*FRIENDSHIP*
*(ABOTA)**_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_*E.W.F*
By
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461.Page.......3
"Waike meye haka? Jiya saboda kiran ki har saida cajina ya k'are"
Sake shigewa nayi cikin bargona ina cewa cikin muryar bacci, "ina ruwa na da karewar cajin ka ni nace kaita kira na"
"Au haka ma zakice ko? Don ma kin samu na kiraki zaki mun rashin kirkin da kika saba ko."
"Kaga karka b'ata mun rai da sassafen nan bacin kai ka tashe ni ina bacci na mai dad'i"
Ya ce, "yai maki kyau sai anjima"
Yar dariya nayi k'asa-k'asa na ce, "kai wallahi ka cika saurin fushi to miye akai yanzu zaka wani k'ule? Kama yi breakfast"
Lumshe idonsa yayi jin har ta fara lallashin sa inda yake jin dadinta kenan indai tasan ta b'ata mashi xata kuma lallashe shi, sai ya langab'e kamar wani yaro ya ce, "banyi ban bana yi kuma"
Murmushi nayi nasan yaji haushi sai na ce, "Ayya sorry dan lelen mama kayi breakfast d'inka kaji"
Har ransa yaji dad'i sai ya sake mak'alewa ya ce, "nifa bana ci"
Na ce, "please Annur yau fa zan dawo don Allah kaci"
Gefen bakin sa ya ciza yana lumshe idonsa ya ce, "inma baki dawo ba gab nake na biyo ki"
Yar dariya nayi na ce, "ina zaka iya gano gombe daga katsina"
"Kina wasa kenan, ki wuce yau baki dawo ba kigani"
Daga nan fira ta b'arke nidashi muyi gardama muyi wasa da dariya karshe dai da fad'a mukai sallama, dirowa nayi na shige wanka nasan sham ta gama had'a mana komi saida na shirya tsaf sannan na wuce cikin gida nayi breakfast, Abby ya fice tuni Ammi kad'ai ce yau bata je ba sai taga ta fiya ta.
Wajen shabiyun rana muka bar gombe sai katsina ta dikko d'akin kara kunya garesu ba dai tsoro ba.*********
Mafarin had'uwa ta da Annur ranar farko da muka shigo makaranta bamu san kowa ba, kunsan dai yadda sabon d'an makaranta yake in kana neman wuri kaita shan wahala, nida sham muketa yawo neman department d'in mu duk wanda muka tambaya sai ya rena mana hankali to haka mukai da Annur, mun gaji ainun munsha wuya sai muka ga mota ta parker bakin wani block, inda muke zaune muna hutawa Annur ne farkon fitowa sai Hamid, sham ta ce, "kaiiiii Noor tunda muka shigo banga saurayin daya burgeni irin wannan ba, akwai dai iya d'aukar wanka"
Dogon tsaki nayi cikin masifa ta dake cikina na rasa wanda zan juye mawa na ce da d'an karfi, "dalla can rufe mun baki wannan k'azamin ne abun burgewa muji ma da wahalar da muka sha yau, ki kyale don Allah"
Ashe yaji abunda na ce masa ita kuma sai ta ce, "Allah ya baki hkr bani na kar zomon ba, ni daki yadda naga suna da hankali ba zasu cuce mu ba mu tambayesu mana"
K'are masu kallo nayi sai kuma naga nima sunyi mun kama da masu hankali, na tashi muka isa wajen su hijab ce jikina har k'asa da safa k'afa ta sai yar jikkata yar karama da wayata ga hannu, fuskata black take babu komi daka kalleni kasan munsha wuya, duk idona yai kwal-kwal saboda wahala sallama mukai masu su uku ne duk suka kallomu yayin da direct idon Annur akaina ya sauka bazan iya gane kallon da yake mun ba, amman dana tab'a tambayar sa sai yace mani wai kawai yaga idanuwa na sun banbanta da na sauran mutanen daya saba gani, shi bai tab'a ganin idon irin nawa ba shiyasa yaita kallona ya kasa dainawa, sham ce take masu magana akan inda muke nema da irin wahalar da aka bamu, dariya sukai tayi mana har raina ya b'aci shi kuma Annur baice komi ba time to time dai still idonmu zai had'u kafin ma su Hamid su gama dariyar su bamu ansa sai shi ya ce, "gaskiya ba'a kyauta maku ba kunsha wahala bari na kwatanta maku ai wajen baida wahala don kun samu yan iska ne"
YOU ARE READING
FRIENDSHIP (A BOTA)
Fanfictiontak'aitaccen labari ne akan abotar mace da namiji ga y'an jami'a, da matan aure shin ya ya kamata ki mu'amalanci namiji matsayinki na mace, ku shigo cikin kabarin domin jin yadda zata kasance.