*FRIENDSHIP*
*ABOTA**SHOT STORY*
*[GAJEREN LABARI]**E.W.F*
BY
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461.Page......17
*Last page*
Abokan nasa da suka rakoshi duka su biyu ne, daga wani shamsu sai Hamid, Bilal yau ya koma tun safe Hamid kuma kila sai gobe yau kam yayi dare, kafin tafiyar su mama safiya kanwar Ammi saida suka sani nayi wanka da ruwan turare, sannan suka shirya ni ciki wata lifaya mai sulb'in gaske bayan na saka top d'ina fara sol sai undy na, sannan aka nada mun ita tare da bad'eni da iyayen turaruka, ba karya nai kyau ainun.
Muna zaune falo sukai sallama su sham ne suka tarbesu tare da gaishe gaishe, uban kilishin da aka aje masu da dambun nama ne suka kawo masu nad'e cikin takadda, sai lemukan su da swan daman wannan ce al'adar mu sai tsokanar sa suke yana ramawa, saida suka ba su sham check d'in 200k sannan nai magana, cikin sanyi da natsuwa muka gaisawa sukai mana nasiha sosai mai ratsa jiki, har hawaye suka balle mani ina sharewa Annur d'in yace, "to gaskiya nasihar ta isa haka, kungani kun samun baby kuka"
Hamid yace "iyye! To ke baby kiyi hkr yanzu zamu tafi sai kayi aikin lallashi"Tare da su sham duk suka tafi hankalina ya tashi ainun, ganin da gaske su sham sun tafi kukana sai ya karu na dunk'ule waje guda ina risgar kukan, tsoro ne yake kamani ba kala guda ba, inajin tsoron sabuwar rayuwar dana shiga yanzu nima zan zama d'aya daga cikin matan aure, gida zan rik'e kamar sauran matan da suke rik'e da gidajen su, zan tara zuri'a kamar kowa.
Ya Allah ka bani ikon rik'e wannan girma daya hau kaina, ya Allah ka tsare mu daga sharri masheranta ka tabbatar mana da duk abunda yake alkairi acikin wannan auren, na jima sosai ina Yi mana addua mai yawa da neman albarka, duk ina kukan har sadda naji karar rufe kofar falon namu na lumshe idona inajin wani faduwar gaba, tabbas Annur yau bazai kyale ni ba duk wani nok'e-nok'e na ba yadda zan bazai fasa ba.Muryar sa kadai ta isa ta gaya mun irin zallar farin cikin da yake ciki, salama yayi mun bana tunanin ma yaji ansar dana bashi saboda kukan dana sha muryata ta shak'e sosai, kusada ni ya zo ya zauna ba tare da wani jinkiri ba ya dago kaina dole na bude idanuna da sukai mun nauyi, hada ido mukai ya sakar mun wani lallausan murmushi wanda bazan iya cewa ya tab'a yi mani shi ba.
Ahankali na ja idanun na lumshe su saboda bazan iya maida masa martani ba, addua yayi mun bayan ya dafa kaina sannan ya kamo hannuna muka mik'e ya dauki ledar daya shigo da ita yajani har cikin daya daga cikin bedroom din da aka shirya mani, ba karya nasha kayan d'aki kamar diyar shugaban k'asa, sosai Abby ya saki kid'i akai mana kaya na kece raini sannan ya mallaka mana wannan gidan yace idan Annur ya fara daukar albashi saiya biyasa ahankali, hakan yai mani dadi don daman nasan baya da inda zai ajeni banda wajen mama, Abban sa kuma nauyi ya masa yawa shiyasa Abby yai haka.
Gefen gado ya zaunar dani sannan ya sunkuyo yana lek'o fuskata cikin zazzak'ar muryar sa yace cikin salon jan hankali "baby plssss mana"
Narke masa fuska nayi ina kauda kaina daga kallon sa muryar tawa can ciki sosai nace, "me nayi to"
Murmushi yayi yace, "ko d'an smile ba zakiyi mani ba, karki b'ata mana rana mana duk wannan kuke kuken kibarsu haka don Allah, kefa kika ce saini"
Duka na kai masa ya goce yana dariya cikin rawar murya zan sake sakin wani kukan nace, "kenan karnayi kukan rabuwa da Ammi na? Sabuwar rayuwa na shigo wadda ban santa ba, bansan ya zataso mun ba shine kace kar nayi kuka?"
Hawayen suka shararo mani cikin sauri yazo ya rungumeni tsam ajikinsa cikin lallashi yace, "Ayya ba haka nake nufi ba baby, kiyi hakuri tsokanar ki nake nasan dole ne kiji ba dadi, amman ki sani haka kowacce mace had'a nata family d'in, kiyi mana addua muma Allah ya sa muga namu family d'in yadda Ammi ta badaki cikin mutunci, kema ki nada taki y'ar haka,insha Allahu ba zakiyi dana sanin zabata ba zanyi iyakar kokarina ganin na saki farin ciki, muddin kika ga nasaki hawaye bada son zuciyata ba wani abune daga Allah, ina fatan noor d'ina zata ba Annur d'inta had'inkai mu raya wannan daren mai cike da tarin farin ciki"
YOU ARE READING
FRIENDSHIP (A BOTA)
Fanfictiontak'aitaccen labari ne akan abotar mace da namiji ga y'an jami'a, da matan aure shin ya ya kamata ki mu'amalanci namiji matsayinki na mace, ku shigo cikin kabarin domin jin yadda zata kasance.