*FRIENDSHIP*
*(ABOTA)**_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_*E.W.F*
By
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461.Page.......14
Kowa ya hallara acikin babban falon hajiya, wannan hon d'in da mukaji su Abby ne suka iso harda baba Azumi da yaya Yusra da Yaya Yusuf, khalil ne babu yana makaranta ga maman Annur ga kuma shi Annur d'in, sai kuma Abban Annur d'in da yazo daga baya daman yana cikin kanon mama ta kirasa yazo akwai maganar da za'ai, bayan duk wasu gaishe-gaishe da za'ai akayi ni dai na mak'ure can wajen Ammi kaina k'asa ko da wasa ban ma kalli Abby ba balle na gaidashi, shima bai damu na gaida shin ba so dai kawai yake nazo inda yake nak'iya.
Hajiya ce tace, "ANNUR bude mana taron da addua"
Cikin natsuwa yafara karanto fatihah cikin zazzak'ar muryar sa mai ratsa zuciya, ya gama ya karanto adduoi dogaye sannan ya kare da salatin annabi, duk muka shafa tare sannan Hajiya ta soma magana.
"Nasan kowa yasan meye mak'asudin daya tara mu anan, don haka ba zamu b'ata lokaci ba zamuyi abunda ya tara mun, Hussain Naja'atu tazo mun da kuken zakai mata auren dole bayan cireta da kayi amakaranta, da irin tsanantawar da kake masu agidan naku duk naji dalilin ka na cireta makaranta amman babu dalilin da zai saka kayi mata auren dole tunda bata so, kuma addini yayi hani da wannan don haka ni a matsayina na mahaifiyar uwarta kuma sarakuwa a wajen ka ina umurtarka daga aura ma Noor wannan yaron, don nidai banga wani nakasu tattare dashi ba, har sai munji daga bakin iyayensa sannan ne xamu iya yanke masa hukunci"
Abby yace, "Hajiya nayi kuskure ta wani wajen, ta wani wajen kuma bani da laifi, hakika anso arabani da y'ay'ana ta karfi da yaji, an cusa mani tsanar su da son suyi nesa dani, duk abunda ya biyo bayan kwana kin nan bani bane ba asalin halina bane, ban tab'a ganin muguwar yar uwa ba irin habiba, Ta cuceni ashe asiri tayi domin shiga tsakanina da iyalina, Allah sai ya tona mata asiri duk abunda tayi baba azumi ta ganta itace ma ta tono abun,kinji musabbabin da yajawo har na ringa wannan abubuwa, har maganar auren noor ni dai da kaina bansan ma nayi ba bazan ma iya tuna abunda nace ba, ai bazan iya yima noor auren dole ba inhar Annur d'in take so kuma yana da nasabar da za'a iya bashi aure ba abunda zai hana"
Hajiya tace, "to Alhamdulillahi Allah abun godiya, yanzu dai ga Annur ga maman sa ga kuma baban sa, muna son muji waye Annur daga bakin daya daga cikin ku"
Annur ya tsura ma mama ido ganin tashin hankali ya bayyana akan fuskar ta, tayi kasa da kanta yayin da shi kuma abban yake ta zaro ido, an rasa wanda zai magana Annur duk inda hankalin sa yakai ya tashi, cikin raunanniyar yace "Mama, Abba me kuke son nuna wa? Anyi tambaya kun kasa cewa komi, me hakan ke nufi"
Abban ne yai karfin halin yin magana don mama kuka ta fara k'asa-k'asa, cikin disashewar murya Abban ya fara magana da cewa, "Hakika ance ranar wanka ba'a boyon cibi, duk da nasan cewa kasan bani ne na haifeka ba hakan bai hana kayi mani biyayya ba Annur, ina alfahari da kai akodayaushe, azahirin gaskiya shine maman ka gata nan zaune, ta shiga k'angin rayuwa tun kafin haihuwar ka, babanka yaya ne uban mu guda dashi sun had'u da mahaifiyarka ne a rugarsu dake karkashin bauchi, Allah ya had'a jinin su sosai har soyayya mai karfin gaske ta kullu tsakanin su, saidai kash zuri'ar mu bama auren fulani domin akwai babbar gaba tsakaninmu mu makiyaya dasu, shiyasa aka haramtama kowa auren fulani, awannan lokacin kuma baban ka Aliyu sunyi nisa ainun da kaunar junan su shida mahaifiyar ka, wanda yaji bazai tab'a rabuwa da ita ba har ciwo ya kwanta asibiti amman duk abanza.
Itama kuma mamanka uwar rik'onta tace inhar ta cigaba da had'uwa dakai ita da ita har abadan abada, hakance kuma ta faru daman kuma mamanka bata da kowa sai wannan diyar wan baban tata dake rik'onta, itama kuma tazo ta rasu rashin galihu ya taso ma jamila maman ka kenan, bata wajen da zata yada kafad'arta idan dare yayi, haka zalika ba wanda zai iya bata lomar abinci daga safe har dare, wannan dalilin yasa Aliyu da yazo yaganta haka sai kawai ya d'auketa suka bar rugar tasu wanda wannan tafiyar ce har yau bata koma ba, Aliyu yakai jamila cikin dangin mu wanda tashin farko baban mu yace inhar bai fiddaki daga gidan ba to shima ya yafesa har abadan, zuciya tasa Aliyu yace eh yaji bazai iya rabuwa da jamila ba bayan bata da kowa sai shi, baba bai saurare sa ba haka suka baro gida basu da wajen zuwa, to ni dai iyakar abunda zan iya cewa kenan daga nan ban sake sanin halin da suke ciki ba sai da muka had'u da jamila tana bara bakin titi kai lokacin kana goye baka wuce shekara d'aya ba, tambayar farko da nayi mata cewar wannan d'an fa tace nata ne kuma itada Aliyu suka haifesa, nai mamaki saboda bayan barin Aliyu gida da kamar wata uku aka tsinci gawarsa wani mai mota ya banke sa ya gudu, baban mu ya shiga tashin hankali matsananci yai kuka kamar ba gobe, saboda tuna irin rabuwar da sukai da Aliyun, nan dai yace ya yafe masa akai masa sutura aka kaisa makwancinsa, bayan nan andad'e sosai shine muka had'u da jamila tana bara, na kama masu gida na dauki duk wasu dawainiyar su tayau da kullin, Annur kuma na sashi makaranta komin sa nine, yanzu sauran labari yana gareki jamila muji ta yadda kuka samar da Annur."Hankalin Annur yai masifar tashi ainun, don kallo daya zakai masa ka gasgata hakan, zufa yake kasarik'a kamar an zuba masa ruwa idonsa kuma yayi jajir kamar jini zai xubo daga ciki.
Ni kaina banda fad'uwar gaba babu abunda nakeji, tsoro ya kamani zuciyata bugawa kawai take ina Addua cikin zuciyata "Ya Allah kasa Annur dina ta hanyar aure aka samar dashi, muddin ba haka bane nasan Abby bazai tab'a barina na auri dan gaba da fatiha, amman in haka ne Annur bashi da laifi sadda aka samar dashi basani ba, ni koma hakan ne wallahi zan iya rayuwa dashi har illa masha Allah..............
Hakiya ce tace, "maman Annur ke muke saurare muji daga gareki, bayan barin ku gidan su baban Annur ina kuka tafi? Shin kunyi aure dashi har aka samu Annur ko kuma ya abun yake?"
Hawaye kawai mama keyi tana shashsheka Ammi ce keta tausarta sannan cikin disasshiyar murya tafara magana tana kukan.
Tace, "bayan barin mu gidan su Aliyu munyi yawon neman inda zamu zauna Abun bai yuwu ba, kwatsam muka had'u da abokinsa a hanya zai wuce sai ya tsaya, suka gaisa dashi yake tambayar inda zamu ya sanar dashi dai halin da muke ciki a takaice, shine fa ya dauke mu muka taho katsina gida ya bamu muka fara zama, wannan zaman da muka farayi da baban Annur na dan lokaci mun fahimci cewar tabbas inhar bamu dauki wani mataki na shaid'an zai iya rabbatar mu, don kowa yana cike da begen d'an uwansa karma ace dare in yayi, muna raba dare dashi dakina muna fira sai yakai zuciyarsa nesa sannan yake tafiya, akwai ranar da tsotsayi yasanya da mun aikata b'arnan da bazamu tab'a yafe ma kanmu ba, wannan dalilin yasa yafara fita neman aiki koda aikin karfi ne, a haka dai har ya fara samun na kanshi da wannan dan rufin asirin ne muka biya haya, sannan ya daukan mukaje ga wani malamin addini kuma limami ne kofar kaura yake ya daura mana Aure, wannan auren anyi sa da wata biyu inama ta laulayin cikin Annur, yace mun zaije ganin gida komi kenan zai mun aike idan sun daidaita da baban sa,nai farinciki sosai amman kasan zuciyata tsoro ne da fargaba haka mukai sallama ya yafi, tunda ya tafi banda kwanciyar hankali kuka ne aikina da damuwa ga ciwo ina fama dashi, gashi ni kadai ban saba da mutanen unguwa ba don kowa kallon zaman dadiro muke nida shi, wannan tafiya itace rabuwar mu ta karshe dashi ban sake jin labarin sa ba koda wasa, har na haifi Annur duniya yai mun zafi, ba maitaimaki ba abokin magana kowa hantara ta yake yana aibata Mun yaro da *SHEGE* banida wani shaida sai Allah sai wannan limamin wanda bazan iya kai kaina wajen sa ba, kila ma yarasu iyanxu amman zan iya dafa alk'ur ani dana ALIYU (ANNUR) ba shege bane, dan sunna ne kamar sauran yaran da aka haifa ta hanyar aure, ban da kowa sai Allah shine nake gayama damuwata ganin ba sarki sai Allah dole na fara fita neman nakai, duk aikin dana nema babu mai bani wai ai ina goye da shegen d'a, jinai kamar in gudu daga wannan unguwa amma ba hali, kwatsam abokin baban Anur yazo rannan yaga halin da nake ciki, ya tambayi Aliyu sai na kama kuka ina bashi labarin abunda yafaru, shine yaje har can garin su yajiyo mani mummunan labarin mutuwar Aliyu, bazan iya kwatanta halin bakin cikin dana shiga ba nasan dai har karamin hauka saida nayi, haka nazo naita takaba har na gama saida na gama sannan ya dawo wai zai aure ni, ni kuma naga baxan iya auren kowa ba saboda zuciyata har yau tana begen Aliyu, rashin amuncewar da banba yasa ya koreni daga gidan gaba d'aya haka na dawo nida annur muna kwana bakin hanya, banda wata mafita dole na kama bara a wannan halin ne Allah ya kawo mana Kanen Aliyu watau Isma'il gashi nan, tunda muka had'u dashi komin mu ya daidaita saidai har yau har gobe mutanen da nake cikin su sheganta mani d'a suke, wallahi tallahi billahi ANNUR D'AN HALAK NE dan sunna ne da aure muka samesa amman idan kun yarda, in kuma baku yarda ba kuje kofar kaura ku nemi malam nayaku mai makarantar Allo limamin masallacin unguwar inhar yana nan to zai baku tabbacin shine ya d'aura mana aure da baban Annur.............
*SAURA 3 PAGE INSHA ALLAH*
Mom muhseen.✍🏻
YOU ARE READING
FRIENDSHIP (A BOTA)
Fanfictiontak'aitaccen labari ne akan abotar mace da namiji ga y'an jami'a, da matan aure shin ya ya kamata ki mu'amalanci namiji matsayinki na mace, ku shigo cikin kabarin domin jin yadda zata kasance.