part 13

35 4 1
                                    

*FRIENDSHIP*
            *(ABOTA)*

*_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_

*E.W.F*

By
Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461.

       Page.....13

"Ya isa haka Noor kibar kukan kar ki jawo ma kanki ciwon kai, duk da laifin mahaifinki kema kin tafka naki laifin na baro gida da kikai ba wanda ya sani, kin kama layi kanki kin karya kin zubar don kar anemi idan shi Abbyn naki yayi abunda yasa kika gudu ita mahaifiyarki laifin me tayi? Kin san halin da kika barota aciki kuwa? Banda bala'in mahaifin ki da zata sha ya sake sata cikin tashin hankali, baki kyauta ba Noor da ace kinyi hakuri kin zauna ko waya ki kai mani zanzo har gidan naku Hussain baxai maki auren dole ba muddin ina raye, domin shima ba dolen akai masa ba don haka zan maidaki da kaina"

Wani kukan na sake sanya wa ina kama k'afafunta numfashina kamar zai fita nace, "Hajiya in ba sokike ki rasa ni ba karki maidani wannan gidan, wallahi Abby yanzu baya sona kuma kina maidani zai aurar dani ga wannan kazamin mutumin, hajiya ni idan ba zab'ina ba bazan tab'ayin aure ba ki taimakeni hajiya karki ce dasu ina nan, rayuwata xata shiga wani hali"

Na karashe ina gurzar kuka kamar nimfashi na zai k'are, dagoni tayi jikinta na kwanta na cigaba da kukan tana shafa kaina tace, "shikenan kibar kukan haka nan, zan san abunyi amman kafin nan shi wanda kike son yana sonki? Kuma ashirye yake ya aure ki? Sannan sana'ar me yake yana aiki? Kuma waye baban shi yana da cikekken asali?"

Gabana yai muguwar fad'uwa na fara in ina ina cewa, "Hajiya cikin satin nan yake gama digree d'insa akan mass com., yana da zuciyar neman na kanshi amman babu halin, kuma asanina shidin yana da cikekken asali"

Jinjina kai hajiyar tayi tace, "in dan aikin yi ne bazai hana auren ku ba, saidai wani abun daban zan saka ayi bincike kanshi ki yi waya dashi yazo mu gaisa"

Tunda mukai maganar nan da hajiya hankalina ya kasa kwanciya basan dalilin hakan ba, text nayi masa da sabon layin dana siya tun barowata adamawa.

_Besty fatan ka tashi lafiya, ya exams d'in fatan Allah ya baku sa'a ina kano nazo wajen hajiyar mu idan kana da lokaci ko gobe ko jibi hajiya na son ganinka._

Na tura masa na silale kasan tayil na kwanta saboda sanyin ya ratsa mun zuwa zuciyata, zuwa can saiga kiran sa ya shigo nai firgigi na tashi na wuce dakin da aka kaimun kayana saida na xauna bakin gado na dauka.

"Besty naga sak'onki yanzu, Amman jiya bakice mun zakiyi tafiya ba kuma tun biyar na asuba nake kiranki ban samu ba wai a akashe, Besty meke faruwa inaji ajikina kamar akwai matsala"

Hawaye suka silalo mun cikin raunin murya nace, "Besty Abby ne zai mun aure gobe, tun ajiyan ya sanar dani nadai b'oye maka ne kawai, shine naga bazan iya zama na auri wanda bana so ba sai kawai na gudo wajen hajiya.............na saki kuka ahankali rikicewa yayi sosai yace "innalillahi wa'inna ilahir raju'un Besty Aure gobe? Waye zai aura makin? Don Allah karki amunce wallahi bazan iya jure rasa ki ba, *BESTY INA SONKI* don Allah karki bari arabani dake"

Ina kukan kasa kasa nace, "to ni ya zanyi? Na rasa abunyi shiyasa na gudo wajen hajiya"

Duk a rud'e yake yace, "guduwarki ba maslaha bace Besty, zaki jefa Ammi a cikin damuwa matsananciya na rasa sanin inda kike, amman da sauki tunda zuciyarki bata gaya maki kije wani wajen ba sai wurin hajiya, komi kenan insha Allah gobe zan iso da safe jibi muke gama exams"

Cikin shashsheka nace, "Aa Besty ka bari ka gama gaba d'aya"

"Bazan iya ba, banda natsuwar dazan iya tsayawa har sai nagama exam, zanzo goben komin dare kuma zan dawo insha Allah"

FRIENDSHIP (A BOTA)Where stories live. Discover now