page 1

18 2 0
                                    

**
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_
MUGUN NUFI
_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

FREE PAGE

🅿️:1️⃣

Yanayin fuskokin mutanen da ke cikin falon kawai za ka kalla ka tabbatar da zaman da su ke yi ba na daɗi bane, a hankali shassheƙar kukan matashiyar budurwar da ta kasance ita kaɗai ce mace a cikin su ke tashi, kaf ilahirin jikinta rawa ya ke, kamar me jin tsoron wani abu kar ya kamata haka ta ƙanƙame kujerar da ke kusa da ita.

Cikin fusata ɗaya daga cikinsu me suna Baba Musa ya ce, "Ke ki buɗe baki ki yi mana magana mun gaji da salon munafurcin da ki ke yi,  a komai sai kin nuna cewar kin sha baƙin nono, wannan shine karo na farko da za ki maishemu ƙananan mutane, tunda har waje ta ƙi ki ai dole ne gida ya karɓe ki, hakanan za mu haɗaki da ɗan uwanki shi sai ya rufa mi ki asiri."
Ya ƙarasa maganar yana huci.

Ɗaya bayan ɗaya na sake kallon fuskokin mutanen da ke wurin, maza ne guda biyar uku daga cikin su magidanta ne, se biyu su ne basu wani zama magidanta ba.

Baba Musa yana gama magana, ƙaninsa ya ɗauka wato Baba Isah, cikin izgili ya ce, "Kana ta maganar gida gida to wa ka ke tunanin ze amsheta ni dai gaskiya ba zan iya aurawa ɗana ba,  yana da wacce ya ke so ta ke sonsa."

Murmushin jin daɗi Baba Musa yayi tare da faɗin, "A'a Isah ai hannu baya rubewa a  yanke a yar, haka dai ni zan yi wannan sadaukarwar na aurawa Bashir ita."

Cike da jin haushi karamin cikin su ya ce, "Wai me ku ke yi haka saboda Allah Yaya, Meemerh fa ƴarmu ce, ƴar ɗan uwanmu ce, ko da ace duniya kowa zai ƙita ya aibata ta mu ba za mu yi haka ba, kowa ya shaida ya kuma tabbatar ita ɗin jinin DURUMBU ce, kuma babu wanda ya isa ya musa haka. Shin dama auren bare yana zama illah ne, menene laifinta a gare ku? ku sani aure lokaci ne, kuma insha Allah za ku yi mamakin Mijin Meemerh, sai kun yi mamaki."

Tsit ka ke ji babu wanda ya sake magana da alama sun ji nauyin maganar kanin nasu garesu, ganin haka ya saka shi kallon inda Meemerh take ya ce, "Kinga Mamana tashi ki tafi, ki kwantar da hankalinki, za mu san abun yi kin ji."

Sai yanzu ne ta samu ƙarfin gwaiwar kallon inda mahaifinta ya ke, dan ta tabbatar cewa zai fita shiga cikin damuwa, ilae kuwa dan tana kallonshi ta ga idon nan nashi ya kaɗa ya yi ja tsabar ɓacin ran abinda ƴan'uwansa su ke yiwa gudan jininsa  kuma a gaban idon sa, suna haɗa ido wani kukan ya sake kubce mata da ƙarfi, tashi ta yi da gudu ta fita daga falon.

Kai tsaye ɗakinta ta shige ta faɗa kan gado ta sake fashewa da wani kukan me cin rai, bata san tsawon lokacin da ta shafe tana wannan kukan ba, sai da ta ji an fara shafa bayanta alamar rarrashi, hakan ne ya bata tabbacin cewar lallai ɗaya daga cikin mutanen da su ke jiɓantan lamarinta ne wani ya zo, wato Babanta ko kuma Aminiyarta Suhaima, duk da zuciyarta na faɗa mata cewar Suhaima ce, dan ta san shi kansa Baban na ta yana can cikin damuwa.

Fara sassauta kukanta ta yi sai ajiyar zuciya ta ke saukewa, tayar da ita Suhaima ta yi ta zaunar ba tare da ta ce mata komai ba ta fita, ita ma bata yi magana ba sai dai binta da ido da ta yi tare da ci gaba da sauke ajiyar zuciya, tana nan zaune sai ga Suhaima ta shigo hannunta riƙe da ruwan gora da kuma cup, buɗe murfin gorar ta yi ta tsiyaya mata ruwan ta miƙa mata, bata Musa ba ta karɓa ta sha, sake zuba mata wasu tayi ta kauda kai alamun sun isheta, marairaice fuska Suhaima ta yi alamar magiya, amsa ta yi ta sha kaɗan ta ajiye kofin tare da jan dogon numfashi, tana hurzar da iska.

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now