*FRIENDSHIP*
*(ABOTA)**_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_*E.W.F*
By
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461.Page......12
Wasa-wasa saida na kwana uku ina kiran kayin Annur wayar sa kashe, iyakar tashin hankali na shiga ciki bana cin abinci banda wani aiki sai kuka, ga bala'in Abby daya sakoni gaba wai ko mutuwa zan bazai fasa aurar dani ba, tunda na nuna auren nakeso gara yayi mani ya zauna lafiya, da inje na dauko masa magana kamar yadda yaya yusra tayi gata nan auren baije ko ina ba ya sakota da ciki, saboda ta riga ta watsar da kimarta tun a titi.
Mama haby ke k'ara masa k'aimin fad'an nashi tana zuga shi shikuma yana sake hawa, gaba d'aya gidan babu kwanciyar hankali safe rana dare duk abu guda ake, wannan fitinar tajawo ma yaya yusra miscarriage cikinta ya zube likita yace jininta ne kullin yake sama, ga damuwa data d'ora ma kanta dole zai jawo mata wanan abun.
Ban tab'a gani kukan Ammi ba sai wannan rana, saboda irin ganin wuyar da yaya tasha kamar matatta haka ta koma, tasha wahala ba kad'an ba saida aka mata wankin ciki sannan aka fiddota dakin hutu, munsha kukan mu mungode Allah lokacin.
Kwanan mu hud'u aka sallamo mu daga asibitin, sau d'aya Abby yaje abun har yasoma bamu tsoro don yadda yake yi kamar wasu makiyansa haka ya maidamu, ko su yaya yusuf badai su rab'esa ba zaihau bala'i da zage zage, dole suka daina shiga sabgar sa itama Ammi ta tattarasa ta watsar gefe ko aiki bata fita, tana nan tare damu tana janmu ajiki tare da kwantar mana da hankali nida yaya.
Kwatsam yau da daddare ya aiko mama haby kiranmu mu duka, bamu yi jinkiri ba muka tafi falon nashi fuskar nan murtik babu rahma, ga wani gefe zaune kamar almajiri mamaki duk ya kamamu yau Abby tare da irin wadannan mutanen daya tsana sama da mutuwarsa, zama duk mukai shi kuma mutumin yahau gaida Ammi da yaya yusra.
Abbyn ya tashi daga jinginar dayayi cikin kujera sannan yace, "ba wani abun yasa nace kuzo ba sai don na sanar daku cewar jibi juma'a zan *DAURA MA NAJA'ATU AURE DA WANNAN BAWAN ALLAHN DA KUKE GANI*..............wata zabura nayi gaba d'ayan idanuna waje sukayo na firgice na kalli Abbyn na kalli wanda yake cewa zai aura mun d'in, na fashe da wani matsanacin kuka nace cikin d'aga murya "wallahi tallahi bazan tab'a auren sa ba, da dai na auri wannan k'azamin garamun mutuwa ta..............ban aune ba naji an dauke ni da wani gigitaccen mari daya saka hancina ya fara fitar da jini, idona kamar zai fad'o kasa nake kallon Abbyn yayin da naji na k'ek'ashe bana jin ko d'ar na tsoro araina, bai bani damar magana ba yace cikin masifa............"aiko zaki mutun, domin babu abunda zai hana jibi na daura miki aure, ko gawarki ce sai ankai don haka saiki yanke shawara mutuwarki ko rayuwarki"
Wani k'ara na fasa had'e da kuka na dira k'afa ina cewa, "wallahi tallahi bazan aure sa ba, ni ba wanda xan aure sai *ANNUR* muddin bashi ba wallahi *yawon duniya* zan shiga"
Nai fittt na fice aguje daga falon inajiyo mama haby na cewa, "kagani ko Hussain da baka b'ata su ba duk da ba haka, da zaka bata umurni ta take ga kuma uwarta mai d'aure mata gindi"
Ban tsaya jin me zasu sake cewa ba na dakina na fad'a kan gado ina gurzar kuka kamar Raina zai fita, ji nake kamar na kashe kaina amman bazan iya ba don bansan da wane yare zan ma Allah jawabin abunda yasa na kashe kaina ba, amman tabbas inaji kamar zan aman zuciyata, ni kad'ai nasan ciwo da rad'ad'in da nakeji na bakin ciki da k'unci, ina cikin haka sham ta shigo d'akin ta saman ina kukan.
Zaman lallashina ta fara tana cewa, "Haba noor meyasa kike son da Allah? Shin kinsan yana sane da halin da kike ciki meyasa ba zaki fawwala masa ba, ke musulmace ki yarda da k'addara aduk halin da tazo maki, Allah zai duba zuciyarki"
YOU ARE READING
FRIENDSHIP (A BOTA)
Fanfictiontak'aitaccen labari ne akan abotar mace da namiji ga y'an jami'a, da matan aure shin ya ya kamata ki mu'amalanci namiji matsayinki na mace, ku shigo cikin kabarin domin jin yadda zata kasance.