan amfana dashi ba ma'ana dole zaka ringa koya mun karatu, na d'aya kenan na biyu kuma shine dole ne ka ringa fitowa class a time d'in da duk wani d'alibi hake shigowa, na uku dole ne ka girmama malami ka bashi girma kai masa biyayya kamar gadda duk wani d'alibi mai hankali da sanin ya kamata yakeyi, na uku dole ne ka sauke wannan girman kan naka da kake dashi wanda mutane ke shakkar yi maka magana, kai ma kuma baka tanka masu ka sani mutane rahma ne Annur duk mutumen da baida jama'a ya shiga uku, saboda tun kafin mutum yaje lahira shaidar da mutane suka bada kanshi itace sheda, kuma mutanen nan daka raina sune zasu kaika kabarinka indan baka gyara alak'arka dasu ba gaya mun wanda za'a ce maka ka mutu yaje ta'aziyyarka, don haka inhar ka yarda zaka gyara wad'anan kurakuran naka 100% ni kuma zan ansheka zan mayar dakai kamar Yaya Yusuf d'ina, don haka shawara ta rage gareka duk sadda ka yanke zaka gyara kai mun waya, inhar kasan ba akan maganar nan bace karka sake kai mun magana ko ahanya ko bakin class din mu balle ta waya"
YOU ARE READING
FRIENDSHIP (A BOTA)
Fanfictiontak'aitaccen labari ne akan abotar mace da namiji ga y'an jami'a, da matan aure shin ya ya kamata ki mu'amalanci namiji matsayinki na mace, ku shigo cikin kabarin domin jin yadda zata kasance.