part 15

33 7 3
                                    

*FRIENDSHIP*
            *(ABOTA)*

*_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_

*E.W.F*

By
Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461.

       Page......15

A wannan ranar Abby da Abba basu zauna ba katsina suka nufa saida suka nemo wannan mutumin nan da ya d'aura Auren mama da Abban Annur, saidai ya tsufa sosai anyi sa'a kuma har certificate d'in auren saida ya fiddo suka gano wanda yake dauke da sunayen su, hankalin su ya kwanta aka sanar da hajiya tabbacin komi dai-dai, a wannan ranan bazan iya misalta yana yin da nake ciki ba, Annur bamu samu damar yin sallama ba ya tafi don kwata kwata baya cikin natsuwa da kwanciyar hankali, nima ban kirasa ba don bansan me zance masa ba konice basan ya zanyi da wannan damuwar ba.

Ammi da su baba Azumi da maman Annur sai washe gari suka wuce maiduguri, ni kuma nace zan cigaba da zama wajen hajiya ba yadda Abby bai yi akan na biyo su Ammi ba aman na k'iya hajiyar  tace mashi ya barni na k'ara natsuwa tukun, komi kenan saina dawo.

Saida nayi sati biyu gidan hajiya kafin na fara shirin komawa gida, tun bayan faruwar wannan abun bamu sake waya da Annur ba, ban san dalili ba amman injin raina yana b'aci akan rashin nema na da yayi, nima ban kira sa ba ko sau d'aya.

A ranar da zan tafin naji Hajiya na waya da Ammi kan cewar wai har sun tsayar da ranar bikina da Annur d'in karshen wata, duk sai naji na duburce abun yazo mani a bazata jikina yai sanyi sosai, saboda ban san me shirun Annur take nufi ba da yake sai da rana zan tafi idan driver ya iso, sai na tsaya na shirya a tsanake hajiya sai tsokana ta take.

"Amaryar Aliyu duk wannan kunufurcin na menene? Ko bikin yayi maki nesa a sauko dashi"

Kamar zan kuka nace, "don Allah hajiya bana so, ki kyaleni da abunda ya isan ni da za'a fasa ma da yafi"

Dariya tayi tace, "naki wasa ne yarinya, wa zaki maida sakarai ki gudu daga gidanku saboda shi sannan yanzu an daidai ta kice a fasa ai kema kin san karyar ki tasha karya"

Sai kawai na kama kuka bansan kona miye ba, kawai dai inajin zuciyata babu d'adi, kewar sa nake k'age nake naji muryar sa, k'amshin sa, murmushin sa amman duk ya tattare komi ya watsar dani.

Lallashina ta shigayi jin da gaske kukan nake, take cewa "inban da abunki Noor miye na kuka kuma daga jin ansaka bikin ki, ai duk wata mace daman dole zataji wannan yana yin, kiyi hkr nasan insha Allah Aliyu zai kula dake"

Da lallami da kalamai masu dad'i ta shawo kaina na daina kukan karshe bacci ya sace ni, ban farka ba sai wurin sha biyu wanda yayi dai-dai da shigowar Hajiya dakin tace, "to gara da kika tashin don da zuwan da nai intada ki ga mijinki can yazo tafiya dake"

Saurin wartsakewa nayi jin abunda tace, ina zaro ido nace "hajiya waye mijina yazo? Wai Annur kike nufi? Shi zai kaini gidan?"

Dafe kai tayi tace, "karki kasheni da tambaya gashi can yana cin abinci ki hanzar ta ki fito saiki tambayeshi, ni kam bazan iya cewa komi ba"

Tafice ta barni nan da mamaki, na dade kafin na shiga wanka ina shirya wa ina tunanin irin yadda zan anshe shi, horanin da yayi na kwana  da kwanaki saina rama, Allah yasa zan iya nasan danayi ido biyu dashi zuciyata zata canza daga abunda tayi niyya, riga da siket ne sun fidda mun shap d'ina, karma ace Boob's d'ina don inadasu masha Allah kamar su kadai nake ba abinci, haka zalika inada hips daidai misali amman nasan Boob's dina sunfi fitowa kanshi.

D'an gyale na sanya yau don inason nayi tsokana, na saka janbaki red yai mun kyau nai daurin kallabi shima mai kyau sannan na feshe jikina da turare dai dai shigowar hajiyar, cikin fad'a tace "kiji tsoron Allah Noor, kina son daukar alhakin yaron nan kenan wannan uban k'amshi da kike bulbulawa, ga kwalliya kinsha irin wannan ai sai anyi aure akeyi yadda koma ya shanye bakomi"

FRIENDSHIP (A BOTA)Where stories live. Discover now