part 4

30 5 1
                                    

*FRIENDSHIP*
            *(ABOTA)*

*_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_

*E.W.F*

By
Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461.

         Page.......4

Tun daga wannan ranar Annur ya fara addama rayuwata da naci, kodayaushe yana bakin department dinmu duk yadda nake k'in kula shi baya damuwa banda kallon banza da dizgashi ba abunda nake, amman baijin haushi wai ai da ban amunce da *ABOTAR* mu ba daban ansar masa chocolate ba, haushi ya kamani ganin yana mun gorin wata banzar chocolate da bata wuce ta d'ari biyu ba, bamu tashi daga lectures ba saida na nemo masa abunsa, sham na biye dani sai dariya take muka isa inda suke zama na tsaya daga nesa dasu ina shan mur na ce, "Hamid ka cema abokin ka ga chocolate d'insa indai akanta yake addabata to daga yau na huta"

Murmushi Hamid yayi yana duban Annur d'in da ya d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya ita kawai yake kallo Hamid ya ce, "Annur kana ji fa"

Dirowa yayi daga inda yake ya nufo inda muke tsaye, ya ce ma Sham "Allah yasa ba rashin mutunci kika rakota tayi mun ba"

Ta d'aga hannu ta ce, "Aa karka sani cikin rigimarku gaka gata nan ai"

Kallon juna mukai cije gefen bakinsa yayi yana d'an sakin wani kafirin murmushi na dalla masa harara na ce, "Anshi jarabarka daga yau karka sake damuna bana yin abotar"

Na jefa masa ga fuska saurin cab'ewa yayi yana dariya kafin ya ce, "kinga malama ai ba irinta na baki ba, indai kina son na kyaleki ki nemo mun irinta komi da komi"

Kamar na kwad'a masa mari na ce, "bazan nemo ba inbaka son wannan ka bari kuma inka kara bina saina kaika k'ara"

Dariya yayi naja sham muka tafi gida saida ta gama dariyar ta sannan ta ce, "ban ga aibun sa ba Noor yana sa k'ok'ari sosai inbacin matsala da yake ta samu da malamai ance da cikin yan aji hud'u yake"

Na b'alla mata harara na ce, "ke yayi dake mana miye dole sai ni to? So kike Abby yaji labari ina tarayya da wani k'ato"

Me zatai ba dariya ba ta ce, "Annur din ne k'ato fisabilillah"

Bai daina nacin bina ba har wasu yan mata sukejin haushina a cikin class d'in mu, ni ban ma san suna yi ba don bana hudda da kowa abunda ya kawoni shi nakeyi in ba sham ba bana kula kowa akwai da yawa masu son mu'amala dani nak'i bada fuska ni ban cika saurin yadda da mutum ba, mafarin yasa nake ta jan annur a k'asa sai na gama karantar sa naji har raina zuciyata ta amunta dashi sannan, to kuma hakan da nayi ya bani damar sanin wasu munanan halayen sa da yake yi, wanda suna daga cikin abunda ya hana shi yin gaba akaratunsa, ba kuma don baisan abunda yake ba yana sane tsabar girman kai ne da izgili gashi ba d'an kowa ba tunda mahaifinsa ba wani babba bane d'an kasuwa ne bama za'a had'ashi da Abby ba ko kadan. wad'anan abubuwan dana gano dangane dashi yasa na anshi *ABOTAR* sa, ranar da zan sanar dashi ni kaina ina jin ranar tayi mun dad'i tunda na tashi nakejin fad'uwar gaba dana tuna abunda zanyin, sham kanta saida ta gane ina cikin wani yana yi ta ce, "wai Noor akwai wani abune mai dad'i dazai zo mana? Naga kinata annashuwa kuma duk kin zama so cool"

Murmushi nayi sannan na gaya mata shawarar dana yanke cikin jin dad'i ta ce, "kin kyauta Allah ya taimakeki akan niyyarki"

Na ce, "bani wayarki na kira Hamid muyi magana"

Mik'o mani tayi da yake tun ranar da muka rage masu hanya ya anshi no d'inta suke gaisawa, kiran sa na shiga yi ina gyara zamana saman bed side yana d'auka na ce masa, "Hamid ina kwana"

Jin nice sai ya amsa da sakin fuska ya ce, "Allah yasa lafiya naga baki tab'a kirana ba"

D'an murmushi nayi na ce, "insha Allah daga yau zamu ringa waya, daman cema zanyi ka gaya ma Abokin ka ina son ganin shi"

FRIENDSHIP (A BOTA)Where stories live. Discover now