*MUGUN NUFI*
_(Baya kashe ɗan_ _barewa)_PAID BOOK
*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* *ASSɷ* 📚✍*
_{Onward Together}__STORY AND WRITTEN_
_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////FREE PAGE
🅿️:8️⃣
*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence via* *my Watsap number*
*08039228702*Ka so 70 na damuwar Abdul-khabeer ta yaye, domin neman ɓacin ransa ya yi ya rasa, se ma murmushi da ya ke saki time to time, a haka har ya koma gida, cire wayar ya yi a silent saboda idan an kira ya ji kara, kwanciya ya yi kan kujera ya na ta tunanin wacece Wannan yarinyar a haka bacci me nauyi ya ɗauke sa.
#Meemerh
Ita sam hankalin ta be je kan waya ba, domin waya ba wai ya dameta bane, wani lokaci ma idan ba kira zatayi ba to bazaka ganta rike da waya ba, hira suke sha sosai ita da Suhaima, duk da ƙasan zuciyar ta ta kasa manta wa da bawan Allahn nan to shi kam miye damuwar sa, ko da yake ko ma menene tana da tabbacin matsalar ta tafi tashi kawai dai raganci ne irin na wasu mutane, idan har ita da take mace me karancin shekaru zata iya danne damuwarta me yasa shi da yake katon namiji ya bari damuwar ta rinjaye shi? Kafaɗar ta da Suhaima ta dafa ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya ta na kallon ta " Ke kam Meemerh tunanin me kikeyi haka, se magana nakeyi amma sam baki ma ji ni ba?"
Tunawa nayi da tsautsayin da ya kusan afka min, ina baki labari, motar wani mafaɗacin mutum na kusa rafka, Allah ne dai ya tsare na san da se ya zabga min mari, Kinga yadda yake jaraba kuwa? Ga babu kowa a hanyar ni har na gama sadaƙarwa ma jibgana xeyi " dariya Suhaima ta yi ta ce, " to ke yanzu idan ma jibgarki xeyi se ki tsaya kina kallon sa? Hmm Suhaima ni ce fa banda gaskiya motar ne ta ƙwacemin" na san dai ba kya tukin ganganci garin ya hakan ya faru? Hmmmm garin tsautsayi, da tunanin rashin mutuncin tsohuwar can mana, wallahi Suhaima yau ba dan ganin idon Abie ba da babu abinda ze hana nayi maganin Dada, abun da takeyi min ya fara isa na, wai me na tsare musu ne a rayuwar nan, kowa burin sa dai ya ga ya tozarta ni, sam zaman gidan ya isheni wallahi, dazu ma na gama da Hajiya Hadiza......" Labarin abunda ya faru ta bata, dariya sosai Suhaima ta yi " kin san Allah Meemerh baki taɓa burgeni irin yau ba, ai haka nake so ki zama jaruma, idan kina yi musu haka wallahi zasu shiga taitayinsu, yanzu ita baki ga ta tsorata ba, kingani ko Dada manta xakiyi cewar ita kakarki ce tunda ita ma ba ta ɗauke ki a jika ba, kina dai gani ko wa'yanda ta ke son ba raga mata sukeyi ba, to bare ke" hmmm ke ni baxan iya yi mata rashin mutunci ba saboda Abie, na barta da halinta ko wa ya yi na gari ai dan kansa, na san dai tukunyar sharri bata isa ta hana tuwon kaddarar alkhairi dahuwa ba, duk abinda xasuyi wlh idan baya cikin ƙaddara ta baze faru ba, ni fa a duniyar nan bayan Abie bana tuna kowa a cikinta, shine komai nawa, dama da na tashi ban san soayyar dangi ba bare abun ya dameni, addu'a ta daya ne Suhaima Ubangiji ya yiwa Abiena tsawon rayuwa, Kinsan matukar ya mutu ya barni to zaman gidan shi baze yiyu a gareni ba, yanzu ma a gaban idon shi menene ba'ayi to idan kuma baya nan fa?"
" Meemerh kenan, ke dai kawai kici gaba da haƙuri, na tabbata Ubangiji yana ta re dake, matslaar ki ɗaya shine kiyayyar da kikeyiwa mahaifiyarki, kina ganin ko alhakin ta baze sa waƴannan jarabawar su rika bibiyarki ba, duk duniya babu kamar uwa Meemerh, sau uku Annabinmu ya fadi abita, ka fin yace abi uba sau ɗaya, Meemerh kina tunanin duk abinda ze sa mahaifiyar ki ta yanke soyayyar da aka sani tsakanin uwa da ƴarta abu karami ne, shin su Baba Musa da Dada basu isa su zama fitilar dubanki akan dalilin rabaki da ita ba? Tabbas zuciyata ta na bani ba barinki tayi ba, anyi mata fin ƙarfi ne, Meemerh lokacin da ɗan Adam ya rasu abubuwa uku ne suka rage masa, sadakatul jariya, ko kuma ilimin da ya amfanar, ko idan ya bar ɗa na gari wanda yake yi masa addu'a, shin kin taɓa zama kin yi mata addu'a? Kina da tabbacin tana raye ko kuwa ta mutu? Memerh ko da iya wahalar daukar ciki da nakuda tayi miki ya ci ki girmamata, wannan abun shine matsalar ki a rayuwa, kiyi yaki da sheɗan domin ki samu yardar Allah, kin sani ba se na sanar da ke ba, yardar Allah tana tare ne da yardar iyaye, kuma Kinji masu iya magana suka ce, uwa mafi uba, ko da kuwa uban mutum sarki ne, amma ke gani kikeyi Abie ya isheki ko? Ta kara sa faɗa tana tsareta da ido
Fashewa Meemerh ta yi da kuka, tabbas ta san gaskiya Suhaima ke gaya mata, sedai ta ya zuciyarta zata amshi matar da ta wofantar da ita a matsayin uwa? Idan har da gaske ne akwai soyayya me ƙarfi da Allah ke sakawa tsakanin uwa da ƴarta, to ita me yasa ta wofantar da soyayyar, komai girman abinda su Baba Musa sukayi mata be ci ace ya shafe ta ba, tunda dai ita ce ta haifeta, kuma meyasa ba tayi tunanin halin da zata shiga a gidan ba ta iya tafiya ta barta, kai bata tunanin zata iya kaunar matar nan ko kaɗan, sedai tabbas yaune rana ta farko da take jin son sanin labarin mahaifiyar ta, da dalilin barin ta gidan Abie duk da ta fahimci cewar har yanzu yana son matar sa to meyasa shima be je ya dawo da ita ba? Lallai ya kamata ta san abubuwan da su ka faru a lokacin.
#Abdul-khabeer
Kiraye-kirayen sallah ne ta tayar da shi daga nannauyan baccin da ya ɗauke shi, wanda rabinsa duk mafalkai ne akan yarinyar da ko sunan ta ma be sani ba. Da sauri ya duba wayar ko an kira se dai a mamakin sa babu wanda ya kira wayar, kurawa hoton da ke yawo kan screen din wayar ido ya yi, tabbas ko ba'a faɗa ba ya san hoton mahaifinta ne domin akwai kammani a tsakanin su, sosai ya kurawa hoton ido kamar ya so ya san mutumin se dai a ina? Shi ba wani yawo ya keyi a KD ba idan baya asibiti to zaka sameshi a gida, ajiye wayar yayi ya mike don jin har an kabbarta sallah, da sauri ya shiga ciki alwala ya yi, ya fito zuwa Masallaci, bayan an idar da sallah ya dawo gida, Still sake duba wayar yayi ba'a kira ba, mamaki ne ya kamashi ya san ƴan matan yanzu babu abinda suke bawa muhimmanci kamar wayar su, amma ita ace ka jefar da waya ba ka nema ba ai ko dan layinta ma ya kamata ta damu.
Ta shi yayi ya watsa ruwa don zuwa dauko su Aunty, tunda yamma yayi, sautin muryarsa wacce babu alamun damuwa ne ya shiga kunnen Auntyn sa, yayi dan yake furta, "Assalamu alaikum" da sauri ta daga kai ta kalleshi, murmushi ya sake mata ta re da kara so wa inda take, "Sannu da gida Aunty, ke kaɗai ce duk ina sauran banga twins ba" ya faɗa yana zama kan hannun kujerar da take zaune, tabbas batayi tunanin ganin sa haka ba a yanayin da ya fita tun ɗazu kawaici kawai takeyi amma hankalin ta na kan shi, dan ta san be iya shiga damuwa ba. Ajiyar zuciya ta dauke tare da sake masa murmushi ita ma " naji daɗin ganin ka Abdul-khabeer, tun dazu nake son kiranka don in rarrashe ka to ina tare da Hajiya ne, ka san halinta ai dama suna fadar ni ce ke daure ma, shiyasa na daure ban kiraba, se gashi Alhamdulillah ma na ganka cikin farinciki da ban taɓa ganin ka ba, anya gist me, i knew there's something behind this smile, miye sirrin?"
Shafa kan sa yayi tare da fadin, " yau dai na samu wacce raina ke so Aunty, ba dai saboda haka ne ake shirin haɗani da wata can ba, to na hutar da shi nima na samu wacce na ke so" fadada fari'arta tayi, " to Alhamdulillah, tun tuni da kayi hakan ai da ba'a zo wannan matakin ba, duk da ka san abu ne ne wahala ya janye maganar hadin nan amma at least yanzu mun samu kwarin gwiwar nuna masa baka son zabinsa, amma wacece wannan me sa'ar, domin duk wacce ta samu soyayyar ka tabbas ba karamin Sa'a ne da ita ba, dan ɗana me tsada ne" kai Aunty addu'a ya kamata kiyi Allah ya sa ta karbi soyayyata, dan da gani se nayi fama kafin na rabata da samari dan mace kamarta dai na san akwai tarin masoya kam, ga ɗan na ki akwai kishi" dukan wasa tayi masa ya tashi yana daria..........
Saura mana page ɗaya mu gana free pages, ku hanzarta biyan kuɗin ku, domin yanzu ne labarin ze soma bakuji komai ba ba kuma ku ga komai ba,
₦300only
VIP wanda baku son zama cikin group kina zaune abinki zan rika turo mk PC zaku biya ₦500onlyComments and share pls
#Real@Bazamfaria💋ention a user
YOU ARE READING
MUGUN NUFI
Mystery / ThrillerSoyayyar uwa soyayya ce da ake haifar ƴaƴa da ita, musamman ma ƴaƴa mata, sedai wannan ya sha banban da rayuwar Meemerh, a duniya babu wacce ta tsana kamar mahaifiyarta, bata tashi tare da ita ba amma ko yaushe addu'ar ta da fatan ta ko a mafalki ka...